Buhari ya nada tsohon gwarzon dan kwallon kafa, Daniel Amokachi, a matsayin jakada

Buhari ya nada tsohon gwarzon dan kwallon kafa, Daniel Amokachi, a matsayin jakada

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da nada tsohon gwarzon dan wasa kuma mataimakin kociyan kungiyar kwallon kafa ta kasa, 'Super Eagles', Daniel Amokachi, a matsayin jakadan kwallon kafa na Najeriya.

Amokachi ya taka muhimmiyar rawa a kungiyar 'Super Eagles' a lokacin da ta samu nasarar lashe gasar cin kofin kasashen nahiyar Afrika a shekarar 1994 da 1996, shekarar da Najeriya ta samu nasarar lashe zinare a gasar 'Atlanta Olympics'.

Tsohon gwarzon dan wasan ya taka leda a kungiyar kwallon kafa ta 'Everton' da ke kasar Ingila, inda ya kai ga samun nasarar lashe kofin FA tare da kuniyar a shekarar 1995. Bayan ya yi ritaya, Amokachi ya zama mai horar wa a kungiyar kwallon kafa ta jihar Nasarawa kafin daga bisani ya rike kungiyar kwallon kafa ta Enyimba da ke garin Aba.

Buhari ya nada tsohon gwarzon dan kwallon kafa, Daniel Amokachi, a matsayin jakada
Daniel Amokachi
Asali: Getty Images

A matsayinsa na jakadan kwallon kafa na Najeriya, duk da mukami ne na girmamawa kawai, Amokachi zai bawa gwamnatin tarayya gudunmawa a ma'aikatar matasa da wasanni musamman a bangaren zakulo masu hazaka da baiwar iya taka leda, inganta harkokin kungiyar kwallon kafa ta kasa da kuma bayar da shawarwari ga matasa, maza da mata, a kan harkokin motsa jiki.

DUBA WANNAN: Abinda Buhari ya fada wa Lawan da Gbajabiamila a kan tsaro yayin ganawarsu

An haifi Amokachi a ranar 30 ga watan Disamba na shekarar 1972 a garin Kaduna. Mahaifinsa, Ikwulechin Amokachi, dan asalin garin Otukpa ne ta karamar hukumar Ogbadibo a jihar Benuwe.

Amokachi ya taka leda a kungiyar 'Super Eagles' tare da fitattun 'yan wasan kwallon kafa da suka hada da; Jay Jay Okocha, Sunday Oluseh, Samson Sia Sia da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel