Rashin Sani: Shaguben da Sanatan Amurka Ya Yi ga Iran Kwana 5 Kafin Ya Mutu

Rashin Sani: Shaguben da Sanatan Amurka Ya Yi ga Iran Kwana 5 Kafin Ya Mutu

  • Sanata Lindsey Graham ya yi martani cikin rashin tsoro ga barazanar Iran kwanaki biyar kafin rasuwarsa a Amurka
  • Graham ya rasu yana da shekara 71 sakamakon gajeriyar rashin lafiya, bayan ya dawo daga ziyarar Ukraine
  • Rasuwarsa ta girgiza Amurka da ƙasashen duniya, yayin da Shugaba Donald Trump da sauran jagorori suka bayyana alhininsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Sanata Lindsey Graham ya yi watsi da barazanar da Iran ta yi masa kwanaki biyar kacal kafin rasuwarsa.

A lokacin jana'izar marigayi Jagoran Addinin Iran, Ali Khamenei, an nuna hotonsa tare da wasu fitattun mutane a kan allunan da ke ɗauke da saƙonnin barazana.

Sanata Amurka ya yi shagube ga Iran kafin mutuwarsa
Marigayi Sanata Lindsey Graham a hagu da wani hotonsa da aka nuna yayin jana'izar Ali Khamenei a Tehran a dama. Hoto: @LindseyGrahamSC.
Source: Twitter

Sanata ya yi martani ga barazanar Iran

A wani saƙo da ya wallafa a shafin X, Graham ya ce aƙalla sun yi amfani da hoto mai kyau, ya yi maganar ce cikin shagube ga hukumomin Iran.

Kara karanta wannan

Martanin Trump kan mutuwar sanatan Amurka da ke zuga shi kan yaki da Iran

Ya ƙara da cewa mutane su rika yi masa hukunci ta hanyar duba irin maƙiyan da yake da su.

Sabon Jagoran Addinin Iran, Mojtaba Khamenei, ya sha alwashin ɗaukar fansar mahaifinsa da sauran waɗanda suka mutu a yaƙe-yaƙen baya, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka wallafa bayan jana'izar mahaifinsa.

Rahotanni sun ce Graham ya rasu yana da shekara 71 bayan wata gajeriyar rashin lafiya lamarin da ya tayar da hankula a tsakanin al'ummar Amurka.

Kiran gaggawa ya nuna cewa ya fara ji ciwon ƙirji kafin daga bisani ya samu bugun zuciya wanda ake tunanin shi ne sanadin mutuwarsa.

Sanatan Amurka ya bar duniya
Sanata Lindsey Graham yana jawabi kafin rasuwarsa. Hoto: Tom Williams.
Source: Getty Images

Gundunmawar da Graham ya ba Trump

Kafin rasuwarsa, Graham ya kai ziyara Ukraine inda ya zagaya wata masana'antar ƙera jiragen yaƙi marasa matuƙa ta SkyFall.

Ya kuma gana da Shugaba Volodymyr Zelensky tare da tattauna batutuwan tsaro da siyasa yayin da ake ci gaba da rigima a yankin.

Sanatan ya kasance ɗaya daga cikin manyan masu goyon bayan manufofin Donald Trump kan Iran.

Kara karanta wannan

Sanatan Amurka da ke zuga Trump kan yaƙar Iran da sauran manufofin kasar ya rasu

Haka kuma ya yi ƙoƙari wajen ganin an ƙaƙaba sababbin takunkumai masu tsauri kan Rasha, kasar da aka fara nuna mata yatsa da zargi kan mutuwar sanatan.

Ofishinsa ya ce iyalansa sun nemi a ba su damar jimamin wannan babban rashi cikin natsuwa, sun kuma gode wa jama'a bisa addu'o'i da goyon bayan da suke samu.

Rasuwar Graham ta jawo alhini daga shugabanni da dama a duniya, shugaba Donald Trump ya bayyana shi a matsayin babban ɗan kishin ƙasa wanda zai yi matuƙar kewarsa.

Mutuwar sanata: An fara zargin Rasha

An ji cewa an fara kira da a gudanar da bincike kan musabbabin mutuwar Sanata Lindsey Graham na jam'iyyar Republican a Amurka.

Masu wannan ra'ayi sun yi zargin ko an ba shi guba, amma ba su gabatar da wata hujja da ta tabbatar da hakan ba.

An ambaci barazanar da wasu jami'an Iran suka yi masa a baya da kuma matsayinsa kan yaƙin Rasha da Ukraine.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.