Kotu Ta Daure Tsohon Shugaban Kasa Shekaru 14 a Gidan Yari kan Cin Hanci da Rashawa
- An yankewa tsohon Firaministan Pakistan, Imran Khan, daurin shekara 14 a gidan yari kan batun rashawa da sauran laifuffuka
- Imran Khan dai ya fuskanci tuhume-tuhume sama da 100, wadanda duka ya musanta tare da ikirarin cewa suna da alaka da siyasa
- Mabiya tsohon shugaban kasar sun gudanar da zanga-zanga, wanda hukumomi suka yi amfani da ƙarfi wajen dakatar da su
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Pakistan - Kotu ta daure tsohon Firaministan Pakistan, Imran Khan, shekaru 14 a gidan yari kan zargin rashawa da manyan laifuffuka.
Wannan hukunci shi ne mafi tsawo da aka taba yankewa Imran Khan, wanda aka tsare tun watan Agustar shekarar 2023.

Asali: Getty Images
Kotu ta daure tsohon shugaban Pakistan
Rahoton BBC ya nuna cewa Amir Khan ya fuskanci sama da tuhume-tuhume 100, ciki har da zarginsa da satar sirrin kasa da kuma sayar da kayan gwamnati.

Kara karanta wannan
Karfin hali: Dan ta'adda ya kai ziyarar jaje gidan mutanen da ya yi garkuwa da su
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukuncin na ƙarshe yana da girma sosai a kasar Pakistan, duk da cewa akwai manyan cin hanci a tarihin kasar da suka shafi shugabannin baya.
An zargi Imran Khan da karɓar wani fili daga wani babban mai harkar gini a matsayin rashawa ta hanyar gidauniyar Al-Qadir Trust da ya kafa lokacin yana mulki.
A cikin wannan yarjejeniyar, hukumar laifuffuka ta Biritaniya ta ce Khan ya yi amfani da fam miliyan 190 ($232m) da aka dawo da su daga Birtaniya don biyan kuɗin tara na mai ginin.
Jam'iyyar PTI ta kare tsohon shugaban kasa
Sai dai jam'iyyar Pakistan Tehreek-e-Insaf (PTI) ta ce an bai wa gidauniyar Trust filin a matsayin kyauta domin gina cibiyar ilimi ta addini, ba don amfanin Khan ba.
A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X, shugaban PTI, Gohar Ali Khan, ya ce Imran Khan bai aikata wani laifi ba kuma wannan shari’ar ba ta dace ba ce.
Ya kara da cewa:
"Amma [Imran Khan] ba zai janye ba, ba zai ƙyale ba kuma ba zai karaya ba."
Hukuncin da aka yanke ranar Juma'a ya kawo karshen jinkirin yanke hukunci da aka samu, yayin da jam’iyyar Khan ke tattaunawa da gwamnati.
Bayan yanke hukuncin, Khan ya shaida wa manema labarai a kotu cewa ba zai yi wata yarjejeniya ko ya nemi sauƙi ba.
Lokuta da dama da aka yankewa Khan hukunci
A cikin shekarar 2023, an yankewa Khan hukuncin shekara 3 a kurkuku kan rashin bayyana kuɗin da ya samu daga sayar da kayan gwamnati da ya karɓa a lokacin yana ofis.
A shekarar da ta gabata, kotu ta daure Kan shekaru 14 kan sayar da kayan gwamnati, da kuma shekaru 10 kan satar sirrin kasa, amma an janye hukuncin duka a cikin watanni.
Duk da kasancewarsa a cikin kurkuku da hana shi rike mukaman siyasa, har yanzu tsohon firaministan yana da tasiri mai ƙarfi a fagen siyasar Pakistan.
Har yanzu Imram Khan na da tasiri a Pakistan
A zaben shekarar da ta gabata, 'yan takarar da Imran Khan ya goyi baya sun lashe mafi yawan kujeru daga dukkanin jam’iyyun siyasar kasar.
Zarge-zargen da ake yi wa Khan sun haifar da tarzoma mai yawa daga mabiya, wanda hukumomi suka yi amfani da karfi wajen danne su.
An ce 'yan sanda sun kama dubban masu zanga-zanga, yayin da dama daga cikin su suka samu raunuka a rikice-rikicen da suka faru da jami'an.
An farmaki tsohon Firamistan Pakistan
A wani labarin, mun ruwaito cewa an kai hari kan tsohon Firaministan Pakistan, Imran Khan, yayin wata zanga-zanga inda aka garzaya da shi asibiti.
Shugaban kasar Pakistan ya yi Allah-wadai da wannan harin na yunkurin kashe Khan, yana mai kiran da a yi bincike domin tabbatar da gaskiya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng