Yadda Masu Amfani da MTN za Su Samu Tallafin N50,000
- Masu amfani da layin MTN da aka zaɓa domin amfana da tallafin Naira 50,000 na gwamnatin tarayya za su iya tantance matsayinsu ta lambar MoMo PSB ta USSD
- Kamfanin MTN ya gargaɗi masu amfani da layinsa kan wani saƙon bogi da ke yaɗuwa a kafafen sada zumunta, wanda ke neman su aika da kalmar “YES” zuwa wata lamba
- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ba sai an yi rajista ko an biya kuɗi ba kafin mutum ya samu tallafin, kuma za a sanar da waɗanda suka cancanta ta saƙon SMS
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Masu amfani da layin kamfanin sadarwa na MTN da aka zaɓa domin cin gajiyar tallafin N50,000 na gwamnatin tarayya za su iya tantance matsayinsu da kuma amincewa da karɓar kuɗin ta hanyar amfani da lambar USSD ta MoMo.

Kara karanta wannan
Tallafin N50,000: Gwamnatin Tarayya ta fitar da ka'idoji 4, ta ja kunnen 'yan Najeriya
Tallafin na ƙarƙashin shirin NERSI, wanda aka ƙaddamar domin tallafa wa iyalai masu ƙaramin ƙarfi a Najeriya.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa matakin ya zo ne a daidai lokacin da wani saƙon bogi ke yaɗuwa a kafafen sada zumunta, inda ake yaudarar masu amfani da MTN da su aika da kalmar “YES” zuwa wata lamba domin a ba su kuɗin cikin sa'o'i 24.
Yadda ake samun tallafin ta MTN
Shafin hukuma na shirin NERSI ya bayyana cewa akwai hanyoyin da waɗanda aka zaɓa za su bi domin tabbatar da cancantarsu da amincewa da karɓar tallafin.
Ga masu amfani da MTN, MoMo PSB ne kamfanin da aka ware domin biyan kuɗin tallafin. Waɗanda suke son tantance matsayinsu za su bi waɗannan matakai:
- Danna lambar USSD: Mai amfani da MTN zai danna *671*0# daga lambar wayar da aka yi rajista da ita, sannan ya bi umarnin da zai bayyana domin tantance matsayinsa.
- Amincewa da tallafin: Idan mutum ya samu saƙon hukuma da ke tabbatar da cewa an zaɓe shi, zai bi umarnin da ke cikin saƙon ko ya yi amfani da lambar USSD domin amincewa da karɓar kuɗin.
- Amsa saƙon MoMo: Idan sanarwar MoMo ta gaskiya ta bayyana a wayar mutum tana neman ya amince da tallafin, zai bi umarnin da aka bayar domin tabbatar da amincewarsa.
- Buɗe asusun MoMo: Waɗanda ba su da asusun MoMo za su iya danna *671# ko sauke manhajar MoMo NG ta hukuma domin buɗe asusu.
- Karɓar kuɗin: Bayan an tura Naira 50,000 zuwa asusun MoMo na wanda ya cancanta, zai iya amfani da manhajar, lambar USSD ko wakilin MoMo wajen cire kuɗin. Haka kuma, zai iya tura kuɗin zuwa asusun bankinsa.

Source: Facebook
Yadda ake tura kudin ta Moniepint
A wani labarin, kun ji cewa kamfanin Moniepoint ya fitar da ƙarin bayani kan yadda waɗanda suka cancanci tallafin N50,000 na gwamnatin tarayya za su karɓi kuɗinsu.
Kamfanin ya bayyana cewa waɗanda suka samu saƙon SMS na sanar da biyan tallafin za su yi amfani da lambar USSD da aka aika musu domin amincewa da karɓar kuɗin.
Moniepoint ta kuma yi bayani kan abin da mutum zai yi idan ya samu saƙon kuskure yayin amfani da lambar *5573*27#, tare da bayyana lokacin da ake sa ran kuɗin zai shiga.
Asali: Legit.ng