A ƙarshe, Ronaldo Ya Faɗi Lokacin da Zai Yi Ritaya daga Bugawa Portugal Ƙwallo
- Cristiano Ronaldo ya tabbatar da cewa gasar cin kofin duniya ta FIFA 2026 ita ce ta karshe da zai bugawa Portugal
- Dan wasan mai shekara 41 ya ce zai yi ritaya ne a lokacin da ya ga dama, yana mai cewa ya nuna duk wata bajintarsa
- Ronaldo ya ce rashin lashe kofin duniya ba zai rage martabarsa ba, yayin da Portugal za ta kara da Spain a yau Litinin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Amurka - Fitaccen dan wasan Portugal, Cristiano Ronaldo, ya tabbatar da cewa gasar cin kofin duniya ta FIFA 2026 da ake yi a Amurka, Canada da Mexico ita ce ta karshe da zai wakilci kasarsa.
Dan wasan mai shekara 41 ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai gabanin wasan da Portugal za ta fafata da Spain a zagaye na 16 na gasar.

Source: Getty Images
Ronaldo ya kafa sabon tarihi a gasar
Ronaldo ya zama dan wasa na farko da ya taba buga gasar cin kofin duniya sau shida, sannan kuma shi ne mafi tsufa da ya kai matakin wasannin fitar da gwani, in ji rahoton Sky Sports.
Ya kuma zura kwallo ta bugun fenariti yayin da Portugal ta doke Croatia da ci 2-1 a zagaye na 32.
Ronaldo na daga cikin ƴan wasa shida da suka kafa tarihi mai girma a kakar gasar Kofin Duniya ta bana, ciki har da su Lionel Messi, Kyalian Mbappe da sauransu.
"Wannan ce gasar kofin duniya ta karshe a gare ni"
Ronaldo ya ce yana fatan kai Portugal zuwa matakai na gaba a gasar, amma ya tabbatar da cewa wannan shi ne karon karshe da zai buga gasar cin kofin duniya.
Ya ce:
"Ina so na ji dadin kowane lokaci na gasar. Wannan ce gasar cin kofin duniya ta karshe a gare ni, amma ina fatan wasan gobe ba zai zama na karshe ba."
Ya kara da cewa ranar ritayarsa za ta zo ne a lokacin da ya ga dama.
"Ko me ya faru, zan bar kwallon kafa cikin kwanciyar hankali saboda na bayar da komai. Ina buga kwallo ne saboda ina sonta."

Source: Getty Images
"Rashin lashe kofin duniya ba zai rage darajata ba"
Duk da cewa ya lashe kyautar Ballon d'Or sau biyar, gasar UEFA Champions League sau biyar da kuma Euro tare da Portugal, Ronaldo ya ce idan har bai lashe kofin duniya ba, hakan ba zai rage irin tarihin da ya kafa ba.
Ya ce shekaru sun ba shi kwarewa da natsuwa, yana mai gode wa masu sukarsa saboda sun taimaka masa ya kara karfi a rayuwa, cewar rahoton Aljazeera.
Yanzu haka Portugal za ta kara da Spain a wasan zagaye na 16 da za a buga a filin wasa na Dallas da ke jihar Texas a ranar Litinin, 6 ga Yuli, inda Ronaldo zai yi kokarin taimakawa kasarsa ta kai wasan daf da na kusa da na karshe.
Ronaldo ya furta 'BisimilLah' kafin buga ƙwallo
A wani labarin, mun ruwaito cewa, bidiyo ya bazu a intanet bayan an ga Cristiano Ronaldo yana furta "Bismillah" kafin ya zura kwallo a bugun fenariti.
Masu sharhi a kafafen sada zumunta sun yi ikirarin cewa Ronaldo ya maimaita kalmar sau biyu kafin ya buga ƙwallon da ya zura a ragar Croatia.
Tun bayan komawarsa ƙungiyar Al Nassr ta Saudiyya a 2023, Ronaldo ya saba amfani da kalmomin Larabci kamar "Assalamu alaikum" da sauransu.
Asali: Legit.ng


