Uba Sani Ya Cika Alkawarin Shekaru 30 da Aka Yi wa ‘Yan Kwallon Najeriya

Uba Sani Ya Cika Alkawarin Shekaru 30 da Aka Yi wa ‘Yan Kwallon Najeriya

  • Uba Sani ya raba wa zakarun Atlanta '96 filayen tare da rada sunayensu a wasu tituna domin karrama su
  • Taurarin sun ji dadin ganin ana sake gina filin wasa na Ahmadu Bello Stadium don mai da shi na zamani
  • Tsofaffin 'yan wasan sun nuna godiya sosai ga gwamnan saboda cika alkawarin da aka yi shekaru 30 ana jira

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kaduna - Tsohon ‘dan wasan Super Eagles, Daniel Amokachi, ya yaba wa gwamna Uba Sani saboda ya cika masu dadadden alkawari.

Gwamnan jihar Kaduna ya cika alkawarin da aka yi wa ‘yan kwallon kafa da suka ci wa Najeriya zinari a gasar Oylmpics a 1996.

Uba Sani
Gwamna Uba Sani tare da tsofaffin 'yan wasan Super Eagles a Kaduna Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

Atlanta 96: Gwamna Uba Sani ya cika alkawari

Gidan talabijin na TVC ya rahoto Daniel Amokachi yana farin ciki da filayen da Gwamna Uba Sani ya ba tsofaffin ‘yan wasan.

Kara karanta wannan

An samu ɓaraka, Ministan Tinubu ya fara takun saƙa da gwamnonin APC 2 a Najeriya

Amokachi, Garba Lawal da Emmanuel Babayaro sun samu fuloti a sakamakon nasarar da suka samu a Atlanta a shekarun baya.

Baya ga kyautan filaye, Mai girma gwamnan ya rada wa wasu hanyoyi sunayen tsofaffin ‘yan kwallon da suka zama zakaru a 1996.

Amokachi ya ce wannan abin da Uba Sani ya yi, ya dawo da amannarsu da gwamnati.

Gwamnati Uba tana gyaran filin wasan ABG

Tsohon tauraron na Super Eagles ya yi wannan bayani ne lokacin da yake duba aikin da ake yi na gyaran filin wasa na Ahmadu Bello.

Mista Amokachi ya tuna da yadda aka yi masu alkawari tun tuni, amma duk gwamnatocin da aka yi a kasar ba su iya sauke nauyin ba.

Sai yanzu ne gwamnatn Uba Sani ta cika wannan alkawari, ta ba ‘yan wasan uku filaye, kuma ta tuna da sauran wadanda suka cika.

Daniel Amokachi ya ce:

"Ba mu san kalmomin da za su ma fada mu gode masa ba da irin wannan abin alheri da kuma kokarinsa na ganin tsofaffin ‘yan wasa da masu horarwa sun samu lada lokacin da suke raye."

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali da 'yan bindiga suka hallaka shugaban APC a Kano

Uba Sani ya sha yabo daga tsofaffin 'yan kwaallo

Punch ta ke cewa Amokaci wanda yanzu mai horar da ‘yan kwallo ne ya ce Gwamna Uba Sani ya yi abin da ya cancanci a jinjina masa.

Shi ma Babayaro ya yaba wa gwamnatin Uba Sani ganin yadda take da sha’awar harkar wasanni da ya gyaran da ake yi a filin ABS.

Garba Lawal wanda ya buga wa Super Eagles kuma ya shugabanci kungiyar Kaduna United ya ji dadin yadda ake gyara filin wasan.

Idan aka kama gyaran filin kwallon na Kaduna, Garba Lawal ya ce zai kai matsayin sauran filayen wasan da ake da su a kasashen waje.

Hakan zai ba Super Eagles damar zuwa yin wasa a Kaduna maimakon su je Uyo a jihar Akwa Ibo.

Hotunan Uba Sani wajen gyaran filin wasan ABS

Shugaban hukumar kula da kwallon kafa ya ajiye aiki

An ji labarin yadda Majalisar Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya (NFF) ta kira taron gaggawa domin tattauna halin da shugabancin hukumar ke ciki.

Kara karanta wannan

An samu matsala: 'Dan El Rufai ya soi dan uwansa Bello game da Gwamna Uba Sani

Taron ya mayar da hankali ne kan binciken gudanar da ayyukan kwamitin zartarwa da sakatariyar NFF sakamakon jita-jitar murabus din shugabanni.

Halartar taron wajibi ne ga dukkan mambobin majalisar da wakilan kungiyoyi domin tunkarar kalubalen da ke gaban hukumar a harkar kwallon kafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng