Osimhen: An Samu Kasar da Ke Son Sayen Dan Wasan Najeriya, Za Ta Biya N115.5bn

Osimhen: An Samu Kasar da Ke Son Sayen Dan Wasan Najeriya, Za Ta Biya N115.5bn

  • Juventus na shirin miƙa tayin €75m domin dauko Victor Osimhe, domin maye gurbin Dusan Vlahovic da ke shirin barin kungiyar
  • Osimhen na tsakiyar shuhurarsa a Galatasaray, inda ya zura kwallaye 17 tare da taimakawa aka ci kwallo sau shida a wasanni 21
  • Juventus za ta cimma nasarar sayen Osimhen ne idan ta siyar da Vlahovic da kuma samun gurbi a gasar Champions League ta badi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Juventus - Babbar kungiya a Serie A, Juventus, na shirin miƙa tayin €75m domin dauko ɗan wasan Najeriya, Victor Osimhen, domin maye gurbin Dusan Vlahovic.

Daraktan wasanni na Juventus, Cristiano Giuntoli, wanda ya dauko Osimhen zuwa Napoli a 2020, ya ayyana ɗan wasan Najeriyar a matsayin wanda yake son saye.

Juventus ta fara shirin sayen Osimhen a kan Euro miliyan 75
Kungiyar kwallon kafar Juventus na son sayen Osimhen a kan Euro miliyan 75. Hoto: @victorosimhen9
Asali: Getty Images

Juventus na son sayen Osimhen a kan €75m

Kara karanta wannan

"Daga Amurka aka samo kudin," Dattijo ya tona yadda aka nemi hana Tinubu takara

A cewar jaridar La Gazzetta dello Sport, Osimhen, wanda ke taka leda a Galatasaray a matsayin dan wasan aro, yana kan gan ganiyarsa a kungiyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya nuna cewa Victor Osimhen, dan gaban kungiyar Super Eagles ya zura kwallaye 17 da ba da taimako aka zura kwallo shida a wasanni 21.

Duk da haka, cinikin na fuskantar matsaloli, domin ƙa’idar daukar Osimhen a kan Euro miliyan 75 tana aiki ne ga ƙungiyoyin wajen Italiya.

Juventus na son sayar da Vlahovic a wata 6

Hakan na nufin cewa dole ne Juventus ta tuntubi abokiyar hamayyarta a Serie A, watau Napoli kai tsaye domin tattauna yiwuwar cinikin Osimhen.

Juventus na fatan siyar da Vlahovic domin samun kuɗi, bayan wakilan ɗan wasan sun dakatar da tattaunawar tsawaita kwantiraginsa saboda ƙarin albashi.

An ce kwantaragin Vlahovic zai ƙare a 2026, amma Juventus na sa ran siyar da shi cikin wata shida domin kada su rasa shi kyauta.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta samo rancen sama da N1bn don tsame Najeriya daga duhu

Abin da zai sa cinikin Osimhen ya yiwu

Idan an kammala cinikin, ana ganin zai zama babban sauyi a Serie A, tunda Napoli ba ta saba sayar da 'yan wasansu ga abokan hamayya ba.

Osimhen, wanda aka zaba gwarzon dan wasan Afirka na 2023, yana daga cikin mafiya kwarewa a Turai, ta fuskar gudu, ƙarfi da iya zura kwallo.

Juventus na ganin ɗaukar Osimhen zai inganta gabansu tare da rage nauyin albashi, kasancewar zai amfana da tsarin rage haraji na Decreto Crescita.

Duk da haka, wannan shirin zai dogara ne kan siyar da Vlahovic da kuma cancantar Juventus zuwa gasar Champions League mai zuwa.

Osimhen ya rasa gurbinsa a Napoli

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Dan wasan gaban Najeriya, Victor Osimhen, ya rasa damar barin Napoli bayan gazawar komawarsa Chelsea ko Al-Hilal.

Rahotanni sun nuna cewa Napoli ta kwace lamba tara da Osimhen ke sakawa, tare da ba Romelu Lukaku wanda ya koma kungiyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.