Goron Sallah: Gwamnan Bauchi Ya Faranta Ran Ma'aikatan Jihar

Goron Sallah: Gwamnan Bauchi Ya Faranta Ran Ma'aikatan Jihar

  • Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayar da umurnin a biya dukkanin ma'aikatan jihar N10,000 domin shagalin bukukuwan Sallah
  • A cewar wata sanarwa da aka fitar a madadin shugaban ma'aikatan jihar, umurnin biyan kuɗin ya shafi ma'aikata a matakin jiha da na ƙananan hukumomi
  • Shugaban ma'aikatan ya buƙace su da mayar da biki kan wannan karamcin da gwamnan ya yi musu ta hanyar mayar da hankali wajen gudanar da ayyukansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya bayar da umarnin biyan N10,000 ga dukkan ma'aikatan gwamnati a matakin jiha da ƙananan hukumomi a faɗin jihar.

Gwamnan ya bada kyautar kuɗin ga ma’aikatan ne domin ba su damar gudanar da bukukuwan Sallah cikin farin ciki, musamman a halin da ake ciki na taɓarɓarewar tattalin arziƙi, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya bi sahun Tinubu, ya kara ranakun hutun Sallah a jiharsa

Gwamna Bala ya ba ma'aikata goron Sallah
Gwamnan Bauchi ya ba ma'aikatan jihar kyautar N10 000 Hoto: @SenBalaMohammed
Asali: Twitter

Meyasa Gwamna Bala ya bada kyautar kuɗin?

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Mohammed Sani Umar ya fitar a madadin shugaban ma’aikatan jihar, rahoton jaridar Daily Post ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ƙara da cewa:

"Bada kyautar ga ma’aikata wani karamci ne na gwamna domin ba su damar gudanar da bukukuwan Sallah cikin nishaɗi sakamakon matsin tattalin arziƙi da ake ciki a yanzu."

Da yake yabawa gwamnan bisa wannan karamcin da tallafin da yake ba ma'aikata, shugaban ma’aikatan, ya buƙace su da mayar da biki.

Ya buƙaci ma'aikatan da su jajirce ta hanyar yin aiki tuƙuru da mayar da hankali wajen gudanar da ayyukansu domin ƙara ƙarfafa gwiwar gwamnati wajen ci gaba da samun nasarorin da take a yanzu.

Gwamnan Bauchi ya tallafawa maniyyata

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya tallafawa dukkan alhazan jiharsa biyo bayan ƙarin kuɗin kujerar zuwa sauke farali da hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta yi.

Gwamna Mohammed ya amince zai biya kaso 50% na ƙarin ga kowane mahajjaci na jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel