Real Madrid vs Dortmund: Abubuwan Sani Dangane da Wasan Karshe na Kofin Zakarun Turai

Real Madrid vs Dortmund: Abubuwan Sani Dangane da Wasan Karshe na Kofin Zakarun Turai

  • Real Madrid da Borussia Dortmund za su kece raini a wasan ƙarshe na gasar zakarun Turai (UCL) a filin wasa na Wembley a yammacin ranar Asabar 1 ga watan Yunin 2024
  • Borussia Dortmund ta doke PSG a wasan na kusa da na ƙarshe, inda ta yi nasara da ci 2-0 a wasanni biyu yayin da Real Madrid ta samu tikitin zuwa Wembley bayan ta lallasa Bayern Munich da ci 4-3 a wasanni biyu da suka buga
  • Borussia Dortmund ta taɓa lashe gasar sau ɗaya kacal, inda ta doke Juventus da ci 3-1 a kakar wasa ta 1996/1997, yayin da Real Madrid ta ɗauki kofin sau 14

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

London, United Kingdom - Za a buga wasan karshe na gasar zakarun Turai (UCL) a ranar Asabar, 1 ga watan Yunin 2024.

Kara karanta wannan

Kwana 1 da lashe gasar Champions League, Madrid ta sayi Mbappe daga PSG

Wasan ƙarshen za a buga shi ne a tsakanin Borussia Dortmund ta ƙasar Jamus da Real Madrid ta ƙasar Spain.

Real Madrid za ta kara da Borussia Dortmund
Real Madrid da Borussia na neman lashe kofin zakarun Turai na 2024 Hoto: Alex Grimm, Florencia Tan Jun
Asali: Getty Images

Ina za a buga wasan ƙarshe na UCL 2024?

Za a buga wasan ƙarshen ne a filin wasa na Wembley da ke birnin Landan na ƙasar Ingila, cewar rahoton Goal.com

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Filin wasa na Wembley ya ƙara tsaurara tsaro saboda wasan ƙarshe na gasar zakarun Turai a ranar Asabar, 1 ga watan Yunin, da nufin kaucewa sake aukuwar rashin bin doka da oda a lokacin gasar Euro 2020.

Su wa za su taka leda a wasan ƙarshen?

Real Madrid da Borussia Dortmund za su fafata domin neman lashe gasar zakarun nahiyar Turai (UCL).

Ana yiwa Real Madrid kallon matsayin waɗanda za su yi nasara a wasan yayin da ake kallon Borussia Dortmund a matsayin wacce za ta iya ba da mamaki.

Kara karanta wannan

Matawalle ya dauki zafi kan kisan sojoji a Abia, ya fadi matakin dauka

Wane lokaci ne za a fara wasan?

Za a fara wasan ƙarshe na neman cin gasar kofin zakarun Turai a filin wasa na Wembley da ƙarfe 8:00 na dare agogon Najeriya.

Za a gabatar da wasu shirye-shiye kafin a fara wasan.

Wanene alƙalin wasan UCL 2024?

Dan ƙasar Slovenia, Slavko Vincic ne zai hura wasan ƙarshen a filin wasa na Wembley.

Hukumar kula da kwallon kafa ta Turai UEFA, ta tabbatar da zaɓen Slavko mai shekara 44 a farkon watan Mayu.

Yadda za a kalli wasan ƙarshe na UCL 2024

A Burtaniya, za a nuna wasan ƙarshe na gasar zakarun Turai a tashar TNT Sports (Discovery+).

A Amurka, za a nuna shi akan tashoshin CBS da TUDN. Ƴan Najeriya za su iya kallo a tashar SuperSport.

Legit Hausa ta tuntuɓi wani mai goyon bayan Real Madrid wanda ya nuna ƙwarin gwiwarsa kan cewa ƙungiyar za ta sake lashe kofin a karo na 15.

Kara karanta wannan

Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda a jihar Kaduna, sun cafke masu ba su bayanai

Muhammad Auwal.ya bayyana cewa yana ji a jikinsa cewa tawagar ƴan wasan Real Madrid za su yi duk abin da ya dace domin lashe gasar.

A kalamansa:

"Ai wannan wasan kamar mun yi nasara ne mun gama duba da irin ƙwarewar da Real Madrid suke da ita a wajen buga wasan ƙarshe."

Ɗan wasan Real Madrid zai yi ritaya

A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan wasan tsakiya na ƙungiyar kwallon ƙafa ta Real Madrid, Toni Kroos, ya bayyana cewa zai yi ritaya daga buga kwallo bayan kammala gasar Euro 2024 a ƙasar Jamus.

Ɗan wasan wanda ya zo Real Madrid daga ƙungiyar Bayern Munich ya sanar da shirinsa na daina taka leda ne a shafinsa na Instagram.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng