Jerin Kasashen da Ba Su Ayyana lokacin Eid-el-Fitr a Matsayin Ranar Hutu

Jerin Kasashen da Ba Su Ayyana lokacin Eid-el-Fitr a Matsayin Ranar Hutu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Lokacin bikin Eid-el-Fitr (bikin ƙaramar Sallah), lokaci ne mai albarka da ke nuna zuwan ƙarshen watan Ramadan.

Al'ummar Musulmai na amfani da lokacin wajen gudanar da bukukuwan Sallah a faɗin duniya.

Kasashen da ba su bada hutun Sallah
Amurka da Kanada na cikin kasashen da basu bada hutu ranar Sallah Hoto: ABDEL GHANI BASHIR/AFP
Asali: Getty Images

A ƙasashe da dama, gwamnatoci na ayyana ranar a matsayin ranar hutu domin ba al’ummar musulmi damar gudanar da bukukuwa da addu’o’i.

Ƙasashen da ba su ayyana hutun Eid-el-fitir

Sai dai akwai ƙasashen da ba ba su ayyana ranar Eid-el-Fitr a matsayin ranar hutu. Amma duk da haka Musulmai na gudanar da bukukuwan Sallah.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton jaridar Nigerian Tribune ya jero ƙasashen da ba su bada hutun ranar Eid-el-fitr a hukumance.

Kara karanta wannan

Goron Sallah: Gwamnan Bauchi ya faranta ran ma'aikatan jihar

Kanada

Ranar Eid-el-fitr ba ranar hutu ba ce a ƙasar Kanada duk da tana da al'adu da yawa.

Sai dai hakan bai hana musulmai gudanar da bukukuwan ƙarshen watan Ramadan da addu’o’i a faɗin ƙasar ba.

Brazil

A ƙasar Brazil ba a ayyana ranar Eid-el-fitr a matsayin ranar hutu.

Gwamnatin ƙasar ta yankin Amurka ta Kudu ba ta ayyana hutu domin bikin Eid-el-fitr.

Argentina

Argentina, kamar makwabciyarta Brazil ba ta amince da Eid-el-fitir a matsayin ranar hutu ba.

Domin haka, ranar Idi ba ranar hutu ba ce a ƙasar mai jama'a da mafi yawancinsu mabiya ɗariƙar Katolika ne.

Amurka

Ƙasar Amurka ba ta bada hutu domin gudanar da bikin Eid-el-fitr duk da yawan al'ummar Musulmai da ake da su a ƙasar.

Duk da haka, an ba Musulmai damar yin bikin ranar tare da iyalai da abokai a cikin yankunansu. Suna taruwa domin yin addu'o'i da bukukuwa.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya bi sahun Tinubu, ya kara ranakun hutun Sallah a jiharsa

Afirka ta Kudu

Ƙasar Afirika ta Kudu ba ta ayyana ranar Eid-el-fitr a matsayin ranar hutu a ƙasar ba.

Sai dai, al'ummar Musulmai na taruwa domin gudanar da bukukuwan Sallah a yankunansu.

Ingila

Ƙasar Ingila, wacce ke da al'umma daban-daban, ba ta sanya ranar bikin Eid-el-fitir a cikin ranakun da take bada hutu ba.

Faransa

Faransa ba ta ayyana ranar Eid-el-fitr a matsayin ranar hutu ba, duk da yawan al'ummar Musulmai da take da su.

Musulmai, duk da haka, suna tunawa da ranar ta hanyar tarurruka da bukukuwa.

Italiya

Italiya, wacce mafiya yawan mutanenta mabiya ɗariƙar Katolika ne ba ta amince da ranar Eid-el-fitr a matsayin ranar hutu ba.

Ranar, wacce ke da muhimmanci ga Musulmai ba ta da matsayin ranar hutu a Italiya.

Sauran ƙasashen su ne:

  • Netherlands
  • Switzerland
  • Rasha
  • Australia

Gwamna Radda ya ƙara ranakun hutun Sallah

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Radda, ya ƙara ranakun hutun ƙaramar Sallah.

Gwamnan ya ayyana ranar Juma'a, 12 ga watan Afirilu a matsayin ranar hutu domin bukukuwan Sallah.

Asali: Legit.ng

Online view pixel