Babbar Ƙungiyar Ƙwallo a Saudiyya Za Ta Sayi Ɗan Wasan Najeriya kan Euro Miliyan 10.5

Babbar Ƙungiyar Ƙwallo a Saudiyya Za Ta Sayi Ɗan Wasan Najeriya kan Euro Miliyan 10.5

  • Kungiyar Al-Ittihad ta Saudiyya ta gabatar da tayin €10.5m, wanda zai iya kaiwa €12.5m, domin daukar Wilfred Ndidi daga Beşiktaş
  • Beşiktaş ba ta yanke hukunci kan tayin ba, tana jiran sabon kocinta Vincenzo Italiano ya tantance matsayin Ndidi a cikin shirinsa
  • Ndidi ya buga wasanni 31 a gasar Turkiyya a kakar da ta gabata, inda ya ci kwallaye biyu tare da bayar da taimako guda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Turkiyya – Kungiyar Al-Ittihad ta kasar Saudiyya ta kara nuna kwadayinta na daukar tauraron Super Eagles, Wilfred Ndidi, bayan gabatar da tayin Euro miliyan 10.5 ga Beşiktaş domin sayen dan wasan.

Rahotanni sun nuna cewa tayin na iya kaiwa Euro miliyan 12.5 idan Ndidi ya cika wasu sharuddan da suka shafi kwazonsa bayan kammala cinikin.

Kara karanta wannan

Amurka ta fara fuskantar matsalar makamai, Trump ya dakatar da hare hare kan Iran

Kungiyar Saudiyya ta Al-Ittihad ta fara shirin daukar dan wasan Najeriya Wilfred Ndidi
Wilfred Ndidi, kyaftin tawagar Super Eagles yana magana da 'yan jarida a Warsaw, Poland. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sabon kocin Beşiktaş zai yanke hukunci

Sai dai har yanzu Beşiktaş ba ta mayar da martani kan tayin ba, domin shugabannin kulob din na jiran sabon mai horas da kungiyar, Vincenzo Italiano, ya tantance 'yan wasansa kafin yanke hukunci kan wadanda zai ci gaba da amfani da su a kakar wasa mai zuwa, in ji rahoton Pan Africa Football.

Rahotanni sun nuna cewa ra'ayin Italiano ne zai kasance muhimmin abin da zai tantance ko za a amince Ndidi ya bar kungiyar ko kuma ya ci gaba da zama a Istanbul.

Ndidi ya taka rawar gani a kakarsa ta farko

Dan wasan mai shekaru 28 ya koma Beşiktaş ne a bazarar bara bayan karewar kwantiraginsa da Leicester City, inda ya koma kungiyar ta Turkiyya ba tare da an biya kudin cinikinsa ba.

A kakarsa ta farko, Ndidi ya zama daya daga cikin fitattun 'yan wasan tsakiyar fili na kungiyar, inda ya buga wasanni 31 a gasar Süper Lig, ya zura kwallaye biyu sannan ya bayar da taimakon kwallo guda.

Kara karanta wannan

Shugaban kasar Bangladesh ya yi murabus kafin karewar wa'adinsa

Kwarewar da ya samu tsawon shekaru yana taka leda a gasar Firimiya ta Ingila tare da Leicester City na daga cikin dalilan da suka sa Al-Ittihad ke son daukarsa domin kara karfafa tawagarta.

Akwai yiwuwar kyaftin din Super Eagles, Ndidi ya taka leda a Al-Ittihad
N'Golo Kante tare da 'yan tawagar Al-Ittihad suna daga kofin Saudi Pro League da suka lashe. Hoto: Yasser Bakhsh/Getty Images
Source: Getty Images

Al-Ittihad na jiran hukuncin Beşiktaş

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa idan cinikin ya tabbata, Ndidi zai shiga jerin manyan 'yan wasan Turai da suka koma gasar Saudiyya cikin 'yan shekarun nan.

Sai dai ga Beşiktaş, sayar da Ndidi ba abu ne mai sauki ba. Duk da cewa tayin Euro miliyan 10.5 zai iya zama babbar riba ga kulob din, kasancewar ya zo kyauta, shugabannin kungiyar na son fara jin ra'ayin sabon kocinsu kan muhimmancin dan wasan.

Ana sa ran makomar Ndidi za ta kara bayyana bayan Vincenzo Italiano ya kammala tantance 'yan wasan Beşiktaş kafin fara sabuwar kakar wasa. Har zuwa yanzu, tayin Al-Ittihad na Euro miliyan 10.5 na nan a kan tebur, yayin da kungiyar ta Turkiyya ke nazarin matakin da za ta dauka.

Mahaifin Wilfred Ndidi ya mutu

A wani labari, mun ruwaito cewa, an tabbatar da mutuwar mahaifin kyaftin din Super Eangles ta Najeriya sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da shi.

Kara karanta wannan

Kotu ta ɗaure wani mutumi a gidan kaso bayan kisan ƴar majalisa da mijinta

Kungiyar Besiktas da ke kasar Turkiyya ta tabbatar da aukuwar lamarin a wata sanarwada ta fitar domin jajantawa dan wasanta, Nadidi.

Wilred Ndidi, wanda ke bugawa Besiktas kwallo yana yawan magana kan mahaifinsa, wanda ya ce shi ne silar nasararsa a rayuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com