An Shiga Jimami Bayan Tsohon Alkalin Kotun Daukaka Kara Ya Rasu Yana da Shekara 71

An Shiga Jimami Bayan Tsohon Alkalin Kotun Daukaka Kara Ya Rasu Yana da Shekara 71

  • Tsohon alƙalin kotun ɗaukaka ƙara, Ahmad Olanrewaju Belgore ya rasu yana da shekara 71 a duniya
  • Shugaban ƙungiyar lauyoyin Najeriya reshen Ilorin, jihar Kwara, Kamaldeen Gambari ne ya bayyana hakan a ranar Talata, 9 ga watan Afrilu
  • Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya bayyana marigayi Belgore a matsayin cikakken mutumin kirki, ƙwararren jami’in shari’a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ilorin, jihar Kwara - Shugaban ƙungiyar lauyoyin Najeriya reshen Ilorin, jihar Kwara, Kamaldeen Gambari, ya sanar da rasuwar tsohon alƙalin kotun ɗaukaka ƙara, Ahmad Olanrewaju Belgore.

Gambari ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafin sada zumunta a ranar Talata, 9 ga watan Afrilu.

Mai shari'a Belgore ya rasu
Mai shari'a Ahmad Olanrewaju Belgore ya rasu Hoto: @justeventsonlin
Asali: Twitter

A kalamansa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya bi sahun Tinubu, ya kara ranakun hutun Sallah a jiharsa

"Bayanan da suka iso gareni a yanzu sun nuna cewa mai shari'a Ahmad Olarewaju Belgore, (mai ritaya) ya rasu. Allah ya gafarta masa kurakuransa."

Kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito, Belgore ya yi ritaya a matsayin alƙalin kotun ɗaukaka ƙara a ranar 18 ga watan Afrilun 2023, bayan ya kai shekara 70.

Sarkin Ilorin ya yi ta'aziyyar rasuwar Belgore

Sarkin Ilorin kuma shugaban majalisar sarakunan gargajiya ta jihar Kwara, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari ya bayyana rasuwar Belgore a matsayin babban rashi.

Sarkin ya yi ta’aziyya ga iyalan Belgore, ɗaukacin mutanen Ilorin da kuma ƴan Najeriya baki ɗaya, cewar rahoton jaridar The Punch.

Sarkin ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mai magana da yawun sa, Abdulazeez Arowona ya fitar.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Wannan babban rashi ne wanda ya faɗo a kan masarautar Ilorin da ƙasa baki ɗaya."
"Cikin kaɗuwa na samu labarin rasuwar mai shari'a Ahmad Belgore. Mutumin kirki ne, ƙwararren mai shari'a wanda ya hidimtawa ƙasar nan a mataki daban-daban cikin gida da ƙasashen waje."

Kara karanta wannan

InnalilLahi: Ƴan bindiga sun halaka jami'an tsaro 30 ana shirin ƙaramar sallah a Arewa

"Yana ɗaya daga cikin haziƙan alƙalan da masarautar Ilorin ta samar. Ya taimaka sosai wajen ci gaban ɓangaren shari'a."

Saratu Gidado ta rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa shahararriyar jarumar masana'antar fina-finai ta Kannywood, Saratu Gidado Daso ta riga mu gidan gaskiya.

Marigayiyar ta rasu ne a cikin barcinta bayan ta kammala cin abincin sahur a ranar Talata, 9 ga watan Afirilun 2024.

Asali: Legit.ng

Online view pixel