World Cup 2026: Kasar Ghana Ta Karya Tarihin Najeriya a Gasar Cin Kofin Duniya

World Cup 2026: Kasar Ghana Ta Karya Tarihin Najeriya a Gasar Cin Kofin Duniya

  • Ghana ta doke kasar Panama da ci 1-0 a wasan farko na rukunin L a gasar cin kofin duniya na shekarar 2026
  • Ghana ta zama kasa ta biyu daga nahiyar Afirka da ta samu nasara a gasar kofin duniya ta bana bayan Côte d’Ivoire
  • Nasarar ta sa Ghana ta kafa tarihin da Najeriya ta kafa a yawan nasarorin kasashe daga Afirka a tarihin Kofin Duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ghana ta zama kasa ta biyu daga Afirka da ta samu nasara a gasar Kofin Duniya ta 2026 bayan Caleb Yirenkyi ya ci kwallon da ta bai wa tawagar Black Stars nasara da ci 1-0 kan Panama a Toronto ranar Laraba.

Da alama wasan zai kare babu ci ko canjaras kafin Yirenkyi ya zura kwallo a minti na 95, lamarin da ya bai wa tawagar Carlos Queiroz muhimmiyar nasara a wasan farko na rukunin L.

Kara karanta wannan

Matasan Arewa sun gano abin da ke kullawa domin sauke manyan hafsoshin tsaron Najeriya

Yan wasan Ghana.
Yan wasan kasaf Ghana suna murna bayan samun nasara kan Panama Hoto: Darrian Traynor
Source: Getty Images

Nasarar ta zo ne kwanaki bayan Côte d’Ivoire ta doke Ecuador, wanda ya sa Afirka ta samu nasara ta biyu a gasar, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

Kasashen Afirka sun nuna bajinta

Baya ga nasarorin Ghana da Côte d’Ivoire, kasashen Afirka sun nuna bajinta a wasanninsu na farko, in da Cape Verde ta yi canjaras da Spain yayin da Morocco ta hana Brazil samun nasara.

Ha zalika, kasar Masar ta tashi kunnen doki da Belgium, yayin da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo ta raba maki da Portugal.

Sai dai Algeria, Afirka ta Kudu, Tunisia da Senegal sun sha kaye da tazarar kwallo daya a wasanninsu na farko.

Yadda kasar Ghana ta samu nasara

Panama ce ta fi kirkirar damar cin kwallo a mafi yawan lokacin wasan, inda Cecilio Waterman ya kusa zura kwallo, amma mai tsaron ragar Ghana, Lawrence Ati Zigi, ya hana ta shiga.

Daga bisani, mai horar da Ghana Carlos Queiroz ya yi sauye-sauye domin neman nasara, kuma matakin ya yi tasiri.

Kara karanta wannan

Duk da cika bakin Amurka kan sulhu, Iran ta ja mata layi, ta gindaya sharuɗa

Dan wasan da ya fito daga benci, Brandon Thomas-Asante, ya kutsa cikin akwatin bugun daga kai sai mai tsaron gida kafin ya bai wa Yirenkyi kwallo, wanda ya saka ta a raga cikin natsuwa domin bai wa Ghana nasara.

Semenyo.
Dan wasan Ghana, Angoine Semenyo, wanda ya samu kyautar dan wasan da ya fi kokari a wasansu da Panama Hoto: Joosep Martinson
Source: Getty Images

Ghana ta karya tarihin Najeriya

Nasarar ta sanya kasar Ghana ta samu maki uku, inta ita da Ingila suka hau sama a rukunin L, kamar yadda Sky Sport ta ruwaito.

Haka kuma, Ghana ta kai nasarori shida a tarihin wasannin da ta taka a Kofin Duniya, inda ta kamo Najeriya a matsayin kasashen Afirka da suka fi samun nasarori a gasar.

Abin lura shi ne Ghana ta cimma wannan nasara a cikin wasanni 16 kacal, yayin da Najeriya ta samu nasarori shida bayan buga wasanni 21.

Bakin fuska a gasar kofin duniya 2026

A wani labarin kuma, mun tattaro muku jerin kasashe hudu da suka zamu gurbin taka leda a gasar cin kofin duniya ta 2026 a karon farko a tarihinsu.

Rahotanni sun nuna cewa fadadagasar da hukumar kwallon kafa ta duniya watau FIFA ta yi zuwa kasashe 48, ya taimaka wajen samun bakin fuska a gasar ta bana.

Cape Verde na cikin wadannan kasashe hudu bayan ta kafa tarihi a matsayin daya daga cikin kananan kasashe mafi karancin yawan jama'a da suka taba kai wa gasar kofin duniya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262