Zamfara: Sojoji Sun Samu Gagarumar Nasara Kan Kasurgumin Shugaban 'Yan Ta'adda

Zamfara: Sojoji Sun Samu Gagarumar Nasara Kan Kasurgumin Shugaban 'Yan Ta'adda

  • Dakarun sojojin Najeriya sun kai samame a maɓoyar shugaban ƴan ta'adda a jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya
  • Jami'an tsaron sun samu nasarar lalata maɓoyar ɗan ta'addan da ya addabi mutane tare da sheƙe ɗaya daga cikin mayaƙansa
  • A yayin samamen sojojin sun kuma ƙwato makamai tare da buhunan hatsi na sata a maɓoyar ta Janbros

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Dakarun sojojin Najeriya da aka tura domin yaƙi da ta'addanci a jihar Zamfara sun kai samame maɓoyar wani shugaban ƴan ta'adda mai suna Yello Janbros.

A yayin farmakin sojojin sun samu nasarar kashe ɗan ta'adda ɗaya bayan sun yi musayar wuta.

Sojoji sun farmaki 'yan ta'adda
Sojoji sun lalata maboyar Yellow Janbros Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Sojojin sun kuma ƙwato makamai da dama tare da lalata maɓoyar ƙasurgumin ɗan ta'addan, Yellow Janbros.

Kara karanta wannan

Rundunar sojoji ta dauki mataki kan 'yan ta'addan da suka farmaki jami'anta a Borno

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar wata sanarwa da rundunar sojojin Najeriya ta fitar a ranar Talata a shafinta na X, Janbros ya daɗe yana yin garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta'addanci a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Wace nasara sojojin suka samu?

Sanarwar ta ƙara da cewa

"Dakarun Sojojin Najeriya da aka tura domin yaƙi da ƴan ta’adda sun kai samame a maɓoyar wani fitaccen ɗan ta’adda da aka fi sani da Yellow Janbros da ke ƙauyen Dangunu a ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara."
A yayin samamen da aka kai a ranar 8 ga watan Afrilu, 2024, sojoji sun yi nasarar farmakar maɓoyar ƴan ta’addan da suka yi ƙaurin suna wajen yin garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya."
"Dakarun sojojin sun samu galaba tare da fatattakar ƴan ta’addan da kashe ɗaya daga cikinsu."

Kara karanta wannan

'Yan bindigan da suka sace dalibai a Arewa sun bayyana kudin fansan da za a ba su

"Sojojin sun kuma kwato bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya, jigida ta bindigar AK-47 guda ɗaya, harsasai na musamman masu kaurin 7.62mm guda 30, da kuma buhunan hatsi na sata da suka kai 150. An lalata maɓoyar ƴan ta'addan gaba ɗaya."

Sojoji sun sheƙe ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarunta sun samu nasarar kashe ƴan ta'adda a jihar Kaduna.

Kakkabe ƴan ta’addan dai ya faru ne a wani harin kwantan bauna da aka kai musu yankin Kidandan cikin ƙaramar hukumar Giwa ta jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel