Sharif Lawal
8218 articles published since 17 Fab 2023
8218 articles published since 17 Fab 2023
Ana zargin jami'an hukumar NSCDC da hallaka wata mata a filin Idi a jihar Zamfara. Jami'an 'yan sanda sun fara gudanar da bincike domin gano gaskiya kan lamarin.
Tsohon alkalin kotun daukaka, Ahmad Olarewaju Belgore, ya yi bankwana da duniya yana da shekara 71. An bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi.
Al'ummar Musulmai a fadin duniya suna gudanar da bukukuwa a lokacin Eid-el-fitr. Sai dai, akwai wasu kasashen da ba su ayyana hutu a ranar bikin.
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yi umurni da a biya dukkanin ma'aikatan jihar N10,000 domin su gudanar da bukukuwan Sallah cikin nishadi.
Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bukaci 'yan Najeriya da su ci gaba da marawa shugaban kasa Tinubu baya.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar kai farmaki a maboyar wani kasurgumin shugaban 'yan ta'adda a jihar Zamfara. Sun hallaka dan ta'adda daya.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya ayyana ranar Juma'a, 12 ga watan Afirilun 2024, a matsayin ranar hutu ga ma'aikata domin bukukuwan karamar Sallah.
Wasu miyagun 'yan daba sun je har gida inda suka tafka ta'asa a gidsn tsohon gwamnan jihar Benuwai, Aper Aku. 'Yan daban a yayin farmakin sun kona gidan kurmus.
Wata babbar kotu a jihar Kano ta sanya ranar da za ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da matarsa kan zargin cin hanci.
Sharif Lawal
Samu kari