Tinubu Ya Samu Kishiya, Jigon APC Zai Fafata da Shi a Zaben Fitar da Gwani

Tinubu Ya Samu Kishiya, Jigon APC Zai Fafata da Shi a Zaben Fitar da Gwani

  • Wani ɗan kasuwa kuma jigon APC ya sayi fom ɗin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC kan Naira miliyan 100
  • Jigon jam'iyyar daga jihar Edo ya dauki wannan mataki ne domin fafatawa a zaɓen fitar da gwani na 2027 da za a yi a Abuja
  • Dan kasuwar yana shirin kalubalantar shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen fitar da gwani na APC, inda ya zama ɗaya daga cikin ‘yan takara na farko

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Wani ɗan kasuwa mai suna Osifo Stanley daga Edo ya sayi fom ɗin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC na Naira miliyan 100.

Dan kasuwar ya dauki wannan matakin ne domin shiga zaɓen fitar da gwani na zaben shugaban kasa da za a yi a zaben 2027.

Kara karanta wannan

2027: Shugaba Tinubu ya karbi fom din neman sake tsayawa takara a inuwar APC

Jigon APC ya sayi domin karawa da Tinubu
Dan kasuwa Osifo Stanley yayin sanyan fom din takarar shugaban kasa, Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga, @imranmuhdz.
Source: Facebook

Tinubu ya samu abokin takara a APC

Stanley ya bayyana aniyarsa ta kalubalantar shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar, inda ake ganin zai fafata da shugaban ƙasa mai ci, cewar The Guardian.

Ya kammala sayen fom ɗin ne a yau Talata 28 ga watan Afrilun 2026 a otal ɗin Sheraton da ke Abuja, gabanin fara shirye-shiryen zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar.

A wani taron manema labarai da ya gudanar a Abuja, Osifo ya yi watsi da zargin da ke danganta takararsa da shugaban ƙasa, yana cewa:

“Ba sabon abu ba ne a ji mutane suna cewa Tinubu ne ke ɗaukar nauyin takarata. Ko lokacin da na so na tsaya takara da Buhari a 2019, an ce shugaban ƙasar na yanzu ne ke daukar nauyina.
“Zan iya faɗa muku karara, kamar yadda nake tsaye a gabanku yau, ban taɓa cin ko sisi ɗaya daga wajensa ba.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya samu wanda za su fafata wajen neman tikitin APC a zaben 2027

Godiya ta tabbata ga Allah, Asiwaju yana raye har zuwa yau. Idan wani na da hujja, ya fito ya nunawa duniya. Saboda haka, ban damu da irin waɗannan zarge-zarge ba.”
Tinubu ya samu abokin takara a APC
Shugaba Bola Tinubu yana jawabi yayin taro a Abuja. Hoto; Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Stanley ne farko da zai kalubalanci Tinubu

Ana kallon Stanley a matsayin ɗaya daga cikin ‘yan takara na farko da suka shiga takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC kafin zaɓen 2027, cewar rahoton Punch.

Shugaba Tinubu, wanda ya hau mulki a shekarar 2023, ana sa ran zai nemi wa’adi na biyu a ƙarƙashin jam’iyyar APC a zaben da za a yi a 2027.

Mai amfani da shafin X, Imran Muhammad ya wallafa wani faifan bidiyo da Stanley ya sayi fom din takara domin kalubalantar Tinubu.

Tinubu ya sayi fom din takarar shugaban kasa

A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai sake tsayawa takara domin neman wa'adi na biyu a babban zaben shekarar 2027 da ake tunkara.

Tinubu ya saya fom din na gani ina so da na tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Sayen fom dai na zuwa ne yayin da lokacin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta kayyade ga jam'iyyu domin fitar da 'yan takara ke kara matsowa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.