Spain da Ta Lashe Kofin Duniya na iya Rasa 30% na Kudin da Ta Samu, An Ji Dalili

Spain da Ta Lashe Kofin Duniya na iya Rasa 30% na Kudin da Ta Samu, An Ji Dalili

  • Ana iya cire har kashi 30 cikin 100 na kudin kyautar da Spain ta samu bayan lashe Kofin Duniya na FIFA 2026 saboda harajin Amurka
  • Rahotanni sun ce dokokin harajin Amurka na bai wa gwamnatin kasar damar karbar haraji daga kudaden da aka samu ta ayyukan da aka gudanar a cikinta
  • Wasu 'yan majalisar dokokin Amurka sun soki yiwuwar cire harajin, suna cewa hakan zai iya rage sha'awar shirya manyan wasannin duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.

Amurka - Rahotanni sun nuna cewa Spain na iya rasa har kashi 30 cikin 100 na kudin kyautar da ta samu bayan lashe gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026 sakamakon dokokin harajin Amurka.

Kasar Spain ta lashe kofin ne bayan doke Argentina da ci 1-0 a wasan karshe da aka buga a filin wasa na New York New Jersey a ranar Lahadi, 19 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Trump ya ji zafin kisan sojojinsa da Iran ta yi, zai karbi gawarwakinsu a wani biki a Amurka

Ana fargabar Spain za ta iya rasa kaso 30 na kudin da ta samu a gasar Kofin Duniya.
'Yan wasan Spain suna murna yayin da suke daga Kofin Duniya na 2026. Hoto: Carl Recine
Source: Getty Images

Nawa Spain ta samu a Kofin Duniya?

A cewar FIFA, zakarun gasar za su karbi dala miliyan 50 daga cikin jimillar dala miliyan 871 da aka ware a matsayin kyautar gasar da aka fadada zuwa kasashe 48.

Sai dai dokokin harajin Amurka sun tanadi cewa kudaden da baki suka samu daga ayyukan da suka gudanar a cikin kasar na iya kasancewa karkashin harajin tarayya.

Rahotanni sun ce 'yan wasa da sauran wadanda ba mazauna Amurka ba na iya fuskantar cire harajin tarayya da ya kai kashi 30 cikin 100, sai dai idan wata yarjejeniya ta haraji ko wata doka ta ba su rangwame.

'Yan majalisar Amurka sun yi martani

Dan majalisar wakilai na jam'iyyar Republican daga jihar Tennessee, Tim Burchett, ya soki yiwuwar cire irin wannan kaso daga kudin Spain.

Ya ce:

"Ina ganin rashin adalci ne. Ban goyi bayan hakan ba, amma 'yan wasan Amurka ma suna biyan haraji, don haka sun san wannan kafin su zo."

Kara karanta wannan

Miliyoyin dalolin da Sifen da sauran kasashe 48 suka samu a gasar cin kofin duniya

Burchett ya kara da cewa irin wannan haraji ba zai taimaka wajen jawo karin manyan wasannin duniya zuwa Amurka ba.

Zarge-zargen rashin rangwame

Wani fitaccen mai sharhi a kafafen sada zumunta, William Copus, wanda aka fi sani da The Feedski, ya ce yawanci kasashen da ke karbar bakuncin Kofin Duniya kan ba FIFA, kungiyoyin kwallon kafa da 'yan wasa rangwamen haraji.

Sai dai ya yi ikirarin cewa Amurka ba ta bayar da irin wannan rangwamen ba.

A cewarsa, FIFA ta samu matsayin keɓewa daga wasu harajin tarayya, amma hakan bai shafi 'yan wasa, masu horaswa da sauran ma'aikata ba.

Sai dai rahoton ya nuna cewa ba a samu damar tabbatar da wannan ikirari daga wata majiya mai zaman kanta ba.

Masana sun yi martani kan dokar harjain Amurka da za ya shafi Spain bayan lashe gasar kofin Duniya.
Trump ya na gaisawa da kyaftin din Spain lokacin mika masu kambun Kofin Duniya, 2026. Hoto: Carl Racine
Source: Getty Images

Wani dan majalisa ya soki tsarin

Dan majalisar wakilai na jam'iyyar Democrat daga jihar Illinois, Jonathan Jackson, shi ma ya bayyana rashin jin dadinsa kan yiwuwar harajin.

Ya ce tsarin harajin ya kamata ya fi dora nauyi kan manyan kamfanoni maimakon ma'aikata da masu aiki.

"Kamfanoni ya kamata su fi biyan haraji maimakon samun hanyoyin kauce wa biyan haraji, yayin da masu aiki ke biyan kaso mai tsoka daga abin da suka samu."

Kara karanta wannan

Kasafin kudin 2026: Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da boye Naira tiriliyan 12.8

- Jonathan Jackson.

Spain ta doke Argentina a Kofin Duniya

A wani labari, mun ruwaito cewa, a karo na biyu a tarihinta, Sifaniya ta ɗaga kofin gasar cin kofin duniya bayan ta doke Argentina a wasan ƙarshe.

La Roja ta samu nasara da ƙwallo 1-0, inda Torres ya zura ƙwallon da ta ba ta damar komawa saman duniya.

Wannan nasara ta ƙara tabbatar da matsayin Sifaniya a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙasashen ƙwallon ƙafa a duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com