A Karon Farko, Malamin Makaranta Ya Zama Shugaban Ƙasa a Peru

A Karon Farko, Malamin Makaranta Ya Zama Shugaban Ƙasa a Peru

  • Pedro Castillo, malamin makaranta ya zama sabon shugaban kasar Peru
  • Castillo ya yi nasarar ne bayan cin galaba kan tsohuwar shugaba Keiko Fujimori
  • Mr Castillo, mai shekaru 51 ne talaka na farko da ya fara lashe zabe a kasar ta Peru

Malamin makaranta, Pedro Castillo ya zama zabeben shugaban kasar Peru, kamar yadda aka sanar bayan makonni shida da kammala zaben saboda zargin magudi da abokin hammayarsa Keiko Fujimori ta yi.

Jorge Luis Salas, shugaban kotun sauraran karar zabe JNE, ne ya sanar da nasarar ta Castillo ta hanyar bidiyo a daren ranar Litinin 19 ga watan Yuli, CBS News ta ruwaito.

Pedro Castillo: Malamin Makaranta Ya Zama Shugaban Kasa a Peru
Pedro Castillo, Malamin Makaranta Ya Zama Shugaban Kasar Peru. Hoto: Top Naija
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Sunday Igboho Ya Sharɓi Kuka Kamar Ƙaramin Yaro Da Muka Yi Magana a Waya, Lauyansa

NBS News ta ruwaito cewa Castillo, mai shekaru 51 shine shugaban kungiyar malaman makaranta na kasar. Shine talaka na farko da ya taba zama shugaban kasa a Peru.

Kara karanta wannan

Tsamo Ƴan Nigeria Miliyan 100 Daga Ƙangin Talauci: Har Yanzu Bamu Makara Ba – Buhari

Akwai yiwuwar abokin hammayarsa, Fujimori, zai fuskanci zargin rashawa bayan Casttillo ya hau mulki.

"A madadin iyali na da ni kaina, ina son jinjinawa hukumomin zabe ... da kuma jam'iyyun siyasan bisa rawar da suka taka a wannan bikin na demokradiyya," Castillo ya fadawa magoya bayansa da suka taru a hedkwatar jam'iyyarsa ta Peru Libre a Lima.
"Ya ku yan kasa, na zo muku ne da budadden zuciya," a cewarsa.

KU KARANTA: Eid-el-Kabir: Gwamna Ya Biya Wa Matafiya 6,000 Kuɗin Jirgin Ƙasa Zuwa Gida Sallah

A wani matakin dattaku ga Fujimori, mai shekaru 46, zababbe shugaban kasar ya bukaci ta taimaka 'don ciyyar da kasar gaba' ya kuma ce 'baya gaba da ita' duk da hare-haren da aka kai masa a makonnin da suka shude.

Da farko Fujimori ta yi ikirarin cewa an tafka magudin zabe duk da cewa masu sanya ido daga Amurka da kasashen Turai sun ce anyi adalci a zaben.

Kara karanta wannan

Ndume na rokon kotu da ta tsame shi daga shari'ar Maina, ta bashi kadarorinsa

Ofishin jakadancin Amurka da ke Lima ya taya yan kasar Peru murnar kammala zaben cikin nasara.

Farfesa Wushishi: Abu 6 da ya kamata ku sani kan sabon shugaban NECO Da Buhari ya naɗa

A wani labarin daban, kun ji Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Farfesa Ibrahim Dantani Wushishi a matsayin sabon shugaban hukumar shirya jarrabawar kasa ta NECO, Daily Trust ta ruwaito.

Mukadashin shugaba ne ya ke rike da hukumar tun bayan rasuwar tsohon shugabanta Farfesa Godswill Okeke.

Wata wasika mai kwana wata 16 ga wata Yulin 2021 dauke da lamba FME/PSE/NECO/1078/C.1/36 da sanya hannun ministan Ilimi, Adamu Adamu, ta ce an nada shi ne karo na farko na shekaru biyar daga ranar 12 ga watan Yulin 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel