Miliyoyin Dalolin da Sifen da sauran Kasashe 48 Suka Samu a Gasar Cin Kofin Duniya

Miliyoyin Dalolin da Sifen da sauran Kasashe 48 Suka Samu a Gasar Cin Kofin Duniya

  • Jimillar kuɗin kyautar kudin da aka ba kasashe sun kai dala miliyan 871 (£662m) daga gasar cin kofin duniya
  • Zakarar gasar Sifen, ta samu dala miliyan 51, yayin da Argentina ta sami dala miliyan 34, mafi yawa a tarihin gasar
  • Kowace kasa da ta shiga gasar an tabbatar mata da aƙalla dala miliyan 12.5 na shiga gasar da kuma na shirye-shirye

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

New York - Makudan kudi aka raba bayan kammala gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a ranar Lahadi, 19 ga watan Yuli 2026.

Hukumar FIFA ta yi rabon kudin da ba a taba ganin irinsu ba tun da aka fara buga gasar cin kofin wasan kwallon kafa a duniya a 1930.

Sifen
Ferran Torres ya taimaki Sifen ta doke Argentina a gasar kofin duniya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sifen ta samu $50m daga Gasar kofin duniya

Kasar Sifen da ta doke Argentina ta lashe gasar kofin duniya na kwallon kafa ta samu kudin da ya fi na kowace kasa in ji Yahoo Sports.

Kara karanta wannan

Kasafin kudin 2026: Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da boye Naira tiriliyan 12.8

Zakarun duniyan sun tashi da Dala miliyan 51, kusan Naira biliyan 70.36 a kudin Najeriya idan dai muka yi lissafin canjin dala a yau.

Argentina da ta je wasan karshe ta samu Dala miliyan 33, kimanin Naira biliyan 45 da za a raba tsakanin 'yan wasa da hukumar kasar.

FIFA ta samu $800m daga gasar 2026

Kamar yadda hukumar FIFA ta sanar tun a watan Disamban 2025, gasar bana shi ne mafi girma kuma wanda ya fi kowane kawo kudi.

Wannan karo kasashe 48 suka fafata wajen cin kofin da ya fi kowane martaba a kwallon kafa, a karshe Sifen ta doke kasar Argentina.

$871m aka raba tsakanin wadannan kasashe 48 da suka buga gasar. Kudin da ya shigo wa kowace kasa ya danganta da irin kokarinta a gasar.

Tun daga Sifen da ta samu kimanin $50m, akwai kasashen da $9m kadai ya shigo lalitarsu da sunan gasar sai wani kaso na dawainiya.

Kowace kasa dama ta samu $1.5m domin dawainiyar shirye-shiryen zuwa gasar cin kofin na kwallon kafa a duniya.

Kara karanta wannan

Mbappe, Rodri da ‘yan wasan da suka lashe kyauta a gasar kofin kwallon duniya

Kasar Ingila da ta doke Faransa da ci 6-4 a ranar Asabar da ta wuce ta samu $29m. Zakarun na shekarar 2018 kuwa sun tashi da $27m.

Mata da mazan Amurka za su raba $16m

Kasar Amurka wanda da ta shirya gasar da Mexico da Kanada ta samu $16m. Sai dai akwai yarjejeniyar da ta sa za a raba kudin ne.

‘Yan wasan kwallon kafa na maza da mata za su raba har 80% na wannan miliyoyin daloli. Kowane ‘dan kwallo zai samu $246,153.85 kenan.

Wasu kasashe sun nemi karin kudi

CNBC ta ce hukumomin kwallon kafan wasu kasashe musamman na Turai sun roki FIFA cewa sai an kara masu kudi ko kuwa su yi asara.

Idan irin wadannan kasashe kamar Faransa ba su kai labari a gasar ba, za su yi asara ne saboda abin da suka kashe wajen shirya wa gasar.

Haka kuma akwai haraji da Amurka ke karba daga kasashen. Hukumomin Kanada da Mexico babu ruwansu da tatsada wadannan kudi.

Gasar cin kofin duniya
Tawagar Sifen bayan cin kofin 2026 da kuma Lionel Messi tare da Lamine Yamal a Gasar cin kofin duniya a New York Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Kudin da aka biya kasashe daga gasar kofin duniya

  1. Sifen: $50m
  2. Argentina: $33m
  3. Ingila: $29m
  4. Faransa: $27m

Kara karanta wannan

Mbappe ya zarce Messi, ya kafa sabon tarihi a gasar cin kofin duniya

Ragowar kudin da FIFA ta ba kasashen duniya

Kasashe na 5 zuwa na 8

Norway, Beljium, Morocco, Switzerland: $19m

Kasashe na 9 zuwa na 16

Mexico, Colombia, Brazil, Amurka, Portugal, Canada, Egypt, Paraguay: $15m

Kasashe na 17 zuwa na 32

Netherlands, Jamus, Côte d'Ivoire, Croatia, Jafan, Australiya, DR Congo, Ghana, Ecuador, Afrika ta Kudu, Suwidin, Bosniya and Herzegovina, Algeria, Sanagal, Cabo Verde: $11m

Kasashe na 33 zuwa na 48

Iran, Koriya ta Kudu, Türkiyya, Scotland, Uruguay, Saudi Arabiya, Czechia, New Zealand, Qatar, Curaçao, Panama, Jordan, Haiti, Uzbekistan, Tunisiya, Iraq: $9m

Wadanda suka yi zarra a gasar kofin duniya

Rahoto ya zo cewa Kylian Mbappe da Rodri sun sha gaban Lionel Messi, sun tashi da kyaututtuka a gasar kofin duniya da aka gama.

Rodri ne ya zama gwarzon 'dan kwallo a gasar cin kofin duniya, ya yi galaba a kan Lionel Messi da ya ci kwallaye har takwas a gasar 2026.

Ingila ce ta zo kasa ta uku a gasar wannan karo bayan ta doke Faransa wanda da farko mutane sun yi tunanin ita za ta lashe wannan kofi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng