Bayan Murja Kunya, Hisbah Ta Sake Kama Wata ‘Yar TikTok Kan Babban Laifi 1 a Kano

Bayan Murja Kunya, Hisbah Ta Sake Kama Wata ‘Yar TikTok Kan Babban Laifi 1 a Kano

  • Hukumar Hisbah a Kano tana ci gaba da kai samame kan masu yada badala da dabiún rashin tarbiya cikin al'umma a jihar
  • Jami'an hukumar Hisbah sun kama shahararriyar jarumar TikTok, Ramlat Princess kan zargin tallata madugo a cikin al'umma
  • Ramlat ta shiga hannu ne bayan ta saki wani bidiyo a dandalinta inda take cewa duk mijin da za ta aura dole ya barta ta auro tata matar

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kano - Hukumar Hisbah ta jihar Kano, ta kama wata shahararriyar 'yar TikTok, Ramlat Princess, kan zargin wallafa wasu bayanai a shafinta na TikTok da ke tallata madigo.

Hukumar wacce aka kafa domin ta yi yaki da alfasha a Kano, ta tabbatar da kamun ta wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na TikTok.

Kara karanta wannan

Kotu ta tura mutumin da aka kama da Murja magarkama, zai shafe watanni 6

Hisbah ta kama 'yar TikTok
Bayan Murja Kunya, Hisbah Ta Sake Kama Wata ‘Yar TikTok Bisa Zargin Tallata Madugo a Kano Hoto: @MobilePunch,@HonAbdullahiM12
Asali: Twitter

Me yasa aka kama Ramlat?

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa an kama jarumar TikTok din ne a daren ranar Alhamis, 15 ga watan Fabrairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kwanakin baya ne Ramlat Princess, wacce ta shahara wajen wallafa abubuwan da suka saba al'ada da nuna rashin tsoro ta wallafa wani bidiyo da ke tallata madugo.

Bidiyon nata ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya, musamman ma a tsakanin al'ummar jihar Kano.

A cikin bidiyo, ta fito karara ta bayyana cewa dole mijin da za ta aura ya barta ta auro tata matar itama.

Kamun nata na zuwa ne 'yan kwanaki bayan hukumar ta damke fitacciyar jarumar TikTok, Murja Ibrahim Kunya, wacce ke jiran hukunci a cibiyar gyara hali a jihar.

Ga bidiyon tsitsiyeta da Hisbah ta yi a kasa:

Hukumar Hisbah dai ta bi ta kan shakiyan 'yan TikTok masu wallafa bidiyoyin da basu dace ba a kokarinta na tsarkake jihar daga masu aikata badala da nuna rashin tarbiyyah.

Kara karanta wannan

Hukumar Hisbah ta aikawa ‘yan iskan gari sako da aka daure Murja Kunya a kurkuku

Hisbah ta fito fili ta aika sako ga masu take hakkin addini da al'ada, musamman ta dandalin soshiyal midiya, inda ta ce ba za ta lamunci hakan ba.

Kasar Girka za ta hallata auren jinsi

A wani labari na daban, mun ji cewa a ranar Alhamis ne majalisar dokokin kasar Girka za ta hallata auren jinsi da daukar rainon yara, wani gagarumin sauyi da gwamnati ta dauka kan adawar Cocin Orthodox na kasar.

Ana sa ran da yawa daga cikin 'yan majalisar dokokin jam'iyyar New Democracy mai mulki za su yi adawa da kudurin a kuri'ar da za a kada a yammacin ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel