Kotu Ta Daure Yar Tik-Tok Shekaru 2 a Gidan Yari Saboda Zagin Shugaban Kasa

Kotu Ta Daure Yar Tik-Tok Shekaru 2 a Gidan Yari Saboda Zagin Shugaban Kasa

  • Kotu ta tura wata yar TikTok, Ana da Silva Miguel, magarkama saboda cin mutuncin shugaban kasar Angola
  • Matashiyar ta garzaya shafinta na TikTok inda ta yi kalaman cin mutunci a kan Shugaba João Lourenço
  • Da farko watanni shida aka yanke mata amma sai kotun daukaka kara ta tsawaita hukuncin zuwa shekaru biyu

Kotun kasar Angola ta tura wata yar TikTok mai suna Ana da Silva Miguel, gidan yari na tsawon shekaru biyu kan zagin shugaban kasarsu, João Lourenço.

Da farko kotun ta yankewa shahararriyar yar TikTok din da aka fi sani da Neth Nahara, hukuncin watanni shida a gidan yari a watan Agusta.

Kotu ta tura yar TikTok gidan yari kan zagin shugaban kasa
Kotu Ta Daure Yar Tik-Tok Shekaru 2 a Gidan Yari Saboda Zagin Shugaban Kasa Hoto: Ver Angola/AllNews Nigeria
Asali: UGC

Sai dai kuma, wata kotun daukaka kara ta zartar da cewar hukunci ya yi sassauci da yawa sannan ta daga shi zuwa shekaru biyu a gidan yari, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tinubu Na Shawarar Kirkiro Kotun Musamman Domin Daure Barayin Gwamnati

Dalilin garkame yar TikTok a kasar Angola

Ms Miguel ta garzaya shafinta na TikTok mai suna @nethnahara.yaya inda ta zargi shugaban kasar da mulki na rashin tsari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta kuma ga laifin shugaban kasar kan rashin makarantu, gidaje da ayyukan yi a kasar ta Kudancin Afrika mai albarkatun man fetur.

An sake zaben Shugaba Lourenço a karo na biyu a watan Agustan shekarar da ta gabata a zaben da aka gwabza da shi wanda ya tsawaita mulkin jam'iyyar MPLA na tsawon shekaru da dama.

Jam'iyyar ta kasance a kan mulki tun 1975 kuma an zarge ta da jagorantar mulkin danniya.

Kotun daukaka karar a Luanda, babban birnin kasar, ta bayyana cewa Ms Miguel ta yi amfani da kalaman batanci kan shugaban kasar, kuma kasancewar ra'ayinta zai iya tasiri a cikin al'umma shine yasa abun da ta yi ya zama abun kyama.

Kara karanta wannan

Sanatoci 107 Sun Tsoma Baki a Lamarin Tinubu v Atiku, Su na Goyon Bayan Shugaban Kasa

Yar TikTok ta nemi sassauci amma kotu ta ki amsa rokonta

Ta roki sassauci saboda wannan shine karo na farko da take aikata laifi sannan ta kasance uwa ga kananan yara tare da yin nadamar furucinta, rahoton BBC.

Sai dai kuma, kotun ta yi watsi da rokonta sannan ta umurceta da ta biya shugaba Lourenço $1,200 (£1,000) na bata masa suna da ta yi.

Mai shari'a Salomão Raimundo Kulanda ya bayyana shugaban kasar a matsayin "mai mulki" kuma cewa yar TikTok din na sane da hakan.

Ms Miguel tana da mabiya sama da 230,000 a dandalin TikTok, akuma bidiyoyinta ya ja hankalin dubban masu kallo.

Lauyanta ya bayyana cewa wannan shine karo na farko da ake hukunta mutum a Angola kan abun da suka wallafa a TikTok.

Lauyan ya kara da cewar hukuncin shine karshe. Ba za a iya daukaka kara a kotun koli kan hukuncin da ya yi kasa da shekaru uku ba.

Kara karanta wannan

Yanzu aka fara: Sanata ya ce mulkin Tinubu ya dace da Najeriya, ya fadi dalilai

Mai gabatar da kara na kasar ya nemi a yanke mata hukunci mai tsauri, yana mai cewa hukuncin farko da aka yanke mata na watanni shida yana tattare da "tausayi" kuma akwai yiwuwar Ms Miguel za ta sake irin wannan wallafar a dandalin sada zumunta.

Angola na daya daga cikin manyan kasashen da ke fitar da mai a Afirka, amma yawancin mutanenta na fama da talauci.

A baya-bayan nan dai ta fuskanci zanga-zanga saboda tsadar rayuwa da ake ciki.

Matashi ya fusata bayan mai aikinsa ta wanke masa laftof da ruwa da sabulu

A wani labari na daban, mun ji cewa wani dan Najeriya ya cika da mamaki bayan ya kama mai aikin gidansa tana yin ayyuka ba yadda ya kamata ba.

A cikin bidiyon da ya yadu a TikTok, mutumin ya shigo sai ya tarar da matar tana amfani da ruwa da sabulu wajen wanke kayan wutan gidan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel