Za a Yi Kewa: Cristiano Ronaldo Ya Yi Ritaya daga Buga wa Portugal Wasa

Za a Yi Kewa: Cristiano Ronaldo Ya Yi Ritaya daga Buga wa Portugal Wasa

  • Cristiano Ronaldo ya sanar da yin ritaya daga buga wa tawagar ƙasar Portugal wasa a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram ranar Alhamis
  • Ɗan wasan mai shekaru 41 ya buga wa Portugal wasanni 234, inda ya zura ƙwallaye 146, abin da ya sa ya zama wanda ya fi kowa zura ƙwallaye da buga wasanni
  • Ronaldo wanda ke wasa yanzu a Al-Nassr ya jagoranci Portugal ta lashe gasar Euro 2016 da UEFA Nations League ta 2019

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Riyadh, Saudiyya - Fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa na ƙasar Portugal, Cristiano Ronaldo, ya sanar da yin ritaya daga buga wa tawagar ƙasarsa wasa.

Ronaldo ya bayyana matakin ne a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram ranar Alhamis, 5 ga watan Nuwamban 2026.

Kara karanta wannan

Yadda masu Opay za su iya karbar tallafin N50,000 duk wata na gwamnatin tarayya

Ronaldo ya yi ritaya
Cristiano Ronaldo na kuka bayan wasan Portugal na karshe a gasar cin kofin duniya ta 2026 Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sanarwar da Ronaldo ya fitar a shafin na sa na Instagram ta sa ya kawo ƙarshen shafe sama da shekaru 20 yana wakiltar Portugal a fagen ƙwallon ƙafa.

Ronaldo ya bayyana cewa lokaci ya yi da zai miƙa rigar tawagar Portugal mai lamba bakwai ga sabon ƙarni, bayan wata doguwar tafiya da ya ce ta sauya rayuwarsa

"Ranar da zan miƙa rigar tawagar ƙasarmu mai lamba bakwai ta zo. Ban taɓa jin cewa rigar tawa ce ni kaɗai ba, amma tsawon shekaru 23 na samu damar sanya ta, kare ta da kuma wakiltar ƙasata da ita a filayen wasa daban-daban a duniya.

“Yanzu lokaci ya yi da zan miƙa ta ga waɗanda za su zo nan gaba. Ba abu ne mai sauƙin yanke wannan shawara ba, domin wasu shawarwari ba tunani kaɗai ake amfani da shi wajen yankewa ba, har da zuciya.”

Ronaldo ya waiwayi tafiyarsa da Portugal

Kara karanta wannan

Maza gumbar dutse: Abin da Peter Obi ya yi da aka farmaki tawagar NDC a Calabar

Ronaldo, wanda ya fara buga wa babbar tawagar Portugal wasa a watan Agustan 2003, ya ce tafiyarsa da ƙasar ta zo ƙarshe.

Ya bayyana cewa idan ya waiwayi shekarun da ya yi yana wakiltar Portugal, ba wasanni, ƙwallaye, tarihi da kofuna kaɗai yake tunawa da su ba.

“Tafiyar da ta fara a watan Agustan 2003, wadda ta sauya rayuwata har abada, ta zo ƙarshe.

“Idan na waiwayi duk abubuwan da suka faru da tawagar ƙasa, ba wasanni, ƙwallaye, tarihin da na kafa ko kofunan da muka lashe kawai nake gani ba.

“Ina ganin mutane. Ina tunawa da ’yan Portugal da ke zaune a ƙasashen waje, waɗanda tsawon mintuna 90 suke jin kamar sun ɗan kusanci gida.

“Ina ganin miliyoyin ’yan Portugal da ban taɓa haɗuwa da su ba, amma suka zama wani ɓangare na rayuwata. Domin a ƙarshe, ƙwallon ƙafa ta fi wasa kawai. Ƙwallon ƙafa tana magana ne kan mutane.” In ji shi.

Ya sadaukar da komai wajen wakiltar ƙasarsa

Ronaldo, wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau biyar, ya ce a tsawon lokacin da ya yi a tawagar ƙasa, ya kasance yana ƙoƙarin zarce iyakokinsa domin samun nasara.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Manyan alkawuran Atiku ga 'yan Najeriya a wajen kamfen ADC a Sokoto

Ya ce burinsa shi ne lashe kofuna, inganta kansa da kuma kafa tarihi, inda ya tabbatar da cewa ya bayar da duk abin da yake da shi wajen wakiltar ƙasarsa.

Sai dai ya amince cewa akwai lokutan da ya yi kuskure, ya sha wahala, kuma bai samu nasarar bai wa ’yan Portugal abin da suke fata ba.

“Na yi kuskure. Na sha wahala. Akwai lokutan da na kasa bai wa ’yan Portugal abin da suke matuƙar fata.

“Amma ban taɓa yin kasa a gwiwa ba. Fiye da komai, ban taɓa daina alfahari da wakiltar Portugal ba.” In ji shi.

Ronaldo ya bar tarihi a ƙwallon ƙafa ta duniya

Bisa bayanan UEFA da aka sabunta a watan Oktoban 2026, Ronaldo ya bar tawagar Portugal a matsayin ɗan wasan da ya fi kowa zura ƙwallaye a tarihin wasannin ƙasa da ƙasa na maza.

Ya zura ƙwallaye 146 a wasanni 234, sannan shi ne ɗan wasan da ya fi kowa yawan bugawa ƙasarsa wasanni a tarihin ƙwallon ƙafa ta maza.

Haka kuma, ya karya tarihin Bader Al-Mutawa na Kuwait, inda ya zama ɗan wasan da ya fi kowa wakiltar ƙasarsa a wasannin ƙasa da ƙasa.

Kara karanta wannan

Atiku ya kaddamar da kamfen a Sokoto, ya yi muhimman alkawura ga 'yan Najeriya

A shekarar 2026, Ronaldo ya kuma zama ɗan wasan farko da ya zura ƙwallaye a gasar cin kofin duniya guda shida daban-daban.

Daga Euro 2004 zuwa lashe kofuna

Ronaldo ya fara bugawa Portugal wasa ne a ranar 20 ga Agustan 2003, a karawar da ƙasar ta yi da Kazakhstan.

Bayan shekara guda, ya wakilci Portugal a gasar cin kofin nahiyar Turai ta 2004, inda ƙasar ta kai wasan ƙarshe amma ta sha kashi a hannun Girka.

A shekarar 2016, ya jagoranci Portugal zuwa lashe kofinta na farko a babban gasar ƙasa da ƙasa, wato Euro 2016.

Duk da cewa ya ji rauni kuma aka cire shi daga wasan ƙarshe da Faransa, tawagar Portugal ta samu nasarar lashe kofin.

Daga baya, Portugal ta lashe gasar UEFA Nations League ta farko a shekarar 2019, sannan ta sake ɗaukar kofin a shekarar 2025.

Ronaldo ya yi ritayar buga wa Portugal wasa
Cristiano Ronaldo bayan wasan Portugal Hoto: Cristiano
Source: Instagram

Hukumar kwallon Portugal ta rasa mabiya

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar ƙwallon Portugal ya yi asarar mabiya Hukumar Kwallon Portugal (FPF) ta yi asarar sama da mabiya a shafukan sada zumunta biyo bayan abin da ya faru da Cristiano Ronaldo.

Hukumar FPF ta rasa sama da mabiya miliyan ɗaya a Instagram cikin sa’o’i 24 bayan Cristiano Ronaldo ya bar sansanin tawagar 'yan ƙasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng