Mace Ta Zama Shugaban Kasar Peru Akaran Farko Bayan Tsige Shugaban Kasar

Mace Ta Zama Shugaban Kasar Peru Akaran Farko Bayan Tsige Shugaban Kasar

  • Dina Boluarte, mai shekaru 60, ita ce mataimakiyar Mista Castillo da aka tsige ranar Laraba bayan sanar da kafa dokar ta baci da kuma rusa majalisar.
  • Sau uku 'yan majalissar kasar sukai yunkurin tsige shugaba Pedro Castillo daga mukaminsa
  • Kasar Peru dai tana yankin kudancin Nahiyar Amurka kuma tana fama da fitutunun siyasa da jagoranci

Peru: Kasar Peru ta rantsar da shugabar kasa mace ta farko kwana guda bayan tsige tsohon shugaban kasar Pedro Castillo. A wani rahotan Jaridar Premium Times

Dina Boluarte, mai shekaru 60, ita ce mataimakiyar Mista Castillo wanda aka tsige a ranar Laraba bayan da aka rusa majalissar kasar da sanya dokar tab'aci.

Bayan tsige Mista Castillo, an yi kira ga Ms Boluarte da ta karbi ragamar jagorancin kasar wadda ta ke a Kudancin Amurka.

Shugabar Peru
Mace Ta Zama Shugaban Kasar Peru Akaran Farko Bayan Tsige Shugaban Kasar Hoto: TSBN
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Zuwa yanzu dai zata shafe shekara hudu akan karagar mulkin da zata bata damar zama har shekarar 2026.

Yadda Aka tsige Tsohon Shugaban kasar Castillo Da Yadda Aka kama Shi

Mista Castillo ya bayar da wata sanarwa a gidan talabijin na kasar, inda yake sanar da kafa dokar ta baci da kuma rushe majalisar kasar.

Ba tare da la’akari da furucin nasa ba, majalisar ta ci gaba da zaman tsige shi, wanda shi ne yunkuri na uku tun bayan hawansa mulki a watan Yulin 2021.

‘Yan majalisa 101 ne suka kada kuri’ar tsige shi, yayin da shida suka ki amincewa, sannan 10 suka zama yan ba ruwanmu.

Gwamnatin Mista Castillo ta fuskanci cece-kuce daban-daban, inda aka nada ministoci da dama, da maye gurbinsu, korarsu ko kuma suka bar mukamansu cikin shekaru kadan.

Mata 21 Ne ke Takarar Mataimakan Gwama A Nigeria A Zaben Shekarar 203

'Yan takarar mataimakan gwamna mata ashirin da daya ne ke neman darewa mukamin mataimakan gwamna a fadin tarayyar Nigeria.

Daga jihohin arewa maso yamma babu 'yar takara ko daya sai a jihar Kaduna inda Hajiya Sabuwa Hadiza Bala take neman matsayin a jam'iyyar APC mai muklin jihar.

Daga jihar Akwa-Ibom kuwa yan takarar har mataimakan gwamnan har guda biyu daga jam'iyyar PDP da kuma jam'iyyar AAC, wato Sanata Caroline Danjumma da Sanata Akon Eyekenyi.

An D'aure Dan Gidan Shugaban Kasa A Mozambique

A Mozambique kuwa dan gidan tsohon shugaban kasar, Armando Gubezua aka daudaure shekara goma sha biyu a gidan maza.

Daurin nasa dai ya biyo zargin da koton kasar tai masa na cin hanci da rashawa, hada baki wajen aikiata laifuka, halasata kudin haram da kuma sabawa kundin tsarin mulkin kasar

Asali: Legit.ng

Online view pixel