Yanzu: Dan wasan Nigeria, Victor Osimhen ya kulla yarjejeniya da Napoli a kan €80m

Yanzu: Dan wasan Nigeria, Victor Osimhen ya kulla yarjejeniya da Napoli a kan €80m

- Dan wasan gaba na Nigeria, Victor Osimhen ya kulla yarjejeniya da kungiyar kwallon kafa ta Napoli, inda ake sa ran zai bar Lille a daren ranar Laraba (yau)

- An sayi dan wasan ne akan kudi €70m da kuma hasafin €10m. Yarjejeniyar shekaru biyar ce, da shekara daya idan ya so

- Osimhen wanda ya saka kwallaye 18 a raga a cikin wasanni 32 a lokacin zamansa a Lille, zai sanya riga mai lamba 9 a Napoli, a kakar wasan badi

Jaridar Punch ta ruwaito cewa dan wasan gaba na Nigeria, Victor Osimhen ya kulla yarjejeniya da kungiyar kwallon kafa ta Napoli, inda ake sa ran zai bar Lille a daren ranar Laraba (yau).

Osimhen, a cewar kafofin watsa labarai a Faransa da Itali, ya sa hannu kan yarjejeniyar taka leda na shekaru biyar akan kudi €70m, wanda zai iya haurawa har zuwa €80m idan ya zage damtse.

"An riga an kammala! An cike dukkanin takardu. Osimhen yanzu ya koma dan wasan Napoli. A yanzu Lille za ta sallameshi a yammacin yau (Laraba).

"Kamar yadda aka sanar a nan, an sayi dan wasan ne akan kudi €70m da kuma hasafin €10m. Yarjejeniyar shekaru biyar ce, da shekara daya idan ya so," a cewar shafin Get French Football.

Jaridar Italy, Tuttomercarto, ita ma ta wallafa cewa, "an kammala sa hannu a dukkanin takardu, a yanzu Victor Osimhen za koma Napoli. Abunda ya rage yanzu kawai shine a sanar."

Cinikin dan wasan shine mafi tsada a tarihin kungiyar, kuma mafi tsada a 'yan wasan da ta saya a kakar wasan bana.

Dan wasan Osimhen mai shekaru 21, wanda ya saka kwallaye 18 a raga a cikin wasanni 32 a lokacin zamansa a Lille, zai sanya riga mai lamba 9 a Napoli, a kakar wasan badi.

KARANTA WANNAN: Aljanin Dambe: "Yadda na kashe mutanen da ban san adadi ba" | Legit TV Hausa

Yanzu: Dan wasan Nigeria, Victor Osimhen ya kulla yarjejeniya da Napoli
Yanzu: Dan wasan Nigeria, Victor Osimhen ya kulla yarjejeniya da Napoli
Asali: Getty Images

A wani labarin, Akwai hasashen cewa mataimakin gwamnan jihar Ondo, Hon Agboola Ajayi, zai fice daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar Zenith Labour Party (ZLP) a mako mai zuwa.

Majiya mai tushe ta ce zai shiga jam'iyyar ZLP, wacce ita ce jam'iyya ta uku mai matukar karfi a jihar.

Ajayi ya fice daga jam'iyyar APC a watan Yuni, inda ya tsaya takara a zaben fidda gwani na PDP a watan Yuli, inda ya zamo na biyu da kuri'u 657.

Rahotanni sun yi nuni da cewa ya hadu da tsohon gwamnan jihar Olusegun Mimiko, inda suka tattauna kan yadda jam'iyyar ZLP zata bashi tikitin takara.

Idan har jam'iyyar ZLP ta ba Ajayi tikitin takara, to zata musanya sunansa da na Hon Rotimi Benjamin, wanda ya lashe zaben fitar da gwani na jam'iyyar.

Majiya daga jam'iyyar ZLP ta ce ana duba yiyuwar ba Ajayi tikitin takara ne la'akari da yawan kuri'un da ya samu a PDP duk da cewa ya shiga jam'iyyar a kurarren lokaci.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng