Super Eagles: Dalilan da su ka sa ba a jin labarin ‘Yan Arewa

Super Eagles: Dalilan da su ka sa ba a jin labarin ‘Yan Arewa

A makon jiya ne Jaridar Daily Trust tayi magana a kana bin da ya sa ake fama karancin ‘Yan wasan kwallon kafa da daga yankin Arewacin Najeriya a cikin Kungiyar kwallon kasa na Super Eagles.

A halin yanzu, wannan matsala da ake fama da ita, tana kara cabewa ne, a madadin abubuwa su gyaru. Tun daga 1963 har zuwa yau, ‘Yan wasan da su ka fito daga cikin kwaryar Arewa, 7 ne kurum su ka taba zuwa Gasar AFCON a tarihi.

Jaridar ta kasar nan ta kawo sunayen wadannan ‘yan wasa kamar haka. Annas Ahmed, Shafiu Mohammed, Ibrahim Mohammed, Ali Baba, Abdul Aminu. Sauran ‘yan wasan su ne; Garba Lawal, Tijjani Babangida da Sani Kaita.

KU KARANTA: Ronaldo zai sake cin kofin Zakarun Turai da Kungiyar Juventus

Manyan ‘yan wasan Arewa da aka yi, irin su Yaro Yaro, da Dahiru Sidi, ba su taba samun damar bugawa Super Eagles a Gasar AFCON na Nahiyar Afrika ba, duk da cewa sun taba takawa kasar ta su leda a wasu wasannin da-dama.

Yanzu haka dai Ahmed Musa da Shehu Abdullahi ne kurum ‘Yan Arewa da su ke cikin Tawagar Super Eagles a Gasar AFCON da za a buga a bana. Shi ma dai Ahmed Musa yana da alaka da Kudancin kasar ta bangaren Mahaifiya.

Shehu Abdullahi wanda yake taka leda a kasar Turkiyya shi ne kurum cikakken Bahaushen da za a gani a gasar 2019. Masana sun ce daga cikin dalilan da ya sa ba a jin duriyar Hausawa a akwai maganar addini da kuma al’ada.

KU KARANTA: Barcelona ba sa'ar Manchester United bace - Deolofeu

Ana kuma fama da karancin wakilan kungiyoyin kwallon kafa da za su shigo cikin Arewa domin zakulo hazikan ‘yan wasa, haka zalika, yawancin masu horas da ‘yan kwallon ba su dama da shigowa cikin Yankin Arewacin kasar ba.

A wani bangaren kuma, akwai laifin ‘yan wasan inda Mutanen Arewa kan nuna halin ko-in-kula yayin da ake kokarin nuna masu gata. Wani abu kuma shi ne rashin iya kashe kudi wajen ganin hakar ‘dan wasa ta cin ma ruwa a Arewa.

Wani wanda yake harkar kwallon yake cewa daga cikin matsalolin da ake fuskanta da su a Yankin Arewa shi ne, Bahaushen mutum bai son ganin yayi nesa da gida. Ya zama dole dai mutanen Arewa su dage su rika fito da kan su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Online view pixel