Kotu Ta Sanya Ranar Gurfanar da Ganduje Tare da Iyalansa Kan Zargin Cin Hanci

Kotu Ta Sanya Ranar Gurfanar da Ganduje Tare da Iyalansa Kan Zargin Cin Hanci

  • Wata babbar kotu da ke zamanta a jihar Kano ta sanya ranar da za ta gurfanar da Abdullahi Umar Ganduje, ɗansa da wasu mutum shida
  • Za a gurfanar da tsohon gwamnan na jihar Kano ne a ranar 17 ga watan Afirilun 2024 tare da sauran waɗanda ake tuhuma a ƙarar da gwamnatin Kano ta shigar
  • A cikin ƙarar dai ana yi wa Ganduje da sauran mutanen tuhume-tuhume har guda takwas da suka haɗa da cin hancin $413,000 da N1.38bn

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Wata babbar kotu a jihar Kano ta sanya ranar da za ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, matarsa, da wasu mutum shida.

Kara karanta wannan

Fitacciyar jarumar Kannywood Saratu Gidado (Daso) ta rasu

Kotun ta sanya ranar 17 ga watan Afirilun 2024, a matsayin ranar da za ta gurfanar da Ganduje tare da sauran mutanen, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kotu ta sanya ranar gurfanar da Ganduje
Kotu ta tsayar da ranar gurfanar da Ganduje kan zargin cin hanci Hoto: Abdullahi Umar Ganduje - OFR
Asali: Facebook

Meyasa za a gurfanar da Ganduje?

Waɗanda ake tuhumar za a gurfanar da su a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume takwas da suka hada da zargin karɓar cin hancin Dala, karkatar da kuɗaɗe da almubazzaranci da cin hancin $413,000 da N1.38bn da dai sauransu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran waɗanda ake ƙara a ƙarar sun haɗa da Abdullahi Umar Ganduje, Hafsat Umar, Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, Lamash Properties Ltd, Safari Textiles Ltd da Lesage General Enterprises.

Gwamnatin jihar Kano a ƙarar da ta shigar a gaban kotu ta ce ta tattara shaidu 15 da za su bayyana a gaban Kotu.

Me gwamnati ta ce kan lamarin?

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Antoni Janar na jihar, Haruna Isah Dederi, ya ce an shigar da ƙarar, kuma za a sanar da duk waɗanda abin ya shafa, rahoton jaridar Punch ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Miyagun ƴan bindiga sun kashe mutum 2, sun yi garkuwa da ɗan takarar gwamna

A kalamansa:

"Eh gaskiya ne. Mun shigar da ƙarar amma abin da ba zan iya tabbatarwa ba shi ne ko an yi sanar da shi ba a sanar da shi ba."
"Abin da shi (Ganduje) bai gane ba shi ne, ba za ka iya gujewa abin da ka shuka ba, tabbas zai zo gare ka, kuma hakan ma zai zama darasi ga dukkanmu."
"Yana mai cewa ba za mu iya tuhumarsa ba ya manta cewa laifin yana a ƙarƙashin sashin laifuffukan jiha. Kwata-kwata ba al’amarin tarayya ba ne."

A cikin ƴan kwanakin nan ne Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sha alwashin bincikar Ganduje inda ya ce ya zubar da ƙimar jihar Kano.

Za a binciki Ganduje a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kafa kwamitocin shari'a guda biyu (JCIs) da za su binciki yadda aka karkatar da kadarorin gwamnati daga 2015 zuwa 2023.

Kwamitocin za su binciki tashin hankulan da aka samu da rahoton ɓacewar yara a lokutan zaɓen 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel