Daga Aron Mota, Ɗan Wasan Najeriya Osimhen Ya Shiga Babbar Matsala a Kasar Waje

Daga Aron Mota, Ɗan Wasan Najeriya Osimhen Ya Shiga Babbar Matsala a Kasar Waje

  • Kamfanin kera motoci na duniya, Mercedes-Benz, ya shigar da ƙara gaban 'yan sandan Italiya kan ɗan wasan Najeriya, Victor Osimhen
  • Ana zargin ɗan wasan mai shekaru 27 da gazawa wajen biyan sauran kuɗaɗen motar da ya yi hayarta tun a 2023, inda bashin ya kai €90,000
  • Rahotanni sun nuna cewa Osimhen bai kammala biyan kuɗin motar ba, sannan kuma bai mayar da ita ga kamfanin Marsandi ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Italiya – Fitaccen ɗan wasan Super Eagles kuma gwarzon ɗan wasan Galatasaray, Victor Osimhen, ya tsinci kansa a cikin wata takaddama ta shari'a.

Rahoto ya nuna cewa babban kamfanin kera motoci na alfarma, Mercedes-Benz ne ya kai ƙarar Victor Osimhen a wurin ƴan sandan kasar Italiya.

Kamfanin Marsandi ya yi karar Victor Osimhen kan bashin kudin hayar mota
Victor Osimhen, fitaccen dan wasan Najeriya da ke taka leda a Galatasaray. Hoto: @victorosimhen9
Source: Twitter

Marsandi ta yi karar Victor Osimhen

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban ƴan sanda ya ƙi yarda da sulhu, ya sayi fom ɗin takarar gwamna

Kamfanin ya yi zargin cewa ɗan wasan ya saɓa wa yarjejeniyar biyan kuɗin wata mota da ya ɗauka a ƙarƙashin tsarin haya tun yana taka leda a ƙungiyar Napoli, in ji rahoton Leadership.

Osimhen bai kammala biyan kuɗin sayen motar baki ɗaya ba, kuma bai mayar da ita ga kamfanin Mercedes-Benz ba, bashin da ya kai €90,000, kwatankwacin Naira miliyan 142, a cewar rahotanni.

Wannan bashi na Yuro 90,000 ya jefa jama'a cikin mamaki, duba da cewa ɗan wasan yana karɓar albashin da ya ninka wannan adadin a duk mako.

Victor Osimhen, wanda ya jagoranci Napoli wajen lashe kofin Serie A bayan kusan shekaru 40, yana ɗaya daga cikin ƴan wasan da suka fi samun kuɗi a tarihin ƙwallon ƙafa na ƙasar Turkiyya.

Albashinsa na shekara a Galatasaray ya haura Yuro miliyan 20, wanda hakan ya sa mutane da dama tambayar yadda aka yi ya kasa biyan ƙaramin sashi na wannan kuɗin.

'Yan Najeriya sun yi martani kan Osimhen

Dangane da wannan dambarwa, wasu masu amfani da yanar gizo sun bayyana ra'ayoyinsu kamar yadda jaridar Punch ta tattaro:

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun nuna tsaurin ido, sun yi gaba da gaba da sojoji, an rasa rayuka

"Mai yiwu wa rashin fahimta ne kawai. Ya kamata su sasanta a tsakaninsu a sirrance, maimakon fito da maganar fili." — @zinux17.

Wasu kuma sun nuna rashin amincewa da sahihancin rahoton:

"Ba zan yarda da wannan ba, a yi haƙuri. Ba shi da ma'ana; akwai wani abu da bai fito fili a gare mu ba." — @nuelpraise213.
"Osimhen ya gagara biyan kudin hayar mota? Wannan ba gaskiya ba ne." — @mondaycaroline.
"Akwai shakku a wannan lamari. Osimhen ba zai yi wani abu da zai bata sunansa ba gaskiya." — @get2lanre.
Kamfanin Marsandi ya yi karar Osimhen kan gaza biyan bashi
Dan wasan Najeriya Victor Osimhen (hagu) da mota kirar kamfanin Marsandi (dama). Hoto: @MercedesBenz, @victorosimhen9
Source: Twitter

Daga kungiyar Napoli zuwa Galatasaray

Osimhen ya yi fice a duniya bayan da ya taka leda a ƙasashe daban-daban tun daga Belgium, Faransa, Italiya, kuma yanzu haka yana Turkiyya.

Ana kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƴan wasan gaba a duniya, kuma wannan takaddama ta zo a daidai lokacin da yake jin daɗin rayuwa a birnin Istanbul.

A halin yanzu, jami'an Carabinieri na ci gaba da nazari kan ƙarar da aka shigar. Duniyar ƙwallon ƙafa tana zuba ido don ganin yadda wannan dambarwa za ta ƙare.

Kara karanta wannan

Tinubu ya samu kishiya, jigon APC zai fafata da shi a zaben fitar da gwani

Sharuddan Messi na taka leda da Osimhen

A wani labari, mun ruwaito cewa, Lionel Messi na shirin komawa kungiyar Galatasaray ta Turkiyya domin buga wasa tare da dan wasan gaba na Najeriya Victor Osimhen.

Tsohon ɗan wasan na Barcelona ya gindaya sharadin cewa zai buga wasanni 12 ne kawai a birnin Istanbul ba tare da buga wasan waje ba.

A lokacin an ji cewa Galatasaray tana tattaunawa da wakilan Messi don ganin ya dawo Turkiyya yayin da aka tunkari gasar cin kofin duniya ta shekarar 2026.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com