Ana Shirin Zaben 2027, Gwamna Inuwa Ya Nada Muhimman Mukamai a Gwamnati
- Gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya, ya amince da naɗin mutum uku a matsayin kwamishinoni, tare da tura sunayensu Majalisar Dokokin jihar domin tantancewa
- Gwamnan ya kuma naɗa masu ba shi shawara na musamman biyu da manyan mataimaka huɗu kan harkokin siyasa da hulɗa da al’umma.
- Sababbin naɗe-naɗen sun fara aiki nan take, sai dai naɗin kwamishinonin na jiran amincewar Majalisar Dokokin jihar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Gombe - Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya amince da naɗin mutum uku a matsayin kwamishinoni, da masu ba shi shawara biyu da manyan mataimaka huɗu.
Gwamnatin jihar ta ce naɗe-naɗen wani ɓangare ne na ƙoƙarin ƙarfafa tsarin tafiyar da mulki da inganta ayyukan gwamnati.

Source: Facebook
An tura sunayen kwamishinoni ga Majalisa
Sakataren Gwamnatin Jihar Gombe, Farfesa Ibrahim Njodi, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, 22 ga watan Satumban 2026, cewar rahoton jaridar The Punch.
Njodi ya ce Gwamna Yahaya ya tura sunayen mutum uku da aka zaɓa domin zama kwamishinoni zuwa Majalisar Dokokin Jihar Gombe domin tantancewa da amincewa da su.
Sunayen waɗanda aka zaɓa sun haɗa da Dakta Ahmed Wali Doho, Nasiru Adamu Degri da Dakta Muhammad A. Bello.
An naɗa masu ba da shawara biyu
Sakataren gwamnatin ya kuma ce gwamnan ya amince da naɗin Abdulmalik Jibrin da Mohammed Nuhu a matsayin masu ba shi shawara na musamman.
Haka kuma, an naɗa Jibrin M. Ali, Sadiq Abubakar, wanda aka fi sani da BB Kumo, John Launa da Danlami Sanda a matsayin Manyan Mataimakan Musamman na II kan harkokin siyasa da hulɗa da al’umma.
Naɗe-naɗen sun fara aiki nan take
Sanarwar ta ce naɗe-naɗen sun fara aiki nan take, sai dai naɗin kwamishinonin da aka tura wa Majalisar Dokokin jihar ya kasance ƙarƙashin amincewar majalisar.
Gwamnatin jihar ta ce manufar naɗe-naɗen ita ce ƙarfafa haɗin gwiwa da gudanar da ayyukan gwamnati yadda ya kamata, tare da taimakawa wajen aiwatar da ajandar ci gaban gwamnatin Yahaya.
Inuwa Yahaya ya fara zama Gwamnan Gombe ne a shekarar 2019, sannan ya sake lashe zaɓen gwamna na 2023 domin ci gaba da wa’adinsa na biyu.
Gwamnatinsa na gudanar da ayyukanta ta Majalisar Zartarwa ta jihar da kuma wasu ofisoshin siyasa da na gudanarwa waɗanda ke da alhakin aiwatar da manufofi da shirye-shiryen gwamnati.

Source: Original
PDP ta kara karfi a Gombe
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP a Jihar Gombe ta samu karin karfi bayan Hon. Usman Sule Dauda, wanda aka fi sani da Kalala, ya yi murabus daga shugabancin Labour Party (LP) na jihar.
Hon Usman Sule Dauda da ake yi wa lakabi da Kalala ya koma PDP tare da Hon. Shehu Abubakar Durbi da dimbin magoya bayansu, lamarin da jam’iyyar ta bayyana a matsayin babban ci gaba na siyasa.
Asali: Legit.ng

