Kaduna: SDP Ta Yi Babban Rashi, Jagoranta Ya Rasu a Mummunan Hadarin Mota

Kaduna: SDP Ta Yi Babban Rashi, Jagoranta Ya Rasu a Mummunan Hadarin Mota

  • Yan siyasa a Kaduna sun shiga mawuyacin hali bayan rasuwar daya daga cikin jiga-jigai, kuma masu fada a ji a garin Zariya
  • Wannan ya biyo bayan rasuwar Bashir Zakariya, shugaban jam’iyyar SDP na yankin Zariya, a wani mummunan hadarin mota
  • Jam’iyyar SDP ta bayyana marigayin a matsayin mutum mai gaskiya da hangen nesa, wanda ya sadaukar da kansa ga adalci

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna – Wani jigon jam’iyyar SDP, reshen jihar Kaduna, Bashir Zakariya, ya rasu a wani haɗarin mota da ya afku a hanyar Zariya zuwa Kaduna a ranar Alhamis.

Kafin rasuwarsa, Zakariya shi ne shugaban jam’iyyar SDP na yankin Zariya shiyya ta daya jihar Kaduna.

An yi mummunan hadari a Kaduna
Jagora a SDP ya rasu a Kaduna Hoto: Isma'il Haruna/Salis Pakeey
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa wasu jami’an jam’iyyar sun ce marigayin na kan hanyar dawowa daga Zariya zuwa Kaduna lokacin da haɗarin ya afku.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun kara da cewa dama ana yawan samun hadurra da cunkoso a hanyar, wanda ke jawo asarar rayuka da dama.

Jagora a jam'iyyar SDP ya rasu a Kaduna

Channels TV ta ruwaito cewa jam’iyyar SDP ta tabbatar da rasuwar jigon nata a wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na jihar, Darius Kurah, ya fitar.

Sanarwar ta ce:

“Mutum ne mai gaskiya, jaruntaka da hangen nesa, wanda sha’awarsa ga adalci da dimokuraɗiyya ta zamo haske ga yan SDP da ma wadanda ke wajen jam’iyyar."
“Zakariya mutum ne da ke tsayawa kan gaskiya, yana magana da gaskiya kuma yana aiki tukuru don bunƙasa SDP a shiyya ta daya da ma sauran yankuna.
“Zai kasance abin koyi ga jam’iyya da al’ummar jihar Kaduna baki ɗaya.”

SDP na jimamin rashin shugaban yankinta

Wasu daga cikin yan jam’iyyar sun bayyana cewa marigayin ya sha yin tafiya tsakanin Zariya da Kaduna a lokacin da yake aikin wayar da kan al’umma da jawo su cikin SDP.

Ana yawan samun hadari a titin Kaduna zuwa Zariya
Yan SDP sun fara jimamin rasuwar Bashir Zakariyya Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Sun ce rasuwarsa ta bar babban gibi a tsarin shugabancin jam’iyyar adawa a jihar da ke Arewa maso Yamma.

An fara kai ziyarar ta’aziyya zuwa gidan iyalan marigayin da ke Kaduna domin jajantawa danginsa, tare da addu'ar Allah Ya yi masa rahama.

Jam’iyyar SDP ta bukaci gwamnatin jihar Kaduna da hukumomin kula da hanyoyi na ƙasa da su ƙara himma wajen magance yawaitar haɗurra da ke afkuwa a hanyar Zariya zuwa Kaduna.

Jigo a LP ya rasu a Kaduna

A baya, mun wallafa cewa Mallam Lawal Garba, shugaban jam’iyyar LP na shiyyar Kaduna, ya rasu a wani haɗarin mota a hanyar Kaduna zuwa Zariya.

Rahotanni sun bayyana cewa haɗarin ya faru ne bayan kammala wani taro na manyan Arewa da ya gudana a Gidan Tarihi na Arewa, Kaduna.

A wata sanarwa daga Dr. Yunusa Tanko, kakakin kwamitin kamfen na Peter Obi ya bayyana mutuwar a matsayin babban abin takaici da ya girgiza su.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.