Gudun abin kunya: Tsohon shugaban kasar Peru ya harbe kan sa
Tsohon shugaban kasar Peru, Alan Garcia, ya mutu sakamakon harbe kan sa da ya yi, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar ya fada a ranar Laraba.
Tsohon shugaban kasa Garcia, wanda ke fuskantar tuhumar cin hanci, ya harbe kan sa ne da safiyar ranar Laraba bayan jami'an 'yan sanda sun isa gidansa, kamar yadda kafafen yada labarai a kasar Peru suka sanar.
Shugaban kasar Peru, Martin Vizcarra, wanda labarin mutuwar ya matukar girgiza shi, ya rubuta a shafinsa na dandalin sada zumunta (Tuwita) cewar; "ina mika sakon ta'aziyya ta ga iyali da masoyan sa."
An garzaya da Garcia zuwa asibitin Casimiro Ullola domin ceto rayuwar sa, kamar yadda ministan lafiyaa kasar, Zulema Tomas, ya fada wa manema labarai. Ya ce an kai tsohon shugaban kasar asibiti cikin mawuyacin hali.
Tomas ya ce an kai Garcia asibitin da misalin karfe 6:45 na safe, sannan an shiga da shi dakin tiyata bayan mintuna 15 da kai shi. Ministan ya ce sau uku tsohon shugaban kasar na samun bugun zuciya a lokacin da ake yi masa tiyata.
DUBA WANNAN: Kotu ta bawa EFCC damar kama wasu manyan ministoci biyu a gwamnatin PDP
Garcia, mai shekaru 69, ya kasance shugaban kasa a kasar Peru har sau biyu; daga sheakarar 1985 zuwa 1990 a karo na farko da kuma daga shekarar 2006 zuwa 2011 a karo na biyu. Ya kara tsaya wa takara a shekarar 2016, amma ya gaza samun kaso 6% na kuri'un da aka kada.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng