‘Yan Keke Napep Sun Rungumi Tafiyar TinubuMustGo domin Hana APC Zarcewa a 2027

‘Yan Keke Napep Sun Rungumi Tafiyar TinubuMustGo domin Hana APC Zarcewa a 2027

  • Wasu matukan A daidaita sahu sun dauko aikin ganin bayan gwamnatin Bola Ahmed Tinubu
  • Direbobin na Keke Napep sun ce babu abin da suke samu saboda tsadar da man fetur ya yi a Najeriya
  • Halin kuncin da suka shiga ya sa wasu direbobin sun zama jakadun tafiyar adawa ta Tinubu Must Go

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Wasu direbobin Keke Napep a jihar Kano sun amsa kiran da ‘yan adawa suke yi na Tinubu Must Go a fadin kasar nan.

An ji wani direban Keke Napep da aka fi sani da ‘A daidata Sahu’ a Kano yana bayanin irin mawuyacin halin da suke ciki.

Keke Napep
Wasu babura masu kafafu 3 da aka fi sani da Keke Napep a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Abba Hikima ya tallata TinubuMustGo

Fitaccen lauya mai kare hakkin al’umma, Abba Hikima ya daura bidiyon matukan a shafinsa na Facebook a cikin makon nan.

Kara karanta wannan

Abubuwa 10 da Tinubu ya tabo a jawabin ranar bikin murnar samun ‘yancin kai

A nan aka ji wani matuki yana nuna da za su za a yi tafiyar Tinubu Must Go saboda ‘dan karen tsadan da man fetur ya yi yau.

Fetur ya doshi N1500 daga N200

Yake cewa a N200 ake saida lita a lokacin da Bola Tinubu ya karbi mulki, amma a yanzu fetur ya kai kusan N1500 a gidan mai.

Ya ce idan suka ware kudin mai Keke Napep, sai a ga babu abin da suke tsira da shi a aljihunsu.

Direban yake korafi cewa sakamakon tsadan da fetur ya yi, duk abin da suke karba daga fasinjoji a gidajen mai yake karewa.

An ji shi yana cewa tamkar gidajen man suke yi wa aiki tuka baburin mai kafafu uku.

Ganin tsadar man fetur ne Gwamnatin tarayya ta kawo tsarin CNG domin ganin talaka yana zurga-zurga cikin sauki a Najeriya.

Sai dai har yanzu, baburan CNG ba su samu karbuwa sosai ba a wajen masu abubuwan hawa.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An kashe wani shugaban jam'iyyar su Kwankwaso a Arewacin Najeriya

Direbobin Keke Napep ba su iya biyan haya

Direban wanda bai bayyana sunansa ba, ya ce tsadan fetur ta jawo suna fada da fasinjoji, abokan hulda da masu gidajen haya.

Kudin da wasu direbobin suke samu bai isa su kula da dawainiyar iyali kuma har a iya sallamar masu gidajen da suke zaman haya.

Wannan matsin lamba ne ya ce ya jawo wasu abokan aikinsu suka tsere daga Najeriya, suka tafi kasashen Larabawa domin yin ci-rani.

Sai dai abin takaici, ya bayyana cewa da yawa daga cikinsu sun mutu a sahara, wasunsu kuma sun zama bayi a hannun larabawa.

'Yan Keke Napep sun ce TinubuMustGo

Sun yanke shawarar za su yi adawa da takarar Bola Tinubu kuma za su yi ta whure wa fasinjoji kunne cewa ka da su zabe shi a 2027.

Har ya ce kyau kowane mai Keke Napep ya iya aika wannan sako na Tinubu Must Go ga mutane 100 da ya dauka kan titi kowace rana.

Kara karanta wannan

An samu matsala, mutum 3 sun mutu a gidan gwammatin jihar Neja

Jawabin Bola Tinubu ranar murnar 'yancin kai

A jawabin Shugaba Bola Tinubu na ranar samun 'yancin kai, rahoton nan ya ce ya yi zancen kuncin rayuwa da ake ciki a Najeriya.

Shugaban kasar ya bukaci 'yan kasar su sani cewa gwamnati za ta karkata akalar hankalinta wajen samar da ayyukan yi ga jama'a.

Tinubu ya tabbatar wa 'Yan Najeriya cewa shekaru uku na sauye-sauyen tattalin arziki sun soma kawo cigaba a halin yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng