Hatsabibin Ɗan Bindiga Ya Sha Harbi, an Cafke Shi bayan Ya Je Asibiti Jinya

Hatsabibin Ɗan Bindiga Ya Sha Harbi, an Cafke Shi bayan Ya Je Asibiti Jinya

  • Dakarun sojojin Najeriya sun cafke fitaccen dan bindiga, Auta Maikyala, a wani asibiti da ke garin Kagarko a jihar Kaduna
  • Binciken farko ya nuna cewa Maikyala na da hannu a hare-haren al'umma, satar mutane da satar shanu a wasu yankuna
  • Sojoji sun lalata maboyar 'yan bindiga a Zamfara, yayin da rundunar sojin sama ta kai hari wuraren da ake zargin maboyar Dogo Gide ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Dakarun sojojin Najeriya sun cafke wani fitaccen dan bindiga da ake zargi da ta'addanci, Auta Maikyala, a wani asibiti da ke garin Kagarko a jihar Kaduna

An cafke wanda ake zargin ne yayin wani samame da sojoji suka gudanar tare da jami'an hukumar DSS, bisa sahihan bayanan sirri.

An cafke dan bindiga a asibitin Kaduna
Taswirar jihar Kaduna da yan bindiga ke yawan kai hare-hare. Hoto: Legit.
Source: Original

Yadda aka kama dan bindiga a asibiti

Kara karanta wannan

Malamin da aka cire a limanci saboda goyon bayan Tinubu ya lashe amansa

Rundunar sojin ta ce binciken farko ya nuna cewa Maikyala na da hannu a hare-haren al'umma, satar mutane da satar shanu a yankin, cewar PM News.

Kakakin rundunar Operation FANSAN YAMMA, Kyaftin Sinive Tamuno, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma'a.

Ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar 5 ga watan Nuwambar 2026 a wani asibiti da ke Kagarko, inda ya je neman magani sakamakon raunin harbin bindiga da ya samu.

Majiyoyi sun nuna cewa ya samu raunin ne bayan arangama da wasu 'yan kungiyar masu aikata laifuka da ke hamayya da shi.

A halin yanzu, Maikyala na hannun jami'an tsaro domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da shi a gaban kuliya.

Sojoji sun kai samame maboyar yan bindiga
Hafsan sojojin Najeriya, Laftanar janar Waidi Shuaibu. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: UGC

Sojoji sun kai samame maboyar 'yan bindiga

A wani bangare na sanarwar, rundunar ta ce dakarunta sun kara kaimi wajen gudanar da samamen kawar da 'yan ta'adda da lalata maboyarsu a jihar Zamfara.

A ranar 5 ga watan Nuwamba, sojojin sun kai farmaki kauyukan Aljummu Hausa, Aljummu Fulani da Tunga Magaji da ke karamar hukumar Maradun.

Kara karanta wannan

Marasa lafiya na shanye a asibiti, an kama likitoci na sheke ayarsu a kan gado

Kyaftin Tamuno ya ce samamen da ake ci gaba da gudanarwa ya taimaka wajen lalata maboyar 'yan ta'adda da takaita ayyukansu a yankin.

Sojojin Sama sun kai hari maboyar Dogo Gide

Haka kuma, rundunar sojin sama ta Najeriya ta kai hare-haren sama kan wasu wurare da ake zargin 'yan bindiga masu alaka da Dogo Gide suke amfani da su.

An kai hare-haren ne a Babban Doka da dajin Kuyumbana da ke karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara, cewar Punch.

Tamuno ya ce an gudanar da aikin ne bayan samun sahihan bayanan sirri da ke nuna cewa 'yan bindigar sun taru a yankin domin tsara hare-hare da sauran ayyukansu na ta'addanci.

Yan bindiga sun yi barna a Kaduna

A baya, an ji cewa wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne sun kai hari al’ummar Akwando da ke Kachia, inda suka kashe mutum biyu tare da sace wasu 20.

Ƙungiyar Kuturmi Unity Development Association ta bayyana sunayen mutanen da aka yi garkuwa da su, tare da nuna damuwa kan yawaitar hare-hare a yankunansu.

Ƙungiyar ta ce hare-haren da aka kai Ariko da Awon a baya sun yi sanadin mutuwar mutane da dama, ciki har da waɗanda suka mutu a hannun masu garkuwa da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.