An Tono Yadda aka Kayata Gidan Buhari na Kaduna Ya Dawo Kamar a Turai

An Tono Yadda aka Kayata Gidan Buhari na Kaduna Ya Dawo Kamar a Turai

  • Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya koma gidansa da ke Kaduna bayan shafe lokaci a Daura, jihar Katsina
  • Rahotanni sun nuna cewa an rushe tsohon gidan nasa, sannan an sake ginawa daga tushe ta hannun wani kamfanin gine-gine
  • Ana tunanin gwamnatin tarayya ce ta dauki nauyin sabunta gidan bisa tanadin da doka ta ba tsofaffin shugabannin kasa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya koma Kaduna, inda ya zauna a tsohon gidansa da ke kan titin Sultan a GRA.

Tun bayan barinsa mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023, Buhari ya kasance a garinsu na Daura, jihar Katsina, kafin wannan sabon matakin.

Buhari
Bayanai kan gidan da Buhari ya koma a Kaduna. Hoto: Kashim Shettima
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta hada wani rahoto na musamman kan komawa Kaduna da Buhari ya yi da yanayin gidan da ya koma.

Kara karanta wannan

Tinubu ya gwangwaje Farfesa Jega da babban mukami a gwamnatinsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa dama zama a Daura bayan barin mulki da ya yi hanya ce ta wucin gadi yayin da ake sake gina gidansa na Kaduna.

Bayan an rushe tsohon gidan, daya daga cikin manyan kamfanonin gine-gine a Najeriya ne ya sake gina shi daga tushe.

Zaman Buhari a Kaduna kafin zaben 2015

Kafin rantsar da shi a matsayin shugaban kasa a ranar 29 ga Mayu, 2015, Buhari ya fi zama a wannan gida da ke Kaduna.

Gidan da aka gina tun yana soja babba ne amma ba shi da wani kyau, musamman idan aka kwatanta shi da gidajen wasu tsofaffin shugabanni.

A baya, manyan baki da suka ziyarci gidan sun sha mamakin yadda yake duk da matsayinsa a wancan lokacin.

A tsawon shekara takwas da ya yi yana mulki, ba a yi wa gidan wani gagarumin gyara ba, kasancewar Buhari na fiye hutawa a Daura.

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi rashi: Tsohon hadimin shugaban kasa ya rasu yana da shekaru 72

Yadda aka gyara gidan Buhari na Kaduna

Bayan zama a Daura, Buhari ya yanke shawarar komawa Kaduna, amma a wannan karon a sabon gida da aka tsara da sake gina shi yadda ya dace da matsayin tsohon shugaban kasa.

Mutane da dama sun yi mamakin yadda sabon ginin ya fito, kasancewar Buhari mutum ne da ke kaffa-kaffa da rayuwa mai sauki.

Sai dai an samu bayani cewa ana iya cewa gwamnatin tarayya ce ta dauki nauyin sabunta gidan bisa tanadin da doka ta yi.

A matsayin tsohon shugaban kasa, Buhari na da hakkin samun wasu fa’idoji da suka hada da:

  • Kula da lafiyarsa da ta iyalansa kyauta
  • Hutun kwanaki 30 a kowace shekara a cikin ko wajen Najeriya
  • Gida mai dakuna biyar a kowane gari da yake so

Rahotanni sun nuna cewa watakila Buhari ya amfana da wannan damar don yin aiki a gidansa na Kaduna, wanda yanzu ke da gine-gine da suka maye gurbin filayen da ke cikin gidan a baya.

Kara karanta wannan

Kwamishinonin El Rufa’i sun bayyana gaskiyarsu kan zargin karkatar da N1.37bn

An kuma lura cewa sabon fentin gidan mai haske sosai ya sa ya fice daga cikin sauran gidaje a unguwar.

Buhari
Lokacin da aka raka Buhari gidansa na Kaduna. Hoto: Kashim Shettima
Asali: Twitter

Fadar shugaban kasa ta ki magana

Duk da yunkurin jin ta bakin fadar shugaban kasa game da wannan cigaban, mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin labarai, ya ki cewa komai.

Sai dai wata majiya daga fadar shugaban kasa ta shaida cewa harkokin jin dadin tsofaffin shugabanni na hannun ofishin sakataren gwamnatin tarayya ne.

'Dan Tinubu ya ziyarci Buhari a Kaduna

A wani rahoton, kun ji cewa dan shugaban kasa Bola Tinubu mai suna Seyi ya ziyarci shugaba Muhammadu Buhari a gidansa na Kaduna.

Seyi Tinubu ya ziyarci Buhari ne a wani rangadi da ya fito wasu jihohin Arewa ta Yamma inda aka ga ya ziyarci Kano, Kaduna da Neja.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng