2023/2024: Man City Ta Lashe Gasar Premier, Ta Kafa Tarihi a Duniyar Kwallon Kafa

2023/2024: Man City Ta Lashe Gasar Premier, Ta Kafa Tarihi a Duniyar Kwallon Kafa

  • Kungiyar kwallon kafa ta Man City ta lashe kofin gasar Premier ta bana bayan ta tashi wasanta da ci 3-1
  • Phil Foden ya zura wa Man City kwallaye biyu yayin da shi ma Rodri ya zura kwallo daya, wanda ya baCity damar lashe kofin
  • A yayin da Arsenal ta zo ta biyu a kakar wasan na bana, Saminu Adamu Namunaye ya shaidawa Legit Hausa cewa tawagar ta yi kokari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Man City ta lashe kofin gasar Premier ta bana da aka buga a shekarar 2023/2024, kuma ta lashe gasar karo na hudu a jere, abin da ba a taba yi ba a tarihin gasar.

Man City ta lashe gasar Premier
Man City ta lashe gasar Premier, karo na 4 a jere, wanda ba a taba yi ba. Hoto: @ManCity
Asali: Twitter

Man City ta lashe gasar Premier 2023/24

Kara karanta wannan

Forbes: Ronaldo ya zama dan wasa mafi samun albashi a duniya, ana biyansa $260m

Phil Foden ya zura wa Man City kwallaye biyu yayin da shi ma Rodri ya zura kwallo daya, wanda ya ba tawagar Pep Guardiola damar lashe kofin karo na shida a cikin kaka bakwai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babu wata kungiya a tarihin gasar Ingila da ta taba lashe kofin Premier sau hudu a jere, amma a wannan karon, City ta rubuta sabon tarihi, kamar yadda ta wallafa a shafinta na intanet.

Kocin na Catalan ya jagoranci tawagar City zuwa lashe gasar Premier shida a cikin shekaru bakwai da suka gabata.

Arsenal ta gaza lashe gasar tun 2003/04

A cikin wadannan shekaru, tawagar ta haye maki 90 a shekaru hudu. Man City ta matsa lamba a kakar bana domin hana Arsenal cin kofin a karon farko tun bayan shekarar 2003/04.

Gunners ta yi tashi wasanta da ci 0-0 a Etihad a watan da ya gabata wanda ya ba ta tazarar maki daya da City a sauran wasanni tara da suka rage, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Tawagar yan wasan Najeriya ta naɗa dalibin sakandare a matsayin kyaftin

Amma zakarun gasar, ba su yi kasa a gwiwa ba wajen fafatawa a sauran wasannin, inda suka lashe wasanni tara na karshe na gasar, bayan sun zura kwallaye 33.

"Arsenal ta yi kokari a bana" - Namunaye

Wani mai sharhin wasanni daga jihar Bauchi, Saminu Adamu Namunaye, wanda ya zanta da Legit Hausa jim kadan bayan kammala wasannin, ya ce Arsenal ta yi abin azo a gani.

A cewar Namunaye, shekaru 20 kenan kungiyar Arsenal ba ta nuna hazaka a gasar ba kamar bana, kuma magoya bayan tawagar sun yi fatan daga kofin bayan nasara a kan Mancester United.

Mai sharhi kan wasan ya yi nuni da cewa, rawar da Arsenal ta taka a bana zai zama tamkar allura a yayin da za ta tunkari kakar wasa na gaba.

A bangaren Manchester City kuwa, Namunaye ya ce Pep Guardiola ya nuna fikira da kuma kwarewa a wasannin da tawagarsa ta buga duk da kura-kuran da suka samu a baya.

Kara karanta wannan

"An yi amfani da bam": Mutum 1 ya mutu da aka bankawa masallata wuta a Kano

Ronaldo: Dan wasa mafi samun albashi a 2024

A wani labarin, mun ruwaito cewa, an ayyana Cristiano Ronaldo a matsayin dan wasa mafi samun albashi a duniya, wanda wannan ne karo na hudu da ya ke zama a kan gaba.

Ronaldo ya zama dan wasan da ya fi karbar albashi a duniya bayan da ya koma kungiyar Al Nassr ta Saudiya inda ya samu kusan dala miliyan 260 a watanni 12.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel