Peru: An Yanke wa Tsohon Shugaban Kasa da Matarsa Hukuncin Ɗaurin Shekaru 15

Peru: An Yanke wa Tsohon Shugaban Kasa da Matarsa Hukuncin Ɗaurin Shekaru 15

  • Kotu a Peru ta yanke wa tsohon shugaban kasa, Ollanta Humala, hukuncin daurin shekaru 15 bisa laifin karɓar rashawa daga Odebrecht
  • Matarsa, Nadine Heredia, ta samu irin wannan hukunci, sai dai ta nemi mafakar siyasa a ofishin jakadancin Brazil da ke birnin Lima
  • Wasu 'yan Najeriya da suka zanta da Legit Hausa, sun nuna cewa akwai bukatar fannin shari'ar Najeriya ya ci gashin kansa don yanke irin wannan hukunci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Peruvian - Kotu ta yanke wa tsohon shugaban kasar Peru, Ollanta Humala, hukuncin zaman gidan yari na shekaru 15 bisa laifin halatta kudaden haram.

Matarsa, Nadine Heredia, ta samu makamancin wannan hukunci, amma ta samu mafakar siyasa bayan da ta shiga ofishin jakadancin Brazil da ke Lima.

Kotu ta yanke wa tsohon shugaban Peru, Ollanta Humala da matarsa Heredia hukuncin daurin shekaru 15
Tsohon shugaban ƙasar Peru (2011-2016), Ollanta Humala, na magana a waya yayin da yake barin harabar kotu a ranar 15 ga Afrilu, 2025. Hoto: CONNIE FRANCE/AFP
Asali: Getty Images

Kotu ta daure tsohon shugaban kasar Peru

Kotun ta same su da laifin karɓar dala miliyan uku daga kamfanin gine-ginen Brazil mai suna Odebrecht, wanda aka gano na haram ne, inji rahoton The New York Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce an yi amfani da wadannan kudi wajen tallafa wa yakin neman zaben Humala a shekarar 2006 da 2011, amma lauyansa ya ce hukuncin ya yi tsauri da yawa.

Odebrecht dai ya amsa cewa ya ba da rashawa a kasashen Latin Amurka da dama don fadada harkokinsa, kuma yanzu haka kamfanin na fuskantar durkushewar tattalin arziki.

An tasa Humala, mai shekaru 62 da ya yi ritaya daga aikin soja, zuwa gidan yari, yayin da zai zauna a kurkuku har zuwa shekarar 2039 bayan hukuncin babban kotun kasar.

Shugabannin Peru da aka daure kan rashawa

Rahoto ya nuna cewa Humala ne shugaban kasar Peru na uku da aka daure kan laifin cin hanci da rashawa a cikin shekara 20 da suka wuce.

An ce tsohon shugaban kasa, Alejandro Toledo ya samu hukuncin shekaru 20 a 2024 bayan karɓar dala miliyan 35 a matsayin rashawa domin ba da kwangiloli na ayyukan gwamnati.

Rahoton Sky News ya nuna cewa an gina sansanin 'yan sanda na musamman domin tsare shugabannin PEru da aka daure, kuma ana sa ran Humala zai yi zaman gidan yari a nan tare da Toledo.

Lauyoyinsa dai sun ce za su daukaka kara da zarar hukuncin karshe ya fito, suna masu cewa masu gabatar da karar sun kasa tabbatar da cewa Humala ya samu kudin daga hanyar haram.

Mazauna Peru sun fusata da tsofaffin shugabanninsu

An tura tsohon shugaban Peru gidan yari yayin da matarsa ta samu mafakar siyasa a ofishin Brazil.
Tsohon shugaban Peru (2011-2016), Ollanta Humala, yana magana kusa da matarsa Nadine Heredia a 2018. Hoto: LUKA GONZALES / Contributor
Asali: Getty Images

A 2019, tsohon shugaban kasa Alan Garcia ya harbe kansa lokacin da 'yan sanda suka je gidansa domin kama shi bisa zargin karbar cin hanci daga kamfanin Odebrecht.

Tsoffin jami’an kamfanin sun bayyana cewa kamfanin ya dauki nauyin kusan dukkanin masu neman shugabancin kasar Peru cikin shekaru 30 da suka gabata.

Wani mazaunin Lima, Fernando Quintalla, ya ce ya fusata sosai da yadda aka bai wa matar Humala mafaka.

"Gaskiya al'ummar kasar Peru sun fusata sosai, ace kusan dukkanin shugaban kasar da muka yi tun daga 2000 zuwa yau, ana samunsu da cin hanci da rashawa.
"Ba a taba samun makamancin wannan ba a tarihin kasar nan, duk sun bi sun mayar da kasarmu ta zamo ta masu cin hanci da rashawa."

- A cewar Fernando.

An nemi fannin shari'ar Najeriya su tashi tsaye

A zantawar Legit Hausa da Nura Haruna Maikarfe, ya nuna cewa akwai bukatar a sakarwa fannin shari'ar Najeriya mara domin yanke hukunce-hukunce irin wadannan.

Ya ce:

"Akwai tsofaffin gwamnoni, sanatoci, 'yan majalisu, jami'an gwamnati da dama da ake zargi da rashawa, amma abin mamaki, ko an je kotu, haka za a shahantar da maganar.
"Duk yadda aka so ga hukunta wadanda suka rike madafun iko, to sai ka ga an samu tangarda, ta yadda hakan ke kara sanya wasu masu mulki satar dukiyar jama'a."

Nura Haruna ya ce akwai bukatar a fara yanke wa tsofaffin shugabanni da ma'aikatan gwamnati hukuncin zaman gidan kaso, kuma a tabbatar da shi, don zama izina ga na baya.

Muhammad Kabir daga jihar Kaduna, shi ma ya tafi da wannan ra'ayin na cewa cin hanci da rashawa ya jawo fannin shari'a ya gagara aiwatar da ayyukansa yadda ya kamata.

Ya ba da misalai da yadda ake samun wasu alkalai da karbar rashawa, ko kuma amfani da shari'ar ba ta hanyar da ta dace ba, wanda ya ce hakan ba dai dai ba ne.

"Idan ya zamana alkalai ba sa karbar umarnin kowa, to ba shakka masu cin hanci da satar dukiyar jama'a za su shiga taitayinsu, don sun san za su sha dauri idan aka kama su da laifi."

- Muhammad Kabir.

Kotun Fakistan ta daure tsohon shugaban kasa

A wani labarin, mun rahoto cewa, an yanke wa tsohon shugaban Pakistan, Imran Khan, hukuncin daurin shekaru 14 kan zargin rashawa da wasu laifuffuka.

Imran Khan ya sha musanta sama da tuhuma 100 da ake yi masa, yana mai cewa duka suna da nasaba da wata manufa ta siyasa da ake ƙulla masa.

Magoya bayansa sun fito zanga-zanga a wasu sassan ƙasar, amma an rahoto cewa jami’an tsaro sun dakile gangamin da karfi da yaji.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.