Jerin 'Yan Wasan Afirka 10 da Suka Fi Haskakawa a Gasar Kofin Duniya na 2026

Jerin 'Yan Wasan Afirka 10 da Suka Fi Haskakawa a Gasar Kofin Duniya na 2026

Afrika - Wakilan Afirka guda goma da suka halarci gasar Kofin Duniya ta FIFA ta 2026 sun nuna kwarewa ta musamman, inda ‘yan wasa daga sassaban nahiyar suka bar tarihi a gasar kwallon kafa mafi girma a duniya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.

Daga kwarewar masu tsaron raga zuwa hazakar ‘yan wasan gaba da kuma taka rawar gani a tsakiya, ‘yan wasan Afirka sun bayar da gudunmawa mai tunawa a duk tsawon gasar.

An samu 'yan wasan Afrika da suka taka rawar gani a gasar Kofin Duniya ta 2026
Hagu zuwa dama: Ismaila Sarr (Senegal), Kofin Duniya 2026, Yoane Wissa (DR Kongo). Hoto: Michael Reaves, FIFA via Getty Images
Source: Getty Images

'Yan wasan Afrika 10 a Kofin Duniya

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA da wasu masana sun fitar da sunayen fitattun ‘yan wasa a ranar Alhamis wadanda suka taimaka wajen nuna karfin da nahiyar ke da shi a fagen kwallon kafa na duniya, in ji rahoton The Nation.

Dan wasan gaba na Senegal, Ismaila Sarr, shi ne ya zama gwarzon masu cin kwallaye daga Afirka bayan ya zura kwallaye hudu a gasar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun birkita kauyen Sokoto da harbi, sun sace sama da mutum 50

Tauraron Crystal Palace ya yi fice saboda gudunsa, iya kutsa kai da kuma basirar kai hari.

Manyan 'yan wasan Afirka 10

Ga jerin 'yan wasan Afrika da suka taka rawar gani a gasar Kofin Duniya ta 2026:

1. Ismaila Sarr (Senegal)

Ya zura kwallaye hudu tare da zama babban mai cin kwallaye daga Afirka a gasar.

2. Yoane Wissa (DR Kongo)

Dan wasan Newcastle ya zura kwallaye uku, ciki har da biyu da suka taimaka wa kasarsa kai wa matakin knockout a karon farko.

3. Yan Diomande (Côte d'Ivoire)

Matashin dan wasan RB Leipzig ya burge duniya da gudunsa, iya jan kwallo da kirkirar damar cin kwallo.

4. Azzedine Ounahi (Morocco)

Dan wasan tsakiya ya ci gaba da nuna kwarewarsa a manyan wasanni tare da taimaka wa Morocco kai wa matakai na gaba.

5. Vozinha (Cabo Verde)

Mai tsaron raga mai shekara 40 ya zama abin mamaki bayan ya yi manyan ceton kwallaye, musamman a wasan da suka buga da Spain.

Kara karanta wannan

Spain da ta lashe kofin duniya na iya rasa 30% na kudin da ta samu, an ji dalili

6. Ismael Saibari (Morocco)

Ya zama daya daga cikin manyan masu cin kwallaye daga Afirka, inda ya ci kwallo a dukkan wasannin rukuni uku.

7. Amad Diallo (Côte d'Ivoire)

Ya taka muhimmiyar rawa ta hanyar cin muhimman kwallaye tare da samar da damammaki ga abokan wasansa.

8. Pape Gueye (Senegal)

Jaridar TVC News ta rahoto cewa dan wasan tsakiya ya yi fice saboda kokarinsa, nutsuwa da kuma gudummawar da ya bayar wajen cin kwallaye.

An ce 'yan Afrika sun taka rawar gani a gasar Kofin Duniya 2026
Kofin da aka fafatawa kansa a gasar Kofin Duniya ta 2026. Hoto: Jordan Bank - FIFA/FIFA via Getty Images
Source: Getty Images

9. Emam Ashour (Masar)

Ya kasance daya daga cikin fitattun 'yan wasan Masar bayan ya ci muhimman kwallaye tare da nuna bajinta a kai hari.

10. Ibrahim Maza (Algeria)

Matashin dan wasan Bayer Leverkusen ya ja hankali saboda iya jan kwallo da kirkirar damammaki duk da kalubalen da Algeria ta fuskanta a gasar.

Kasashen Afrika 10 sun nuna bajinta

A wani labari, mun ruwaito cewa, Bayan da Morocco ta zama ƙasa ta ƙarshe daga cikin ƙasashen Afirka 10 da aka koro daga Kofin Duniya ta FIFA 2026, lokaci ya yi da za a yi nazari kan yadda nahiyar ta taka rawar gani a gasar.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kaddamar da manyan ayyukan tallafawa talakawa

Gaba ɗaya, kasashen nahiyar Afirka sun nuna ƙwazo a gasar, amma dai babu wata ƙasa da ta iya maimaita bajintar da Moroko ta yi a gasar 2022 lokacin da ta kai wasan kusa da na ƙarshe.

Ganin cewa Morocco tana matsayi na bakwai a jadawalin FIFA, rashin kai wasan kusa da na ƙarshe ya bar ɗan takaici a zukatan magoya bayanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com