Ana Cikin Azumi 'Yan Daba Sun Kona Gidan Tsohon Gwamna a Jihar Arewa, Bayanai Sun Fito

Ana Cikin Azumi 'Yan Daba Sun Kona Gidan Tsohon Gwamna a Jihar Arewa, Bayanai Sun Fito

  • Wasu ƴan daba sun ƙona gidan tsohon gwamnan jihar Benuwai, marigayi Aper Aku da ke a yankin Gboko na jihar
  • Ƴan daban sun ƙona gidan ne bayan wata taƙaddama ta faru inda wani mutum ya yi zargin cewa akuyarsa ta rasu sakamakon shan ruwan gidan
  • Ɗiyar marigayi tsohon gwamnan wacce ta tabbatar da aukuwar lamarin ta ce ƴan sanda sun samu nasarar kwashe su daga gidan kafin a cinna masa wuta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benuwai - Rahotanni sun ce ƴan daba sun ƙona gidan tsohon gwamnan jihar Benuwai marigayi Aper Aku da ke yankin Gboko a jihar.

Lamarin ya faru ne a ranar Litinin bayan an yi nasarar kwashe mutanen da ke cikin gidan, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Mataimakin kakakin majalisa Kalu ya sha alwashin duba batun karin kudin wuta

'Yan daba sun kona gidan tsohon gwamnan Benuwai
'Yan daba sun tafka ta'asa a gidan tsohon gwamnan jihar Benuwai Hoto: @PoliceNg
Asali: Facebook

Ɗiyar tsohon gwamnan, Deborah Aku, ta shaida wa manema labarai a Makurdi cewa ƴan sanda sun ceto mutum shida kafin ƴan daban su ƙona gidan, rahoton jaridar Daily Post ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda abin ya auku a Benuwai

Ta bayyana cewa rikicin ya fara ne tun a watan Maris bayan da wani mutum ya zo gidan da adda tare da yin barazanar ɗaukar mataki a kansu idan akuyarsa ta sake mutuwa, inda ya ce an gaya masa cewa akuyar tasa ta mutu ne bayan shan ruwan gidan.

Aku ta ce mahaifiyarta ta kai rahoton lamarin ga ofishin ƴan sanda da ke Gboko kuma daga baya aka kai lamarin a gaban kotu.

Sai dai ta ƙara da cewa sabon harin ya faru ne tsakanin karfe 7:00 zuwa ƙarfe 8:00 na safiyar ranar Litinin lokacin da ƴan daban suka yiwa gidan ƙawanya tare da kulle dukkanin mutane shida da ke ciki.

Kara karanta wannan

Miyagun ƴan bindiga sun kashe mutum 2, sun yi garkuwa da ɗan takarar gwamna

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

A halin da ake ciki, jami’ar hulɗa da jama’a ta ƴan sandan jihar, SP Catherine Anene, ta tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a ranar Talata a Makurdi.

Sai dai, Anene, ta ce ba ta da ƙarin cikakkun bayanai kan lamarin har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

An farmaki gidan ɗan majalisa

A wani labarin kuma, kun ji cewa Ƴan bindiga sun kai farmaki a gidan ɗan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar Logo-Ukum-Katsina Ala, Solomon Wombo.

Ƴan bindigan sun kai harin ne a gidan ɗan majalisar wanda yake a birnin Makurdi, babban birnin jihar Benuwai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel