Siyasar Najeriya
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya jagoranci babɓar tawagar zuwa wurin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a gidansa na Daura a Katsina.
Sunday Igboho ya sha suka, Fulani sun nemi jami'an tsaro su kame shi bayan da ya dawo daga tsare da aka yi a kasar waje kan wasu dalilai na shiga kasa ba lasisi.
Jami'an yan sanda sun yi kokarin tarwatsa wasu da ake zaton magoya bayan Gwamna Alia ne yayin da suka yi yunkurin taɗa rikici a sakatariyar APC a Makurdi.
Hukumar ƴan sanda reshen jihar Benuwai ta kwace iko da babbar sakatariyar APC mai mulki a jihar bisa umarnin Gwamna Alia na hana duk wani taron siyasa.
Gwamnan Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas ya bada umarnin a daina banbanta malaman makaranta a wajen biyan alawus na rage raɗaɗi N35,000 ga ma'aikata.
Shina Peller, tsohon mamban majalisar wakilan tarayya da wasu dubban mambobin Accord Party sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP ranar Alhamis a Oyo.
Adnan Mukhtar Adam Tudunwada ya ce Atiku Abubakar kuma jagoran adawar shi ne mafi karfin ‘yan siyasa daga Arewa a yau, Atiku shi ne wanda gwamnati ke tsoro.
Urum Kalu, ɗaya daga cikin mutum 5 da shugaba Bola Tinubu ya naɗa a CBN ya ƙi karban tayin, ya ce aikin zai ci karo da wanda ya fara a bankin duniya.
Anthony Adefuye ya roƙi yan Najeriya su kara hakuri da gwamnatin Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, inda ya ce sauye-sauyen da ake yi zai haifar da abu mai kyau.
Siyasar Najeriya
Samu kari