An Kama 'Yar Tiktok da Laifin Batanci ga Annabin Allah a Azumin Ramadan
- Kotun Indonesia ta yanke wa Ratu Thalisa hukuncin daurin shekaru 2 da watanni 10 a gidan yari bisa batanci
- Rahotanni sun nuna cewa an tuhume ta ne bayan ta yi hira da hoton annabi Isa a TikTok tana cewa ya aske gashinsa
- Kungiyoyin kare hakkin bil'adama, ciki har da Amnesty International, sun soki hukuncin tare da kira a soke shi
- Wani malamin addinin Musulunci ya bayyanawa Legit cewa hakkin kowane Musulmi ne ya girmama dukkan Annabawa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Indonesia – An yi wa wata 'yar Tiktok a kasar Indonesia mai suna Ratu Thalisa hukuncin daurin shekaru biyu da watanni 10 a gidan yari bayan kotu ta same ta da laifin batanci ga annabi Isa.
Kotun Medan da ke yankin Sumatra ta ce kalaman Thalisa na iya haddasa rashin zaman lafiya da kuma lalata kyakkyawar dangantaka tsakanin addinai a kasar.

Asali: Getty Images
BBC ta rahoto cewa hukuncin ya biyo bayan koke-koken da kungiyoyin Kiristoci da dama suka shigar suna zarginta da batanci ga addini.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda Ratu ta yi batanci ga Annabi Isa
Ratu Thalisa, wacce ke da dubban mabiya a TikTok, tana gudanar da hirar kai tsaye lokacin da wani ya bukaci ta rage gashinta domin ta fi kama da maza.
A martaninta, ta juya wayarta zuwa wani hoto da ake cewa na annabi Isa ne ta na cewa:
"Kai ma kamata ya yi ka aske gashinka."
Wannan magana ta jawo ce-ce-ku-ce, inda wasu Kiristoci suka dauke ta a matsayin batanci, suka kuma garzaya gaban hukuma.
Kotun Medan ta ce wannan furuci na iya haifar da hargitsi a kasar, don haka ta yanke mata hukuncin zaman gidan yari.
Martanin kungiyoyin kare hakkin Bil'adama
Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta soki hukuncin, tana mai cewa hukuma ta tauye ‘yancin fadar albarkacin baki ga Thalisa.

Kara karanta wannan
'Sun koma barayi': Ana zargin jami'an tsaron da gwamna ya kafa suna satar dabbobi
Shugaban Amnesty a Indonesia, Usman Hamid, ya ce:
"Gwamnatin Indonesia ba za ta ci gaba da amfani da dokar hana batanci don tauye ‘yancin fadin albarkacin baki a kafofin sada zumunta ba.
"Hukuncin da aka yanke wa Thalisa ya saba wa ka’idojin dimokuradiyya."
A karkashin haka, Hamid ya bukaci a soke hukuncin tare da yin garambawul ga dokar hana batanci a kasar.
Dokar hana batanci a kasar Indonesia
Dokar hana batanci ta kasar Indonesia wacce aka fara amfani da ita a 2008 kuma aka gyara a 2016 ta dade tana haifar da ce-ce-ku-ce.
Binciken Amnesty International ya nuna cewa mutane 560 ne aka tuhuma da laifukan da suka shafi batanci daga 2019 zuwa 2024, inda 421 daga cikinsu aka yanke wa hukunci.
Yawancin mutanen da aka tuhuma a karkashin dokar ‘yan wasu addinai ne da ake zarginsu da batanci ga Musulunci.
Sai dai a wannan karon, shari’ar Ratu Thalisa ta sha bamban, domin ita Musulma ce da aka tuhume da batanci ga Kiristanci.

Asali: Getty Images
Masu gabatar da kara sun nemi a yanke mata hukuncin da ya wuce shekaru hudu, inda suka daukaka kara bayan yanke hukuncin kotu.
A yanzu haka, Thalisa na da kwanaki bakwai don daukaka kara, yayin da duniya ke ci gaba da bibiyar yadda za a kammala shari’ar.
Legit ta tattauna da malamin addini
Wani Malamin addinin Musulunci, Ustaz Abubakar Yakubu ya bayyanawa Legit cewa abin takaici ne a samu Musulma da rashin girmama Annabi Isa.
"Kowa ne Annabi na da daraja a Musulunci. Duk wanda ya raina wani Annabi kamar ya raina dukkan Annabawa ne.
"Ya kamata kowa ne Musulmi ya san cewa wajibi ne a kansa ya girmama dukkan Annabawa."
- Muhammad Abubakar
An daure 'yan Tiktok a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa wata kotu a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya ta yanke hukuncin zaman gidan yari ga wasu 'yan Tiktok.

Kara karanta wannan
Ajali ya yi kira: Hatsabibin ɗan bindiga, Shekau ya mutu yayin arangama da ƴan ta'adda
Rahotanni sun tabbatar da cewa an yanke musu hukuncin ne bayan an kama su da laifin yada bidiyon batsa da ya saba dokokin Kano.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng