'Yan Ta'adda da Dama Sun Mutu a Wani Sabon Fada Tsakanin Mayakan ISWAP da Boko Haram

'Yan Ta'adda da Dama Sun Mutu a Wani Sabon Fada Tsakanin Mayakan ISWAP da Boko Haram

  • Mayaƙan ƙungiyoyin ta'addanci na ISWAP da Boko Haram sun gwabza wani sabom ƙazamin faɗa a tsakaninsu
  • Mummunan artabun ya auku ne a yankin tsibirin tafkin Chadi bayan mayaƙan Boko Haram na Bakoura Buduma sun kai farmaki a sansanin ISWAP
  • Bayan gwabza ƙazamin artabu, an hallaka mayaƙa masu yawan gaske na ƙungiyoyin biyu masu gaba da juna

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

An gwabza mummunan sabon faɗa tsakanin mayaƙan ƙungiyoyin ta'addanci na ISWAP da Boko Haram.

Ƙazamin faɗan da ƴan ta'addan suka yi ya jawo an yi asarar rayukan mayaƙa masu yawa daga ƙungiyoyin biyu.

'Yan ta'adda sun gwabza fada
'Yan ta'addan ISWAP da Boko Haram sun gwabza fada Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Rikicin dai ya ɓarke ne tsakanin mayaƙan ISWAP da na ɓangaren Boko Haram na Bakoura Buduma wanda aka fi sani da Abou Umaymah.

Kara karanta wannan

Barka da Sallah: Ganduje ya bayyana abin da 'yan Najeriya ya kamata su yi wa Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda rikicin ya auku

Rikicin ya auku ne a tsibirin Kukiri da Lelewa da ke gabar tafkin Chadi a Jamhuriyar Nijar.

Wata majiya mai tushe ta shaidawa Zagazola Makama, masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, cewa rikicin ya fara ne da yammacin ranar Alhamis.

An tattaro cewa Abu Umaima Ari Kau shi ne ya jagoranci mayaƙan Buduma inda suka kai hari a sansanin ƴan ta'addan ISWAP.

Mayaƙan sun tashi ne daga Lelewa da Gadira a Bosso na yankin Diffa a jamhuriyar Nijar tare da ƙaddamar da sabon farmaki a sansanin, inda suka kashe mayaƙan ISWAP da dama.

Zagazola ya yi hasashen cewa za a ci gaba da gwabaza bata kashi a tsakanin ɓangarorin biyu cikin makonni masu zuwa.

Ƴan ta'adda sun hallaka soja

A baya kun ji cewa wasu ƴan ta’adda da ake fargabar ‘yan Boko Haram ne sun kai hari a wani sansanin soji da ke garin Gujba da ke karamar hukumar Gujba a jihar Yobe.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun fadi babbar nadamar da yankin ya yi kan zaben Shugaba Bola Tinubu

Maharan masu ɗauke da makamai sun kashe wani jami’in soji tare da lalata motocin sintiri na sojoji a jihar.

Faɗan ISWAP da Boko Haram

A wani labarin kuma, kun ji cewa mayaƙan ƙungiyar ƴan ta'adda ta ISWAP sun kai farmaki kan ƴan ta'addan Boko Haram.

Faɗan da aka yi da aka yi a Tumbun Rago ya yi sanadiyyar zubar da jini yayin da ƙungiyar Boko Haram ta yi asarar rayuka da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel