'Yan wasan kwallon kafa da su ka fi tsada a tarihi
- Mun kuma kawo jerin 'Yan wasan da su ka fi tsada a Duniya
- Daga ciki akwai sabon Dan wasan Kungiyar Barcelona Dembele
- Dan wasa Neymar Jr. ya fi kowa tsada a Duniyar kwallon kafa
A yau ma mun kuma kawo jerin 'Yan wasa 5 da su ka fi tsada a tarihin Duniya.
1. Neymar Jr.
Tsohon Dan wasan Barcelona Neymar Jr. ya fi kowa tsada a Duniyar kwallon kafa bayan ya bar kulob din zuwa Kungiyar PSG ta Kasar Faransa kan kudi Miliyan €222.
2. O. Dembele
Sabon Dan wasan Barcelona Ousman Dembele ne na 2 a jerin 'Yan wasa mafi tsada a Tarihi bayan Dortmund ta saida shi a kan kudi kusan Miliyan €145.
KU KARANTA: Arsenal ta sha mugun kashi wajen Liverpool
3. Pogba
Dan wasa Paul Pogba ne dan kwallo na 3 mafi tsada a Tarihi. Manchester United ta saye Pogba daga Juventus kan kudi Miliyan €100.
4. Bale
Dan wasan Real Madrid Gareth Bale ne na 4 a jerin ‘Yan wasan da su ka fi tsada a Duniya. Real ta saye Bale daga Tottenham kan kudi Miliyan €100.
5. Ronaldo
Cristiano Ronaldo ya dade a matsayin wanda ya fi kowa tsada a Duniya. Real Madrid ta saye Dan wasan kan kudi Miliyan €94 daga Manchester United a shekarar 2009.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Beraye sun hana Shugaba Buhari sakat
Asali: Legit.ng