Jerin 'Yan Kwallon Kafa 10 da Suka Mutu a Hadari Suna cikin Tashe a Duniya

Jerin 'Yan Kwallon Kafa 10 da Suka Mutu a Hadari Suna cikin Tashe a Duniya

  • Diogo Jota na Portugal da Liverpool ya rasu a haɗarin mota tare da ɗan uwansa a Spain, kwana kaɗan bayan aurensa
  • Tarihi ya nuna cewa da dama daga cikin 'yan ƙwallo sun rasa rayukansu a haɗurran mota a kasashe daban-daban na duniya
  • Wadanda suka rasun sun hada da fitattun 'yan wasa kamar Federico Pisani, Michael Millett da Ray Jones daga Turai da Afirka

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Mutuwar Diogo Jota ta sake jaddada wani abu da ake yawan mantawa da shi a cikin ƙwallon ƙafa — cewa rayuwar ɗan wasa na iya yankewa kowane lokaci.

Wannan ba shi ne karon farko da al’umma ke kuka da rasuwar 'yan wasa sakamakon haɗurran mota ba.

Emiliano Sala da Diago Jota sun rasu a hadari
Emiliano Sala da Diago Jota da suka rasu a hadari. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Punch ta yi rahoto kan wadanda suka rasu ta irin wannan hanya, wasu tun suna matasa, wasu kuma bayan sun shahara sosai kafin haɗari ya kawo karshen su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Federico Pisani na Italiya ya rasu 1997

Dan wasan gaba da ya yi tashe, Federico Pisani yana da shekara 22 kacal lokacin da ya rasu a cikin haɗarin mota.

Federico Pisani ya kasance ɗaya daga cikin matasan da ake sa ran zai wakilci ƙasar Italiya kafin rasuwarsa.

2. Millett na Ingila ya yi hadari a 1995

Michael Millett ɗan shekara 17 ne daga kulob ɗin Wigan Athletic ya rasu a wani haɗari a kusa da Garswood.

Ya rasu ne bayan shigarsa cikin manyan 'yan wasan kulob ɗin kuma bayan mutuwarsa, Wigan ta ci kyautar girmamawa a duniya.

3. Davis ya rasu a 2003 bayan hadari

Jimmy Davis ya kasance ɗan kasar Ingila kuma ɗan wasan Manchester United ne da ya je aro kulob din Watford.

Ya rasu ne a haɗarin mota a kan babbar hanyar M40 kuma an yi shiru na dan lokaci da saka riguna bakake a wasannin Watford da United don girmama shi.

4. Jones ya yi hadarin mota a 2007

Ray Jones ɗan wasan gaba ne a kulob din Queens Park Rangers kuma ya kasance dan asalin kasar Ingila ne.

Ya rasu ne makonni kaɗan bayan samun damar shiga gasar Premier League, kuma an shirya taron tunawa da shi bayan ya rasu.

5. Malanda na Belgium ya rasu a 2015

Junior Malanda na kulob ɗin Wolfsburg ya rasu bayan motarsa ta kife a kan hanya mai danshi yana tsaka da cin zamaninsa.

Rahotanni sun nuna cewa motar ta yi wurgi da shi yayin hadarin, kuma ya mutu nan take kafin zuwa asibiti.

6. Reyes na Spain ya mutu 2019

Tsohon ɗan wasan Arsenal da Sevilla, Antonio Reyes, ya mutu ne a cikin haɗarin mota a garinsu Utrera, yayin da motarsa ke gudu fiye da kima.

An ruwaito cewa daya daga cikin ’yan uwan tsohon 'dan wasan na Arsenal da Real Madrid da ke tafiya da shi shi ma ya rasu yayin da suka yi hadarin.

7. Montiel na Argentina ya rasu a 2019

Dan wasan kulob din Atlético de Rafaela da ake kira da Diego Montiel ya mutu yana da shekara 23.

Motarsa ta kife a kan hanya kuma mutuwarsa ta girgiza masu harkar ƙwallon ƙafa a matakin ƙananan kulob a Argentina.

8. Sala na Argentina ya yi hadari a 2019

The Guardan ta wallafa cewa Sala ya mutu ne a hatsarin jirgin sama bayan da ya kammala komawa kulob din Cardiff City daga Faransa.

Jirgin da ya dauke shi ya fadi cikin Tekun Ingila kuma sai bayan makonni ana nema, aka gano jirgin da gawarsa.

9. Madisha na Afirka ta Kudu ya rasu a 2020

Motjeka Madisha ya rasu ne bayan motarsa ta kama da wuta sakamakon faduwa da ta yi a wani hadari.

Duk da an ciro shi da rai, daga bisani ya mutu a asibiti kuma ya kasance daya daga cikin matasan Mamelodi Sundowns da Afirka ta Kudu ke alfahari da shi.

10. Diogo Jota ya yi hadarin mota a 2025

Dan wasan Portugal, Diago Jota ya rasu tare da ɗan uwansa bayan hadarin mota a Zamora, kasar Spain.

Legit ta rahoto cewa hadarin ya ya faru ne kwanaki kaɗan bayan aurensa kuma Jota yana da shekara 28 ya kwanta dama yana cikin taka leda a Liverpool.

Jota tare da Cristiano Ronaldo
Diogo Jota tare da Cristiano Ronaldo. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

'Yan wasan Kano 22 sun rasu a hadarin mota

A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan wasan jihar Kano su 22 sun rasu sakamakon mummunan hadarin mota.

Rahotanni sun bayyana cewa hadarin ya auku ne a karamar hukumar Kura yayin da suke daf da shiga birnin Kano.

Gwamnatin jihar da sauran masu ruwa da tsaki a harkar wasanni a Najeriya sun yi jimamin rasuwar 'yan wasan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng