Shugaban Isra'ila ya zaɓi Eisenkot maimakon Netanyahu a kafa sabuwar gwamnati
- Isaac Herzog, ya zaɓi Gadi Eisenkot maimakon Benjamin Netanyahu domin kafa sabuwar gwamnati a Israila bayan zabe
- Tsohon sojan yana da kwanaki 28, tare da yiwuwar ƙarin kwanaki domin samun kujeru 61 da ake buƙata a kafa gwamnati
- Jam'iyyun Larabawa sun goyi bayansa domin kawo ƙarshen mulkin Netanyahu, duk da har yanzu akwai ƙalubale gabansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Israel - Tsohon sojan yana da kwanaki 28, tare da yiwuwar ƙarin kwanaki domin samun kujeru 61 da ake buƙata don kafa gwamnati.
Jam'iyyun Larabawa sun goyi bayansa domin kawo ƙarshen mulkin Netanyahu, duk da cewa har yanzu akwai ƙalubale gabansu.

Source: Getty Images
An dauko Gadi Eisenkot, an kyale Benjamin Netanyahu
Gadi Eisenkot, yana da kwanaki 28 domin kafa gwamnatin haɗin gwiwa da za ta kawo ƙarshen mulkin Benjamin Netanyahu na tsawon shekaru.
Shugaban ƙasar Isra'ila ya zaɓi Gadi Eisenkot domin ya kafa sabuwar gwamnati, ya ƙyale Benjamin Netanyahu, duk da shi ne babban abokin adawarsa.

Kara karanta wannan
"Nan ba da daɗewa ba yan Najeriya za su fara murna da tsare tsaren Shugaba Tinubu"
Reuters ta ce Kakakin shugaban ƙasar ya ce Herzog ya sanar da Eisenkot wannan shiri daren Asabar, kuma za a miƙa masa takardar izinin kafa gwamnati.
A makon nan Herzog ya gana da jam'iyyun siyasa domin tantance wanda zai ba damar kafa gwamnati, ganin babu wanda ya iya lashe zaɓen Oktoba.
Babu wanda ya iya lashe zaben Israila?
'Yan majalisar dokoki 67, ciki har da wakilan jam'iyyun Larabawa, sun goyi bayan tsohon hafsun sojoji, Eisenkot, wanda shi ne shugaban jam'iyyar Yashar.
Sai dai 'yan majalisa 46 ne kawai suka goyi bayan Netanyahu don haka ake ganin zai bar kujerarsa.
Eisenkot zai samu kwanaki 28, tare da yiwuwar ƙarin kwanaki 14, domin haɗa kawancen jam'iyyun da za su ba shi aƙalla kujerun majalisa 61 cikin 120.
A zaɓen da aka gudanar, masu goyon bayan Netanyahu sun samu kujeru 53. A gefe guda kuma jam’iyyun da suke tare da Eisenkot sun tashi da kujeru 43.
Hakan ya nuna cewa babu ɗaya daga cikinsu da ya samu kujeru 61 da ake buƙata domin kafa gwamnati.
Hada kai da jam'iyyun Larabawa
Jam'iyyun Larabawa da ke wakiltar Falasɗinawa 'yan ƙasar Isra'ila sun samu kujeru 19, wanda shne mafi yawan kujerun da suka taɓa samu wajen takarar.
Sai dai Eisenkot ba zai kafa gwamnati tare da jam'iyyun Larabawa ba idan ya samu goyon bayan manyan jam'iyyun Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi.
Kawancen shi da United Torah Judaism da Shas, zai iya jawo ya samu kujeru 61 a majalisa.
Nour Odeh, wakiliyar Al Jazeera da ke bayar da rahoto daga Ramallah a Yammacin Kogin Jordan, ta ce matakin shugaban Isra'ila ba abin mamaki ba ne.
An ji cewa Eisenkot ne ya samu mafi yawan goyon bayan 'yan majalisar Isra’ila a halin yanzu.
Babban ƙalubalen Mista Eisenkot yanzu shi ne kafa gwamnati da za ta samu amincewar majalisa, ba tare da karya alkawuran da ya yi wa jama’a ba.
Idan Eisenkot ya kasa kafa gwamnati a cikin wa'adin da aka ba shi, shugaban ƙasar zai iya zaɓar wani ɗan takara. Idan nan ma ya gaza, za a nemo wani.
Muddin duk waɗannan sun gaza, za a sake gudanar da zaɓe cikin kwanaki 90, yayin da Netanyahu zai ci gaba da riƙe muƙamin Firaminista na wucin gadi.
Haɗin kai domin kawar da gwamnatin Netanyahu
Eisenkot wanda ya jagoranci rundunar sojin Isra'ila daga shekarar 2015 zuwa 2019. Ya kuma kasance mai sa ido a kwamitin yaƙin Netanyahu a 2023.
Ahmad Tibi, wani babba a ƙungiyar haɗin gwiwar jam'iyyun Larabawa ta Joint List, ya shaida wa Al Jazeera cewa matakin shugaban abin da ake tsammani ne.
Ya ce sun damu da yiwuwar shugaban ƙasar ya zaɓi kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa tsakanin Eisenkot da Netanyahu, amma hakan bai faru ba.
A maimakon haka, jam'iyyun Larabawa sun goyi bayan Eisenkot domin samun damar kafa gwamnati.
Tibi ya bayyana cewa yana ganin Eisenkot zai iya kafa gwamnatin marasa rinjaye, wadda za ta samu goyon bayan jam'iyyun Larabawa daga waje.
Ya ce duk da cewa irin wannan gwamnati ba ita ce burin jam'iyyun Larabawa ba, babban abin da suke son cimmawa shi ne kawo ƙarshen Netanyahu.
Bayan haka an ji cewa manyan masu goyon bayansa su ne Itamar Ben-Gvir da Bezalel Smotrich.
An maida wa Netanyahu martani
Kafin sanarwar, Netanyahu ya yi gargaɗin cewa kafa gwamnati da 'yan adawa za su yi tare da goyon bayan jam'iyyun Larabawa zai jefa Isra'ila a cikas.
Netanyahu wanda ya shekara 77 kwanan nan ya yi ikirarin cewa gwamnati da ta dogara da masu ra'ayin Islama za ta rusa ƙasar Isra'ila daga cikin gida.
Sai dai Ahmad Tibi ya mayar masa da martani, inda ya zargi Netanyahu da kasancewa babban mai goyon bayan ta'addanci a Isra'ila da Gabas ta Tsakiya.
Ya zarge shi da abin da ya kira ta'addancin Yahudawa a Yammacin Kogin Jordan da sauran yankunan Falasɗinawa.
A ƙarshe, Nour Odeh, ta ce duk da cewa Eisenkot ya ce ba ya son kafa gwamnati tare da jam'iyyun Larabawa, za su yi hakan don ganin ƙarshen Netanyahu.
Asali: Legit.ng


