Kwanaki kaɗan bayan Ɗaura Aurensa, Fitaccen Ɗan wasan Liverpool Ya Rasu
- Ɗan wasan Liverpool da kasar Portugal, Diogo Jota ya rasa ransa a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da shi a Sifaniya
- Jota, wanda ya lashe gasar Firimiya a kakar wasan da ta gabata, yana cikin tawagar Portugal da ta lashe Nations League a watan Yuni, 2025
- Wannan rasuwa ta Jota tare da ƙaninsa ta girgiza duniyar kwallon ƙafa, inda tuni aka fara miƙa ta'aziyya da alhinin wannan rashi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Spain - Ɗan wasan gaba na Liverpool, ɗan asalin ƙasar Portugal, Diogo Jota, ya rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a yankin Zamora da ke ƙasar Sifaniya.
Ɗan uwansa, Andre Silva, mai shekaru 26, ɗan wasan kulob ɗin Penafiel da ke buga kofin gajiyayyu a Portugal, ya rasu a hatsarin motar tare da shi.

Asali: Getty Images
Hukumar ƴan sandan Spain ‘Guardia Civil’ ta tabbatar wa da BBC Sport cewa hatsarin ya faru ne da misalin karfe 12:30 na tsakar dare (agogon yankin) wayewar garin yau Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta ce motarsu kirar Lamborghini ta sauka daga hanya bayan tayar motar ta fashe yayin da suke kokarin wuce wata mota, kafin daga bisani motar ta ƙone gaba ɗaya.
Jota, ɗan kimanin shekara 28 ya mutu ne kwanaki 11 bayan ya auri masoyiyarsa da suka jima tare, Rute Cardoso, wacce suka haifi 'ya'ya uku.
Liverpool ta yi alhinin wannan rashi
Kungiyar Liverpool ta bayyana cewa tana cikin “matuƙar baƙin ciki” bisa wannan rashi mai raɗaɗi, rahoton Sky Sport.
Jota ya koma Liverpool daga Wolverhampton Wanderers a 2020 kan kuɗi £41m, inda ya zura ƙwallo 65 a wasanni 182.
Marigayin yana daga cikin 'yan wasan da suka taimaka wa kulob ɗin wajen lashe gasar FA Cup da League Cup a 2022, da kuma kofin Firimiya a kakar wasan da ta gabata.
A kwanan nan, Jota ya wakilci ƙasar Portugal a wasan karshe na gasar Nations League, inda suka doke Spain a ranar 8 ga Yuni 2025, shi ne wasa na 49 da ya buga wa ƙasarsa.

Asali: Getty Images
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Portugal ta yi alhini
A wata sanarwa da ta fitar, Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Portugal (FPF) ta bayyana cewa:
“Hukumar Ƙwallon ƙafa ta Portugal gaba ɗaya ta shiga cikin alhini. Baya ga kasancewa ƙwararren ɗan wasa, Diogo Jota mutum ne mai kima da girmamawa.
"Mutum ne da kowa ke son kasancewa da shi. Ya kasance abin koyi a cikin al’umma, mun rasa hazikan matasa biyu.
"Rasuwar Diogo da Andre Silva babban rashi ne wanda ba za a iya maye gurbinsa ba a duniyar ƙwallon ƙafa ta Portugal. Za mu ci gaba da girmama sunayensu da abin da suka bari.”
Ronaldo ya yi ikirarin zama gwarzon duniya
A wani labarin, kun ji cewa zaƙaƙurin ɗan kwallo, Cristiano Ronaldo, ɗan asalin Portugal ya yi ikirarin cewa ya fi kowa iya buga tamaula.
Ronaldo ya kuma bayyana yadda ya kusa komawa kungiyar Barcelona kafin a kammala cinikin da ya kai shi Man United a shekarar 2004.
A wata hira da aka yi da shi kwanakin baya, ɗan wasan ya yi fariyar cewa babu wanda ya taɓa kai matsayin da ya kai a wasan kwallon kafa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng