Zakarun Turai: Yadda Jadawalin Kwata Final Na UEFA Champions League Ya Kasance

Zakarun Turai: Yadda Jadawalin Kwata Final Na UEFA Champions League Ya Kasance

  • Bayan kammala wasannin 'yan 16 a gasar cin kofin zakarun Turai ta UEFA Champions League, yanzu kuma an iso matakin kwata final
  • Hukumar gudanarwar gasar ta UEFA, a wannan Juma'ar, ta fitar da jadawalin wasannin da za a buga a zagayen kwata final din
  • Za a fara buga zagayen farko na kwata final a gasar cin kofin zakarun Turai na 2023/24 a ranar 9 da 10 ga watan Afrilu, 2024

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Gasar cin kofin zakarun Turai ta UEFA Champions League ta iso matakin kwata final, inda ya rage saura tawaga takwas da za ta fafata a wannan mataki.

Hukumar gudanarwar gasar ta UEFA, a wannan Juma'ar, ta fitar da jadawalin wasannin da za a buga a kwata final.

Kara karanta wannan

Jerin tsofaffin 'yan wasan Najeriya 5 masu son kujerar Peseiro bayan barin kocin Super Eagles

UEFA 2023/2024: Jadawalin kwata final
UEFA 2023/2024: Za a fara buga zagayen farko na kwata final a ranar 9 da 10 ga watan Afrilu. Hoto: Sporting News
Asali: UGC

Manchester City ta Pep Guardiola za ta iya zama kungiya ta biyu kacal da ta lashe kofin gasar zakarun Turai a jere

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda ta wallafa a shafinta na yanar gizo UEFA.com, Za a buga zagayen farko a ranar 9 da 10 ga watan Afrilu, 2024, yayin da za a buga zagaye na biyu a ranar 16 da 17 ga Afrilu, 2024.

Ga yadda jadawalin ya ke:

UEFA Champions League 2023/2023 - Kwata final

Arsenal VsBayern Munich
Atletico MadridVsBorussia Dortmund
Real MadridVsManchester City
Paris Saint-GermainVsBarcelona

UEFA: Yaushe za a buga kwata final?

Shafin wasanni na Sporting News ya wallafa cewa za a fara buga zagayen farko na kwata final a gasar cin kofin zakarun Turai na 2023/24 a ranar 9 da 10 ga watan Afrilu, 2024.

Kara karanta wannan

Tinubu na fuskantar sabuwar matsala yayin da 'yan fansho ke shirin fita zanga-zanga tsirara

Za a gudanar da wasannin zagaye na biyu na kwata final din bayan mako guda da kammala zagayen farko a ranar 16 da 17 ga watan Afrilu.

Jadawalin wasannin kusa da na karshe

Bayan kammala wasannin kwata final, ga kuma yadda ake hasashen kungiyoyin kwallon kafar za su kara da juna a wasan kusa da na karshe na gasar ta UEFA.

Atletico Madrid/Borussia DortmundVsParis Saint-Germain/Barcelona
Arsenal/Bayern MunichVsReal Madrid/Manchester City

UEFA: Yaushe za a buga wasannin gaba?

Za a buga zagayen farko na wasan kusa da na karshe a gasar UEFA 2023/24 a ranar 30 ga watan Afrilu da 1 ga watan Mayu, 2024.

Haka kuma za a buga zagaye na biyu na wasan kusa da na karshe bayan mako guda da kammala zagayen farko a ranar 7 da 8 ga watan Mayu.

UEFA: Cikakken jadawalin wasanni

Ga cikakken jadawalin wasannin da ya hada da; tawagannin da za su kara da juna da kuma ranar buga wasannin.

Kara karanta wannan

Buga takardun bogi: Kotu ta dauki mataki kan tsohon shugaban bankin NIRSAL, Abdulhameed

Wasannin kwata final

Haduwar tawagaRanakun zagayen farkoRanakun zagaye na biyu
Arsenal vs. Bayern Munich9/10, Afrilu, 202416/17, Afrilu, 2024
Atletico Madrid vs. Borussia Dortmund9/10, Afrilu, 202416/17, Afrilu, 2024
Real Madrid vs. Manchester City9/10, Afrilu, 202416/17, Afrilu, 2024
Paris Saint-Germain vs. Barcelona9/10, Afrilu, 202416/17, Afrilu, 2024

Wasannin kusa da na karshe

A wannan bayanin na kasa, za mu yi amfani da KF a matsayin 'kwata final', sannan TN a matsayin 'tawagar da ta yi nasara.

Haduwar tawagaRanakun zagayen farkoRanakun zagaye na biyu
TN a wasan KF 2 Vs TN a wasan KF 430 ga Afrilu/1 ga Mayu7/8, Mayu, 2024
TN a wasan KF 1 Vs TN a wasan KF 330 ga Afrilu/1 ga Mayu7/8, Mayu, 2024

Wasan karshe

A wannan bayanin na kasa, za mu yi amfani da WKK a matsayin 'wasan kusa da na karshe', sannan TN a matsayin 'tawagar da ta yi nasara.

Kara karanta wannan

Ramadan 1445: Gwamnatin Jigawa ta dauki matakin saukakawa ma’aikata da azumi

Haduwar tawagaRanar buga wasaLokacin buga wasa
TN a wasan WKK 1 Vs TN a wasan WKK 21 ga Yuni, 2024Karfe 1:00 na rana

Jerin kungiyoyin da aka fitar

Ga cikakken jerin kungiyoyin da aka fitar da su daga gasar zakarun Turai ta 2023/24.

  1. Red Star Belgrade (SER)
  2. Young Boys (SWI)
  3. Royal Antwerp (BEL)
  4. Union Berlin (GER)
  5. Braga (POR)
  6. Benfica (POR)
  7. RB Salzburg (AUS)
  8. Feyenoord (NED)
  9. Celtic (SCO)
  10. Lens (FRA)
  11. Sevilla (SPA)
  12. Galatasaray (TUR)
  13. Man United (ENG)
  14. Shakhtar Donetsk (UKR)
  15. Milan (ITA)
  16. Newcastle United (ENG)
  17. Lazio (ITA)
  18. Real Sociedad (SPA)
  19. FC Copenhagen (DEN)
  20. RB Leipzig (GER)
  21. Napoli (ITA)
  22. Porto (POR)
  23. PSV (NED)
  24. Inter Milan (ITA)

UEFA2023/2024: A ina za a buga wasan karshe?

An shirya gudanar da wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai na 2024 a ranar Asabar, 1 ga Yuni a filin wasa na Wembley, London, UK.

An dakatar da Ronaldo a Saudiya

Kara karanta wannan

Duk da gwamnati ta dauki mataki, farashin gas din girki ya sake lulawa har ya haura N1300

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa hukumar gudanarwar wasanni ta kasar Saudiya ta dakatar da Cristiano Ronaldo daga taka leda na wasu kwanaki.

Wannan dakatarwar ta biyo bayan samun Ronaldo da karya dokar wasanni ta kasar a bangaren murna yayin da aka ci kwallo.

Ronaldo ya yi murna a wani yanayi na rashin da'a bayan zura kwallo a ragar kungiyar Al-Shabab.

Asali: Legit.ng

Online view pixel