An Kira Taron Gaggawa bayan Rade Radin Shugabannin NFF Sun Yi Murabus

An Kira Taron Gaggawa bayan Rade Radin Shugabannin NFF Sun Yi Murabus

  • Majalisar Ƙungiyar Kwallon Ƙafa ta Najeriya ta kira taron gaggawa a Abuja domin tattauna halin da harkokin ƙwallon ƙafar ƙasar ke ciki
  • Za a duba yadda kwamitin zartarwa da sakatariyar NFF ke gudanar da ayyukansu da kuma tasirin abubuwan da suka faru a baya-bayan nan
  • An umarci dukkannin mambobin majalisar su halarta, inda aka ce kasancewarsu wajibi ne domin tunkarar kalubalen da ke tafe a nan gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Mambobin Hukumar Ƙungiyar Kwallon Ƙafa ta Najeriya (NFF) za su gudanar da taron gaggawa a Abuja, yayin da ake ƙara samun damuwa kan wasu abubuwan da ke faruwa a cikin hukumar

An bayyana hakan ne cikin wata takardar gayyata da Yakubu Sarma ya sanya wa hannu, wadda aka aika wa dukkan mambobin Majalisar NFF.

Kara karanta wannan

EFCC ta yi tayin lada ga masu kwarmato game da dukiyoyin Najeriya da aka wawure

NFF ta kira taron gaggawa
Shugaban NFF mai murabus, Ibrahim Gusau Hoto: Adekunle Ajayi
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa taron, wanda aka shirya gudanarwa da ƙarfe 12 na rana a Abuja a ranar Alhamis, zai mayar da hankali kan yadda ake tafiyar da ayyukan kwamitin zartarwa na NFF da kuma sakatariyar hukumar.

NFF ta kira taron gaggawa

A ruwayar Vanguard, a cikin ajandar taron, an tanadi tattaunawa kan abubuwan da ke faruwa a halin yanzu a NFF, da kuma matsayin kwamitin zartarwa da sakatariyar hukumar da yadda suke gudanar da ayyukansu.

Haka kuma, majalisar za ta duba yadda abubuwan da suka faru a baya-bayan nan za su iya shafar shugabanci, kwanciyar hankali da kuma ‘yancin cin gashin kan hukumar kwallon ƙafa.

Ana kuma sa ran mambobin za su tattauna matakan da suka dace da za a ɗauka bisa tanade-tanaden dokokin NFF, Hukumar Kwallon Ƙafa ta Afirka (CAF) da kuma FIFA, kafin su yanke shawarar matakin da za a ɗauka nan gaba.

Kara karanta wannan

2027: Matan da suka fito neman kujerar Tinubu a zaben Najeriya

Su wa aka gayyata taron NFF?

Daga cikin waɗanda aka gayyata zuwa taron akwai shugabannin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na jihohi, wakilan kungiyoyin ƙwallon ƙafa, mambobin Ƙungiyar Alƙalan Kwallo, Ƙungiyar Masu Horaswa, Ƙungiyar ‘Yan Wasa da kuma Ƙungiyar Alƙalan Kwallon Ƙafa ta Najeriya (NRA).

NFF ta gayyaci kungiyoyi domin halartar taron gaggawa a Abuja
Alamar hukumar wasanni ta NFF Hoto: Getty
Source: Getty Images

Taron na gaggawa ya zo ne a daidai lokacin da ake ƙara mayar da hankali kan yadda ake tafiyar da harkokin ƙwallon ƙafa a Najeriya, musamman kan shugabanci da gudanar da ayyukan NFF.

Ana sa ran Majalisar za ta tattauna batutuwan da suka janyo damuwar tare da duba matakin da ya dace a ɗauka domin magance su da kuma tabbatar da daidaito a tafiyar da hukumar.

Malami ya yi magana kan Ronaldo

A wani labarin kuma Shugaban majalisar malaman Kano kuma dan siyasa, Sheikh Ibrahim Khalil ya yi bayani game da shan kayen Cristiano Ronaldo a kofin duniya.

A sharhin da ya yi, malamin ya bayyana wasu abubuwa da ya ce su ne suka hana Ronaldo yin abin kirki a gasar duk da shi kwararre ne a harkar kwallon kafa.

Ya yi magana ne a cikin jerin shirye-shiryen da ya ke gabatarwa karkashin shirin Mahangar Malam, yayin da ya ke bayani kan amfanin hadin kai wajen cimma manufa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng