Ministan Tinubu Ya Fadi Lokacin da Za a Kawo Karshen 'Yan Ta'adda a Jihohin Arewa

Ministan Tinubu Ya Fadi Lokacin da Za a Kawo Karshen 'Yan Ta'adda a Jihohin Arewa

  • Ƙaramin ministan tsaro Bello Muhammad Matawalle ya yabawa sojojin Najeriya kan nasarorin da suke samu a kan ƴan ta'adda
  • Matawalle ya bayyana cewa sojojin suna da ƙarfin da za su iya kawo ƙarshen ayyukan ƴan ta'sdda a ƙasar nan
  • Ministan ya yi nuni da cewa ƙarshen ƴan ta'adda ya zo inda ya ƙara da cewa nan bada jimawa ba za a samu zaman lafiya mai ɗorewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙaramin ministan tsaro, Dakta Bello Matawalle, ya bayyana cewa sojojin Najeriya suna da ƙarfin da za su iya kawo ƙarshen ƴan ta'adda.

Ya ce hakan a bayyane yake duba da irin nasarorin da suka samu cikin ƴan kwanakin nan na kawar da shugabannin ƴan ta'adda a yankin Arewa maso Yamma, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

DHQ: Dakarun sojoji sun halaka ƴan bindiga sama da 150, sun samu nasarori a Arewacin Najeriya

Matawalle ya yabi sojoji
Matawalle ya.yabawa sojojin Najeriya Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Ya kuma yabawa rundunar sojoji kan hare-haren da ta kai kan ƴan ta’adda a jihohin Zamfara, Sokoto, Katsina da Kaduna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na ma’aikatar tsaro, Henshaw Ogubike, ya fitar, ministan ya ce ƙarshen ƴan ta’addan ya zo, inda ya ƙara da cewa al’ummar ƙasar nan za su sake samun zaman lafiya mai ɗorewa.

Wane yabo Matawalle ya yi wa sojoji?

Ya kuma yabawa sojojin musamman kan hare-haren da suka kai kan ƴan ta’adda a ƙananan hukumomin Zurmi, Gusau, da Maradun wanda ya yi sanadiyyar sheƙe ƴan ta’adda da dama tare da lalata maɓoyarsu, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

A kalamansa:

"Tare da addu'a da goyon bayan sojojinmu, nan ba da jimawa ba za su kawo ƙarshen hare-haren ƴan bindiga a waɗannan jihohin."

Ya kuma bayyana cewa sojojin sun yi nasarar gano tare da lalata sansanonin fitattun ƴan ta’adda, Abdullahi Nasanda da Mallam Tukur.

Kara karanta wannan

Barka da Sallah: Ganduje ya bayyana abin da 'yan Najeriya ya kamata su yi wa Tinubu

Matawalle ya buƙaci sojoji su tashi tsaye

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙaramin ministan tsaron Najeriya, Bello Matawalle, ya buƙaci rundunar soji ta ƙara matsa ƙaimi a yaƙin da take da ƴan ta'adda da ƴan bindiga a Arewa maso Yamma.

Matawalle ya ce yawaitar hare-haren ƴan bindiga a jihohin musamman a Kaduna, Katsina da Zamfara ya ƙara nuna buƙatar ƙara girke jami'an soji a yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel