Yadda Masu Opay Za Su Iya Karbar Tallafin N50,000 duk Wata na Gwamnatin Tarayya
- Gwamnatin Tarayya ta fara biyan tallafin Naira 50,000 na wata-wata ƙarƙashin shirin NERSI, wanda aka ƙaddamar a ranar 30 ga Oktoba, 2026
- Masu amfani da OPay za su iya duba ko an zaɓe su ta hanyar lambar USSD 95520# ko kuma manhajar OPay
- Gwamnati ta ce ba a karɓar kuɗi domin rajista ko karɓar tallafin, tare da gargaɗin mutane kan masu damfara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta fara biyan tallafin kuɗi na Naira 50,000 duk wata ga wasu ’yan Najeriya masu ƙaramin ƙarfi, ƙarƙashin shirin agajin gaggawa da daidaita tattalin arziki na ƙasa, wato National Emergency Relief and Stabilisation Intervention (NERSI).
An ƙaddamar da shirin ne a ranar 30 ga Oktoba, 2026, domin tallafa wa talakawa da gidaje masu rauni waɗanda ke fama da tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki.

Kara karanta wannan
Shin tallafin N50,000 da aka fara turawa 'yan Najeriya bashi ne ko kyauta? An samu bayani

Source: Twitter
Leadership ta ce Ministan Harkokin Jin Ƙai da Rage Talauci, Dakta Bernard Doro, ya bayyana cewa za a rika tura kuɗin kai tsaye ga waɗanda suka cancanta ta hannun kamfanonin samar da hidimomin kuɗi na zamani da gwamnati ta amince da su.
OPay na ɗaya daga cikin kamfanonin da aka amince da su wajen biyan kuɗin. Kamfanin ya kuma bayyana hanyoyin da waɗanda aka zaɓa za su bi domin duba cancantarsu da amincewa da karɓar tallafin.
Ga yadda masu amfani da OPay za su duba ko an zaɓe su da kuma karɓar tallafin Naira 50,000.
Yadda za a duba cancanta ta hanyar OPay
1. Latsa lambar USSD: Buɗe wajen kiran waya, sannan ka latsa 95520# ta amfani da lambar wayar da aka haɗa da asusunka na OPay.
2. Bi umarnin da aka bayar: Zaɓi amsar da ta dace daga cikin zaɓuɓɓukan da suka bayyana, sannan ka bi umarnin domin duba ko ka cancanci tallafin da kuma amincewa da karɓarsa.
3. Yi amfani da manhajar OPay: Haka kuma, za ka iya shiga manhajar OPay, sannan ka duba shafin farko domin ganin sanarwar da ke nuna cewa an zaɓe ka cikin waɗanda za su amfana.
4. Amince da karɓar tallafin: Idan an zaɓe ka, bi umarnin da aka nuna domin bayar da amincewarka da kammala aikin.
5. Karɓi kuɗinka: Bayan kammala duk matakan da ake buƙata, za a tura maka tallafin Naira 50,000 zuwa walat ɗin wayarka da aka ware domin karɓar kuɗin.
Waɗanne mutane ne suka cancanci tallafin N50,000?
Bisa ƙa’idojin shirin NERSI na Gwamnatin Tarayya, ana zaɓar waɗanda za su amfana ne daga sahihan bayanan rajistar shaidar zama ɗan ƙasa da kuma kundin bayanan iyalai masu ƙaramin ƙarfi na ƙasa, wato National Social Register.
Shirin ya shafi talakawa da gidaje masu rauni a faɗin Najeriya, musamman waɗanda ke cikin yankuna shida na ƙasar.
Sai dai gwamnati ta bayyana cewa mutum ba zai iya neman a saka shi cikin jerin waɗanda za su amfana da kansa ba, haka kuma ba a buƙatar ya biya kuɗi domin samun gurbi.
Ana zaɓar waɗanda suka cancanta ne bisa sahihan bayanai da matakan tantancewa da hukumomin da abin ya shafa ke gudanarwa.

Source: Twitter
Shin wakili zai iya karbar tallafin N50,000
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta fayyace cewa babu wanda zai iya karɓar tallafin Naira 50,000 na wata-wata a madadin wani mutum.
Gwamnatin tarayyar ta yi bayanin cewa ana tura kuɗin ne ta hanyar lambar wayar wanda aka yi wa rajista.
Asali: Legit.ng

