'Sun Koma Barayi': Ana Zargin Jami'an Tsaron da Gwamna Ya Kafa Suna Satar Dabbobi

'Sun Koma Barayi': Ana Zargin Jami'an Tsaron da Gwamna Ya Kafa Suna Satar Dabbobi

  • Jama’a na zargin jami’an tsaron da aka kafa a Sokoto na kwace shanu daga makiyaya ba tare da dalili ba, lamarin da ke tada hankula
  • Shugabannin yankin sun yi gargadin cewa wannan mataki na iya kara dagula tsaro, musamman a yankunan da ke fama da hare-hare
  • 'Yan gari sun bukaci gwamnatin Sokoto ta gudanar da bincike mai zaman kansa don gano gaskiyar lamarin domin yiwa tufkar hanci da wuri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sokoto - Tashin hankali na karuwa a kananan hukumomin Sabon Birni da Isa a Sokoto sakamakon zargin cewa jami'an tsaron jihar suna wuce gona da iri.

Legit Hausa ta rahoto cewa gwamnatin Sokoto ta kafa rundunar tsaronta domin kare kauyuka daga hare-haren ‘yan bindiga, amma yanzu an ce sun koma farmakar makiyaya Fulani.

Kara karanta wannan

Mayakan ISWAP sun kai hari Borno, sun yi barna kafin isowar sojoji

Mazauna Sokoto sun zargi jami'an tsaron jihar da satar dabbobi
Mazauna Sokto sun nemi gwamnati ta binciki jami'an tsaron jihar kan satar dabbobi. Hoto: @Ahmedaliyuskt
Asali: Twitter

Ana zargin jami'an tsaro da satar dabbobi

Rahoton Zagazola Makama ya nuna cewa ana zargin jami'an tsaron da kwace shanu daga hannun makiyaya masu kiwo a dazuka ba tare da wani dalili ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An jiyo cewa jami'an na sayar da shanun da suka kwace, kuma ana zargin suna saka kudaden a asusun gwamnati na kananan hukumomi.

Wani da ke da masaniya kan lamarin ya ce:

“Mu mun san ba wannan ne dalilin da aka dauke su aiki ba. Suna ikirarin cewa shanun na ‘yan bindiga ne, amma kuma sai su rika sayarwa.”

Karuwar tashin hankali kan jami'an tsaron jihar

Shugabannin al’umma sun yi gargadi cewa irin wannan mataki na iya dagula tsaro a yankin da ya dade yana fama da hare-hare.

Suna fargabar cewa kwace dabbobi ba tare da hujja ba zai haddasa karin bacin rai da kara dagula rikici a yankuna Isa da Sabon Birni.

Kara karanta wannan

El Rufa'i: Kotu ta umarci ICPC ta kwato sama da N1bn da aka karkatar a Kaduna

Ana kuma zargin cewa wasu jiga-jigan siyasa a gabashin Sokoto na kare wadanda ke da hannu a aikata ire-ire wadannan laifuffuka.

Wani dattijo a Sabon Birni ya ce: “Ko yara sun san wasu ‘yan siyasa na kare miyagu, amma gwamnati ba ta daukar mataki.”

“Yanzu su ne suka ba da damar kwace shanu ba tare da tabbatar da cewa na ‘yan bindiga ne ba. Wannan zai jefa yankin cikin matsala.”

An nemi gwamnatin Sokoto ta yi bincike

An aika sako ga gwamnatin Sokoto da ake zargin jami'an tsaron jihar na satar dabbobi
Gwamna Ahmad Aliyu yayin kaddamar da rundunar tsaron jihar Sokoto. Hoto: @Ahmedaliyuskt
Asali: Twitter

Mazauna yankin da wasu masu ruwa da tsaki sun bukaci gwamnatin jihar Sokoto da hukumomin tsaro su gaggauta bincike.

Sun jaddada cewa ana bukatar yakar ‘yan bindiga, amma dole ne a yi hakan cikin adalci da bin doka.

Ana kuma bukatar bincike mai zaman kansa kan yadda ake sayar da shanun da aka kwace da kuma yadda ake batar da kudaden.

Wani masanin tsaro ya yi gargadin cewa idan ba a shawo kan wannan matsala ba, za ta haddasa rashin amincewa da jami'an tsaron.

Kara karanta wannan

'Dan bindiga ya tono sirrin 'yan ta'adda ga sojoji kafin 'yan uwasa su harbe shi

“Idan ba a sa ido kan jami'an tsaron da aka kafa a jihar ba, za su iya zama matsala maimakon mafita ga matsalar tsaro. Dole a binciki duk wani korafi," inji masanin.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, gwamnatin jihar Sokoto ba ta fitar da wata sanarwa kan zargin da ake yi ba.

Sai dai ana ci gaba da matsin lamba ga hukumomi don daukar matakin gaggawa domin dakile tabarbarewar tsaro a yankin.

Majalisar Sokoto ta amince da kafa rundunar tsaro

Tun da fari, mun ruwaito cewa, majalisar dokokin Sokoto ta amince da ƙudirin da Gwamna Ahmed Aliyu ya gabatar don kafa rundunar tsaro a fadin jihar.

A zaman ta na Laraba, 20 ga Disambar 2023, majalisar jihar ta amince da kafa rundunar tsaro mai suna Community Guards Corps don inganta tsaro a Sokoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.