An Samu Matsala: Dan El Rufai Ya Soki Dan Uwansa Bello game da Gwamna Uba Sani
- Dan tsohon gwamnan Kaduna Bashir El-Rufai, ya caccaki ɗan’uwansa Bello kan sauya sheka tsayawa tare da gwamnati
- Bashir ya zargi Bello da kasancewa tare da Gwamna Uba Sani har sai da ya fahimci ana watsar da shi, sannan ya tuna da iyali
- Bello ya bar APC a ranar 7 ga Mayu 2026, ya koma ADC tare da mahaifinsa, yayin da Bashir ya yi masa wasu zarge-zarge a shafinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Bashir el-Rufai, ɗan tsohon gwamnan Kaduna Nasir el-Rufai, ya yi wa ɗan’uwansa Bello kakkausan suka a safiyar Asabar.
Hakan ya biyo bayan zargin da Bsshir ya yi na cewa Bello ya tuna da iyalansa ne bayan ya fahimci za a watsar da shi a gwamnatin Uba Sani.

Source: Facebook
Bashir ya wallafa jerin saƙonni a shafinsa na X wanda a yanzu aka goge inda ya caccaki Bello kan wasu matakan siyasa da ya ɗauka kwanan nan, cewar TheCable.
Ya zargi Bello da watsi da iyalinsu, bayan ya kasance yana goyon bayan Uba Sani, wanda ya gaji mahaifinsu a matsayin gwamnan Kaduna.
Uba Sani, gwamnan Kaduna mai ci, ya kasance tsohon aminin el-Rufai, amma dangantakarsu ta lalace bayan Sani ya lashe zaɓen gwamna na 2023.
Bayan el-Rufai ya fice daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a watan Maris 2025, Bello, wanda ke wakiltar mazabar Kaduna ta Arewa a Majalisar Wakilai, ya ci gaba da kasancewa cikin jam’iyyar.
Sai dai a ranar 7 ga Mayu 2026, Bello ya fice daga APC, inda ya koma African Democratic Congress (ADC) tare da mahaifinsa.
Da yake magana a ranar Asabar, Bashir ya yi zargin cewa ɗan’uwansa ya ci gaba da kasancewa mai biyayya ga Sani har sai da ya fahimci cewa ana watsar da shi.
Bashir ya ce bayan haka ne Bello ya fara magana kan biyayyar iyali da komawa ADC.
Bashir ya rubuta cewa:
"Ya kasance da Uba Sani har sai da ya fahimci an yi watsi da shi, nan take ya tuna da iyalinsa kuma ya sauya sheka zuwa ADC, da din a ina yake? kawai yana biyewa son ransa ne."
Bashir ya kuma zargi ɗan’uwansa da kasancewa cikin yanayi na rashin nuna matsaya, yayin da wasu ke sukar gwamnan Kaduna.
Ya kuma yi zargin cewa Bello ya taɓa roƙonsa da ya rage tsananin sukar da yake yi wa tsohon shugabansa, wanda ake ganin yana nufin Uba Sani.
Bashir ya ƙara yin wasu zarge-zarge kan Bello a cikin saƙonninsa wasu daga cikinsu kuma daga baya aka goge su.
Wasu daga cikin zarge-zargen sun shafi batutuwan haihuwa da kuma zargin amfani da ƙwayoyi, waɗanda ba a tabbatar da su ba.
Dan El-Rufai ya magantu kan ziyartar mahaifinsa
An ji cewa dan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce duk lokacin da ya ziyarci mahaifinsa a tsare yana mamakin irin ƙarfin zuciya da jajircewar da yake nunawa.
Ya ce El-Rufai ya tabbatar masa cewa har yanzu yana ganin sadaukarwar da ya yi ta dace, inda ya amsa da cewa “eh” ba tare da wani jinkiri ba.
Kalamansa sun jawo martani daga masu amfani da kafafen sada zumunta, yayin da wasu ke addu'ar samun 'yancin El-Rufai a nan gaba kadan.
Asali: Legit.ng

